Wace illa juyin mulkin Nijar zai yi wa duniya?

Asalin hoton, AFP
Waɗanda aka ɗorawa alhakin tsaron Zaɓaɓben Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum su suka hamɓarar da gwamnatinsa.
Shugaba Bazoum ya kasance na farko da ya gaji shugaban da wa'adin mulkinsa ya kammala karon farko tun bayan da Nijar ta samu ƴanci a shekara ta 1960.
Amma a halin yanzu waɗanda suka kama shi sun yi watsi da tanadin kundin mulkin ƙasar ta hanyar naɗa Janar Abdourahmane Tchiani a matsayin shugaban kasa.
Nijar na a wani muhimmin yanki ne a Afirka da aka fi sani da Sahel wanda ya ke fama da ayyukan masu ikirarin jihadi, kuma yanki ne da gwamnatocin sojoji suka kewaye shi.
Kasashen Yammacin duniya sun ɗauki yankin a matsayin wurin da karya doka da oda ya samu gurin zama bayan tasirin Rasha a kasar.
Mene ne ya sa Nijar ke da muhimmanci?
A matsayinta ta ƙasa mafi faɗin ƙasa a Afirka ta Yamma kuma mahaɗar hanyoyin ƙasashe ce.
A siyasance dai an yi wa Nijar kallon ƙasar da dimokuraɗiyya ta samu gurin zama tsawon shekaru a lokacin da makotanta irin su Mali da Burkina Faso suka faɗa juyin mulkin soja.
Kasashen Faransa da Amurka sun haɗa gwiwa da ita wajen yaƙar masu ikirarin jihadi.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana Nijar a matsayin abokiyar yaƙi da ta'addanci kan ƙungiyoyin Islama daban-daban masu alaƙa da IS da kuma Al-Qaeda.
Ta fuskar tattalin arziki kasar ta na da wadatar albarkatun 'Uranium', har an sanya wa ɗaya daga cikin manyan titunan birnin Yamai suna Avenue de 'Uranium.
Sai dai duk da haka ana kallon al`ummar ƙasar a matsayin matalauta.

Mene ne dalilin juyin mulkin?
Yankin Sahel, shi ne ya fi kowanne yanki fama da ƙalubalen tsaro a duniya, yanzu kuma dimokuraɗiyya ta shiga tsaka-mai-wuya.
Kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin addini sun yi nasara ta hanyar mamaye yankuna da dama tare da kai hare-hare a iyakokin Mali da Nijar da kuma Burkina Faso.
Sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar sun bayyana tabarbarewar tsaro a matsayin dalilin hamɓarar da gwamnatin, duk da cewa Nijar ta fi kasashen Mali da Burkina Faso ɗaukar matakan kawo karshen tashe-tashen hankula.
Yawaitar tashe-tashen hankulan da rashin tsaro sun sa wasu na ganin sojoji ne kawai za su iya magance matsalar, wannan ce ta sa al`umma suke goyon bayan juyin mulki a wasu yankuna.
To sai dai kuma babu tabbas cewa gwamnatin sojan kasar za ta fi samun nasara wajen tunkarar masu tayar da ƙayar baya fiye da gwamnatin da aka hambarar.
Kodayake karɓe mulki bai yi tasiri a kasashen da suke maƙotaka da Nijar ba.
Ko juyin mulki a Mali da Burkina Faso ya dakatar da ayyukan masu ikirarin jihadi?
Wani abin da ke kara rashin kwanciyar hankali a yankin shi ne sauyin yanayi, wanda ke haifar da kwararowar hamada zuwa Kudu da sahara.
Masana sun ce yanayin zafi a yankin Sahel na karuwa fiye da ko ina a duniya.
Kasar Faransa wacce ta yi wa Nijar mulkin mallaka, ta yi kakkausar suka kan yadda sojoji suka karɓe ragamar mulkin kasar.
A wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Faransa ta fitar ta ce shugaba Bazoum shi ne shugaban da Faransa ta amince da shi, don haka Janar Tchiani ba shugaba ba ne.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken, hadin gwiwa da Kugiyar Ƙasashen Afirka da ECOWAS da Tarayyar Turai da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da juyin mulkin.
Amma shugaban ƙungiyar sojojin haya ta Rasha watau Wagner Group, Yevgeny Prigozhin ya bayyana juyin mulkin na Nijar a matsayin nasara.
Ya kuma ƙara da cewa abin da ya faru rikici ne tsakanin al'ummar Nijar da masu mulkin mallaka, kodayake ba a tantance sahihancin waɗannan kalamai ba.
Ana ganin kungiyoyin masu ikirarin jihadi da sojojin haya na Wagner sun yi mummunan tasiri a Nijar.
An dai ga wasu masu goyon bayan juyin mulkin suna ɗaga tutar Rasha tare da ta Nijar.

Asalin hoton, Getty Images
Kafin juyin mulkin shugaba Bazoum ya yi korafin game da yadda Wagner ta ke yaɗa labaran karya kan gwamnatinsa.
Babu shakka Wagner ta yi amfani da ma'adinan wasu kasashen Afirka wajen samar da kudaden gudanar da ayyukanta za ta so yin haka a Nijar.
To sai dai Amurka ta ce babu wata alama da ke nuna cewa sojojin haya na Wagner na da hannu wajen hambarar da gwamnatin Bazoum.
Juyin mulkin Nijar ya sa yankin da ke fama da tashin hankali ya ƙara samun rauni
Yanzu akwai fargabar sabon shugabancin na Nijar zai juya wa ƙasashen yammacin duniya baya ta hanyar haɗa kai da Rasha.
Idan haka ta faru, za su bi tsarin da Burkina Faso da Mali suka ɗauka na haɗa kai da Moscow tun bayan juyin mulkin da su ka yi.
Gwamnatin Shugaba Bazoum ta taimaka wa kasashen Turai wajen dakile kwararar bakin haure ta teku, har ma ta karɓi daruruwan bakin haure daga cibiyoyin da ake tsare da su a Libiya.
Ya kuma dakile ayyukan masu safarar mutane a hanyar wucewa tsakanin wasu kasashen Yammacin Afirka da kuma wadanda ke bin hanyar Arewa.
Ina mafita yanzu?










