Dabarar da sojojin Mali suka yi wa Ecowas ta janye musu takunkumi

Mai goyon bayan shugaban mulkin sojin Mali

Asalin hoton, Getty Images

Sojojin da ke mulki a Mali sun yi nasarar janyo hankalin ‘yan kasar tare da tayar musu da tsimi na kishin kasa.

Sun yi nasarar sanya shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, Ecowas, sun janye takunkumin da suka sanya wa kasar, sakamakon juyin mulkin da suka yi, kamar yadda Paul Melly ya yi nazari.

 Bayan tsayar da watan Fabrairu na 2024 a matsayin lokacin da za su gudanar da zabe, gwamnatin sojin ta Mali ta yi nasarar shawo kan Ecowas ta cire mata takunkumin da ta sanya wa kasar.

Ga talakawan Mali, musamman mazauna babban birnin kasar Bamako, wadanda yawancinsu sun dogara ne da kayan abincin da ake shigarwa kasar daga waje, wannan labari ne mai dadin ji a gare su.

Ko da yake matakin ba wai yana nufin dakatar da shigar da kayan masarufi ba ne, a zahiri wani karin nauyi ne ga ‘yan kasuwa da iyalai, wadanda suke fama da tsadar kayan abinci da mai da duniya ke fama da ita a yanzu, sakamakon bukatarsu da ta karu a duniya saboda annobar korona da yakin Ukraine.

An sanya wa kasar takunkumin ne a watan janairu bayan da sojojin da suka kwace a mulki suka sanar da jinkirta mayar da kasar hannun farar-hula da shekara hudu.

A yanzu sun rage wannan wa’adi da kasa da shekara biyu, inda za a yi zabe a watan Fabrairu na 2024.

Shugabannin Ecowas sun amince da wannan mataki a yayin taron kolinsu da suka yi a babban birnin Ghana, Accra a karshen mako.

Cin zalin makwabta

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wannan ba karamar nasara ba ce ga gwamnatin sojin ta Mali kadai har ma ita kanta Ecowas, wadda yawancin ‘yan Mali da sauran mutane ke wa kallon gungu ne na shugabannin kasashe masu ji da kai, wadanda ke yi wa sojoji masu juyin mulki kallon hadarin-kaji, su kuma su kawar da kai daga laifukansu.

 Shugabannin mulkin soji na Mali da Firaministan kasar Choguel Maïga sun yi dabara inda suka tafi a kan doron wannan kallo da ake yi wa shugabannin na Ecowas, inda suke nuna wa al’ummar kasar cewa su masu kishin kasarsu ne tare da kare ta da jama’arta daga makwabtansu masu cin zali.

Makwabtan da ba sa maraba da duk wani yunkuri na samar da gagarumin sauyi a kasar da shugabanninta da suka babbake al’amura suka kasance cikin almundahana da rashawa iya wuya.

A cikin watanni shida da suka gabata duk wani sako mai tsauri da ya fito daga Ecowas ko Turai ko kuma Majalisar Dinkin Duniya, yana haduwa da tirjiya da kakkausar suka daga al’ummar Mali.

A tsakiyar watan Mayu, gwamnatin sojin ta sanar da cewa za ta fice daga kungiyar G5 Sahel, wadda aka kirkira a 2014, domin yaki da masu ikirarin jihadi.

Iyalan wani gida a Mali

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnatin sojin ta ci gaba da mu’amalarta da kamfanin tsaron nan na kasar Rasha Wagner, duk da irin zargin da ake yi wa kamfanin kan yadda sojojin hayarsa ke take hakkin dan-Adam da cin zarafin farar-hula.

 Tabarbarewar mu’amala tsakanin kasar da Faransa da kuma sauran kasashen Turai, inda Faransa ta sanar da janye sojojinta da ta kai domin yakar masu ikirarin jihadi, janyewar da sojojin za su kammala a wata mai zuwa.

Haka kuma a halin da ake ciki sojojin na Mali sun tsaurara dokokinsu a kan sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, da ake kira Minusma.

Sun hana masu bincike kan cin zarafi da sauransu na jama’a, kamar wanda ake yi wa sojojin haya na kamfanin na Rasha da sojin kasar, na kashe mutane kusan 300 a kauyen Moura a karshen watan Maris.

 Duk da wannan tirjiya ta sojin na Mali, suna nasara sannu a hankali wajen wanzar da shirinsu na siyasa, wanda Ecowas ka iya yarda da shi.

Yawan juyin mulki

Da farko shugabannin kasashen Afirka ta Yamma sun so sun una dan sassauci.

Wakilinsu a kan rikicin Mali, kuma tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya rika kai gwauro yana kai mari a Mali.

Sai dai kuma daga bisani kungiyar ta Ecowas ta ga ya kamata ta taka birki kan yadda ake samun yawan juyin mulki a yankin, wanda kafin yanzu zai yi tunkahon cewa yawancin kasashensa na karkashin mulkin farar-hula ne na jam’iyuyu da dama.

An samu juyin mulki na biyu a watan Mayu na shekarar da ta gabata, bayan na farko na watan Agusta 2020.

 Sai kuma ga Guinea, ita ma a watan Satumba Kanar Mamady Doumbouya ya hambarar da gwamnatin Shugaba Alpha Condé.

Manyan sojojin Mali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kanar Mamady Doumbouya (a tsakiya) tsohon sojan Faransa ne

Haka ita ma Burkina Faso, a watan Janairu sai kwatsam sojoji suka hambarar da Shugaba Roch Marc Christian Kaboré, wanda aka zaba a wa’adi na biyu a karbabben zabe, watanni 14 baya, saboda zargin gazawar gwamnatin na dakile yawan hare-haren masu ikirarin jihadi.

Daga nan sai kuma aka samu abin da ake kallo a matsayin wani yunkuri na juyin mulki da bai yi nasara ba a Guinea-Bissau.

Mutane goma sha daya ne suka rasa ransu, yayin da sojojin da ke biyayya ga Shugaba Umaro Sissoco Umbaló suka yi nasarar kawar da masu yunkurin kawar da shi daga mulkin, da suka kai hari fadar gwamnatin kasar.

Akwai kuma jita-jitar cewa wasu kasashen ma na yankin na Afirka ta Yamma za su iya bin sahu na juyin mulkin na soji.

Saboda haka wajibi ne Ecowas ta dauki matakin taka birki ga wannan ta’ada ta hambarar da gwamnatocin farar-hula.

Haka kuma dole ne kungiyar ta samu yadda za ta sake mayar da wadancan kasashe kan mulkin farar-hula, kasashen da suka hada da Mali da Guinea da kuma Burkina Faso.

Wannan ba wai kawai domin amfanin mulkin farar-hula a yankin Afirka ta Yamma ba kawai, saboda cewa ita Mali tana tsakiyar rikicin yankin Sahel da kuma kokarin dakile tashin hankalin kungiyoyin mayaka da rikicin kabilu a yankin.

A don haka ci gaba da mayar da kasar saniyar-ware ba abin da zai ta’zara sai wadannan rikice-rikice da kuma matsin lamba da gwamnatocin kasashe a yankin ke sha na karancin abinci da sauyin yanayi.

Dakatar da fito-na-fito

Sannu a hankali gwamantin sojojin ta Mali, na daukar matakan sasantawa da kuma samun karbuwa da ke tabbatar wa da kungiyar Ecowas cewa da gaske suke.

Daga cikin matakan akwai sabuwar dokar zabe da samar da hukumar zabe da kuma bayani ko matakan mayar da kasar kan mulkin farar-hula, muhimma ma daga cikinsu shi ne fitar da jadawalin gudanar da zaben shugaban kasa a watan Fabrairu na 2024.

To amma duk da haka kuma akwai rashin tabbas na cewa ko tsarin zai hana shugaban mulkin sojin kasar na yanzu Assimi Goïta, tsayawa takara.

Ko ma dai mene ne, alamun da aka gani na mayar da kasar mulkin dimokuradiyya zuwa yanzu sun ba wa Ecowas karfin halin ci gaba da tattaunawa da shugabannin sojin na Mali, a kan sauran bayanan da suke bukata.

Mutane na maraba da soji a Mali

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan Mali da dama sun yi maraba da soji da zummar za su yi maganin hare-haren masu ikirarin jihadi

Wannan ya sa shugabannin na kasashen Afirka ta Yamma suka yanke shawarar cewa, ya kamata su dage takunkumin da suka sanya wa kasar.

Kuma suna ganin hakan ko ba komai wata galaba ce a wurinsu, wadda kuma za ta kai ga dawowa daga turbar da ake kai ta yin fito-na-fito da shugabanin sojin na Mali da ke nuna kansu a matsayin ‘yan kishin kasa, da kuma makwabtanta.

Wannan kuwa suna ganin abu ne da ake matukar bukata a yankin da ke fama da matsaloli da dama.

Da hakan ne kuma shugabannin na Ecowas suka cimma yarjejeniya da shugabannin soji na Burkina Faso, wajen samar da jadawalin mayar da kasar kan mulkin farar-hula a watan Yuli na 2024.

 Ecowas na fatan wannan nasara da ta yi a tsakanin da wadannan shugabanni na soji, zai karfafa wa suma sojin Guinea su bi sahu.

Hakan ya sa kungiyar ta zabi tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Benin Thomas Boni Yayi a matsayin mai shiga Tsakani, domin tattaunawa da hukumomin sojin na Conakry.