Zaɓin da Ecowas ke da shi na kawar da masu juyin mulki a Nijar

niger coup

Asalin hoton, ECOWAS/FACEBOOK

Bayan cikar wa'adin da Ƙungiyar Raya Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecowas) ta bai wa sojoji masu juyin mulki a Nijar ranar Lahadi, ƙungiyar ƙasashen a yanzu ta tsara gudanar da wani taron ƙoli ranar Alhamis, inda ake sa ran za ta fitar da matsayi na gaba.

Tuni dai, shugabannin juyin mulki suka rufe sararin samaniyar Nijar, bayan sun yi ƙememe sun ƙi mayar da hamɓararren Shugaba Bazoum Mohamed kan karagar mulki.

A cewar Ecowas, rashin biyan buƙatunta na iya sanya ta ɗaukar "duk wani mataki.....ciki har da yiwuwar kai hare-haren soji cikin Nijar.

Manyan hafsoshin tsaron ƙasashen Ecowas a cikin makon jiya dai sun tsara wani shiri na yiwuwar amfani da ƙarfi fatattakar 'yan juyin mulkin 26 ga watan Yuli, ciki har da lokaci da kuma yadda za su tura dakarun sojoji da za su faɗa wa Nijar.

Hakan dai ya ƙara fargabar ta'azzarar rikici a yankin da ke fama da fitinar 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi.

Ƙungiyar dai ta ƙi yarda ta kwarmata bayanai, amma dai ko ma yaya ne za ta buƙaci amincewar shugabannin ƙasashen yankin kafin tura sojoji zuwa Nijar.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi nazari game da zaɓin amfani da ƙarfin sojoji ko akasin haka, da Ecowas take da shi, ko da yake dukkan zaɓin yana tattare da kasada.

Tura sojojin mamaya ta ƙasa

Ƙungiyar Ecowas ta sha tura dakarunta zuwa yankunan da ke fama da rikici kafin yanzu, amma dai ba ta taɓa tura sojoji cikin Nijar ba, musamman a lokaci irin wannan da yankin ke fama da matuƙar rarrabuwar kai.

Masu sharhi a fannin tsaro sun ce fayyace bayanai game da wani babban shirin amfani da sojoji na iya ɗaukar tsawon makonni kafin ya kammala, sannan mamaye irin wannan, yana ƙunshe da ɗumbin kasada.

A ciki har da yiwuwar sarƙewa a rikicin da zai shafe tsawon lokaci da kuma yiwuwar ɗaiɗaita Nijar da ma yankin Afirka ta Yamma gaba ɗaya.

Jagoran juyin mulkin, Janar Abdourahamane Tiani ya taɓa aiki a matsayin kwamandan bataliyar dakarun Ecowas na wanzar da zaman lafiya a Ivory Coast bayan tsagaita wuta tsakanin gwamnati da mayaƙa 'yan tawaye a shekara ta 2003.

Don haka ya san yadda ɗaukar matakin soji a kan wata ƙasa yake.

Sai dai, har yanzu wasu za su ji cewa suna da zaɓi ƙalilan.

"Idan ba su tafi can ba, hakan zai kasance wata babbar matsalar kare mutunci. Ecowas ta shata jan layi," a cewar Djiby Sow, wani babban mai bincike a Cibiyar Nazarin Harkokin Tsaro ta Dakar.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya faɗa cewa gwamnatinsa ta shirya wa tunkarar jerin zaɓin da take da su ciki har da yiwuwar tura dakarun soji zuwa Nijar.

Senegal ma ta ce za ta iya tura dakarunta.

Sai dai shugabannin juyin mulki a Guinea da Burkina Faso da Mali sun bayyana goyon bayansu ga sojojin da suka ƙwace mulki a Nijar, kuma sauran ƙasashen ma suna da nasu ƙalubalen tsaron.

Hare-haren dakaru na musamman

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wannan zaɓi zai ƙunshi amfani da 'yan tsirarun dakarun ƙasa da za a harhaɗo su cikin gaggawa.

Dakarun mai yiwuwa ne za su mayar da hankali ne wajen ƙwace muhimman cibiyoyin tsaro da na mulki, tare da kuɓutar da Bazoum daga ɗaurin talala da ake yi masa, sannan su mayar da gwamnatinsa kan mulki, a cewar Ikemesit Effiong, wani babban mai bincike a cibiyar tuntuɓa kan ayyukan bayanan sirri ta SBM a Najeriya.

Ecowas tana iya neman taimakon bayanan sirri daga dakarun Amurka da na Faransa da ke cikin Nijar.

"Lokacin da dakarun za su yi amfani da shi taƙaitacce ne kuma tuni akwai ƙwarewar da za a iya aiwatar da hakan a cikin yankin na Afirka ta Yamma.

Irin wannan aikin sojoji zai fi zama tabbas," in ji Effiong.

Duk da haka, shi dai cike da kasada. Kasancewar dakarun ƙasashen waje a wasu cibiyoyi suna gadi cikin tsakiyar babban birnin Niamey na iya harzuƙa tarzoma a birnin da ɗaruruwan mutane suka hau kan tituna don nuna goyon baya ga masu juyin mulki da kuma adawa da katsalandan ɗin ƙasashen waje.

Niger Coup

Asalin hoton, Defence Hqtrs/Facebook

Amfani da rarrabuwar kan sojojin Nijar

Nijar makekiyar ƙasa ce da ke da mabambantan al'ummomi, inda Bazoum Mohamed ya lashe zaɓen 2021 da kashi 56% na ƙuri'un da aka kaɗa.

Babu masaniya ƙarara a kan yawan goyon bayan da ɓangarori daban-daban za su bai wa sabbin shugabannin.

Masharhanta a fannin tsaro da jami'an diflomasiyya sun kuma nunar da ɓarakar da ta fito fili a cikin rundunar sojin Nijar.

Ba dai lallai ne a ce dukkaninsu sun haɗu wajen mara baya ga juyin mulkin ba.

"Wani lamari guda ɗaya kawai da nake ganin zai iya tasiri a ganina... shi ne ya kasance a cikin sigar nuna taƙaitaccen goyon baya ga wani ɓangare na wasu dakarun rundunar sojin Nijar," a cewar Peter Pham na Atlantic CouncilT, cibiyar ƙwararrun masu ba da shawara kuma tsohon jami'in jakadancin Amurka na musamman a yankin Sahel.

"Ban ga ta yadda za su iya shiga ba, ba tare da gudunmawar 'yan gari ba."

Nazari, tare da jaddada matakin takunkumai

Ecowas ta ɗauki tsattsauran mataki a kan Nijar idan aka kwatanta da yadda ta yi wa sojoji masu juyin mulki a Burkina Faso da Mali da suka ƙwace iko shekara uku da ta wuce.

Hakan na nufin, tana iya yanke shawarar ci gaba da ƙaƙaba takunkumai, ta dakatar da shirin ɗaukar matakin soji, maimakon haka ta buƙaci masu mulkin su mayar da iko hannun farar hula bayan gudanar da zaɓuka.

Shugabannin juyin mulkin sun ce a shirye suke su tattauna game da haka, ba tare da sanya wani lokaci ba.

Shi ma wannan zaɓi, yana da irin tasa kasada a yankin.

Idan takunkumai suka raunana tattalin arziƙin Nijar, ɗaya daga cikin ƙasashen duniya mafiya talauci, hakan na iya rura wutar goyon baya ga sojojin juyin mulki da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi da ke kwaɗaitawa matasa aƙidunsu da kuɗi da kuma matsugunni.