Abubuwan tarihi biyar da suka janyo rikici a Haiti

Haiti

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Paula Rosas and Americas Visual Journalism Team
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Yayin da Talauci ya yi wa kasar kanta, ga samun aukuwar bala'o'i a wasu lokuta , ga kuma tarin bashi da ya yi wa kasar katutu sannan da rashin tabbatacciyar gwamnati.

Haiti na neman zama kasar da rikici ke son samun wurin zama, inda kasashen duniya ke kallon kasar a matsayin wadda ta kasa magance wadannan tarin matsaloli.

Kisan da aka yi wa shugaban kasar, Jovenel Moïse a 2021, tare da mamayar da kungiyoyin 'yan daba suka yi wa kasar, ya haddasa mutuwar dubban mutane, tare da jefa kasar cikin halin rashin tabbas.

To amma rikicin kasar na da tarihi mai yawa, inda wasu matsalolin suka samo asali tun lokacin samun 'yancin kan kasar, wadanda kuma suka ci gaba da wanzuwa daruruwan shekaru.

Ga wasu matsalolin ƙasar na tarihi waɗanda suka taimaka wajen jefa ƙasar cikin halin da take ciki ma yanzu.

1. Rikicin siyasa

Haiti ta faɗa cikin rikicin siyasa tun lokacin samun 'yancin kan kasar a 1804.

Fiye da ƙarni biyu kenan, Haiti na fama da mulkin kama-karya, a maimakon mulkin dimokraɗiyya, a wasu lokuta ma har ƙasashen waje ne ke saka baki.

Shugaban ƙasar na farko, Jean-Jacques Dessalines, ya haramta cinikin bayi, amma kuma ya taƙaita duk wani ikon komai ga kansa, inda ya ayyana kansa a matsayin shugaban komai a ƙasar har na tsawon rayuwa, watanni bayan haka ya samar wa kansa matsayin Sarki Jacques na farko a Haiti.

Sai dai daga baya an kashe shi, kamar yadda ake kashe sauran shugabannin ƙasar da suka biyo bayansa.

Batun wanda zai gaje shi ya haifar da yaƙin basasa a ƙasar a ƙarni na 19, inda aka samu sauyin shugabanni daban-daban.

Da yawa daga cikinsu 'yan tawaye ne suka kashe su bayan shekaru kaɗan a kan mulki inda wasu kuma suka yi gudun hijira suka bar ƙasar.

Amurka ta mamayi Haiti a shekarar 1915, sakamkon fargabar katsalandan din ƙasar Jamus da kuma kare muradun Amurka a tsibirin.

Ba su fice daga ƙasar ba har sai shekarar 1945, duk da cewa a lokacin sun yi ƙoƙarin sauya dokokin ƙasar, daga ciki shi ne bai wa 'yan kasashen waje damar sayan fili a ƙasar ( wani abu da a baya ke zama haramun a ƙasar) wanda kuma hakan na kawo cikas ga kamfanonin Amurka a ƙasar.

François and Jean Claude Duvalier

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mafi yawan ƙarni na 20 cike yake da rikicin siyasa a ƙasar, inda gwamnatocin François "Papa Doc" Duvalier tare da ɗansa, Jean-Claude, da ake yi wa laƙabi da "Baby Doc", suka ci karensu babu babbaka.

A tsawon shekara 29 da Duvalier ya yi mulki, cin hanci da rashawa sun yi wa ƙasar katutu, sannan wasu tsare-tsare na zalunci sun tilasta mutuwa ko ɓacewar kusan mutum 30,000 a ƙasar.

Bayan yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a 1958, sai shugaba François Duvalier ya yi yunƙurin kafa sojojinsa na ƙashin kai da nufin kawar da sojojin ƙasar.

Ya kafa wata runduna ta masu tayar da ƙayar baya mai suna ''Tonton Macoutes'', waɗanda suka riƙa uzzura wa al'umma tare da kare shugaban ƙasar da kuma muzguna wa waɗanda ke adawa da shi.

Haka ma zamanin mulkin ɗansa Jean-Claude, ya ci gaba da amfani da wannan salo, har sai da aka yi masa bore tare da tilasta masa yin gudun hijira a shekarar 1986.

Bayan juye-juyen mulki masu yawa, ƙasar Haiti ta zaɓi shugaban mulkin farar hula a shekarar 1990, Jean-Bertrand Aristide wanda ya samu goyon bayan talakawan ƙasar ya zama shugaban farar hula na farko a ƙasar.

To sai dai bayan wata bakwai da hawansa mulki, sojoji suka kifar da gwamnatinsa, inda shi ma ya yi gudun hijira zuwa ƙetare.

Aristide ya samu damar sake komawa Haiti a shekarar 1994, sakamakon sanya hannu da sojojin Amurka suka yi.

Shekara biyu bayan haka, aka zaɓi René Preval, a matsayin shugaban ƙasar da ya gaji mista Aristide, aka kuma sake zaɓen sa a watan Nuwamban 2000.

2. Rikice-rikice masu ƙarfi

Haiti ƙasa ce da rikici ya mamaye, saboda ƙungiyoyin 'yan daba kusan 200 da ke iko da manyan yankunan ƙasar, musamman babban birnin ƙasar, Port-au-Prince.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin ya raba kusan mutum 314,000 da muhallansu.

Tun bayan kafa rundunar ''Tonton Macoute'' da Papa Doc ya yi a shekarar 1958, masu aikata laifuka suka ci gaba da wanzuwa a ƙasar, musamman idan aka samu kafa sabuwar gwamnati.

Tun lokacin da shugaba Aristide ya soke rundunar sojin ƙasar, da cin hanci ya yi wa katutu, ƙasar ta kasa samun ƙarfin yaƙar ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

A lokacin ne, masu safarar ƙwaya a ƙasar suka riƙa aiki tare da masu safarar ƙwaya na Colombiya, kamar yadda darakta cibiyar lura da al'amuran kudancin Amurka da yankin Caribbean na jami'ar Essex ya bayyana.

Wata mummunar girgizar ƙasa da aka yi a ƙasar a shekarar 2010, ta bai wa 'yan daba da dama da ke gidajen yari damar tserewa.

Lamarin dai ya ƙara wa ƙungiyoyin 'yan dabar ƙarfi a ƙasar, inda suka yi ta garkuwa da mutane tare da kai wa 'yansanda da kafofin yaɗa labarai da 'yan siyasa hare-hare, lamarin da ya ƙara jefa rayuwar al'ummar ƙasar cikin hatsari.

A yanzu duka ƙungiyoyin 'yan daban na yin mubaya'a ga ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin 'yan daba biyu a ƙasar, wato ''G-9 and Family'', ƙarƙashin jagorancin Jimmy Chérizier, da aka fi sani da "Barbecue", ko kuma ''G-Pep'' ƙarƙashin jagorancin Gabriel Jean-Pierre.

Ƙungiyar G-9 da aka kafa a shekarar 2020, - ita ce ke iko da manyan cibiyoyin tattalin arzikin ƙasar, kamar tashohin mai na babban birnin ƙasar, da cibiyoyin shige da ficen birnin Port-au-Prince.

Ita kuwa ƙungiyar G-Pep na iko ne da Cité Soleil, wuri mafi yawan jama'a kuma talakawan da ke zaune a babban birnin ƙasar, kuma tana samun goyon bayana PHTK mai adawa, to amma kawo yanzu ba a sani ba ko tana samun tallafin kuɗi da kayan aiki daga ƙungiyar.

Alƙaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa yawan mutanen da suka mutu sakamakon ayyukan 'yan daba a shekarar da ta gabata ya ninka, inda aka kashe fiye da mutum 5,000.

Rundunar 'yansandan ƙasar ba ta da wadatattun jami'an da za su yaƙi 'yan dabar, lamarin da ya sa da dama suka bar aikin a shekarar da ta gabata, kamar yadda wani rahoton MDD ya nuna.

3. Bashi da katsalanda daga ƙetare

Haiti ce ƙasar yankin latin ta farko da ta fara samun 'yancin kai, kuma ita ce tsohuwar jamhuriyar baƙar fata a duniya, sannan kuma ƙasar jamhuriya ta biyu a yankin Yammacin duniya bayan Amurka.

Tawayen da ƙasar ta fara ya faro ne a shekarar 1791, inda ta yi wa tsohuwar uwargijiyarta, Faransa tawaye a shekarar 1804 kuma ta ayyana 'yancin kanta.

To sai dai 'yancin kan ya zo da matsala.

Koƙarin da ƙasar ta yi na samun 'yancin kai daga Faransa ya lalata mafi yawan harkokin noman ƙasar da abubuwan more rayuwa, lamarin da ya jefa ƙasar cikin matsin tattalin arziki.

Mafi yawan amfanin noman na Faransa ne don haka tsohuwar uwargijiyar tata ta buƙaci Haiti ta biya ta tarar lalata mata amfanin gonar.

An illustration showing a white French sailor throwing black men overboard

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tutsun da bayi suka yi a ƙasar ne ya haifar da samun 'yancin kan Haiti, inda Faransa ta buƙaci ta raba gari da ƙasar saboda asarar kayan amfanin gona da ta yi.

Haiti ta ci gaba da karɓo bashi mai yawan gaske daga bankunan Amurka da Faransa da Jamus tare da kuɗin ruwa mai yawan gaske, lamarin da ya tilasta wa ƙasar kashe mafi yawan kasafin kudinta wajen biyan basukan.

Sai a shekarar 1947 ne Haiti ta kammala biyan tara ga masu gonakin da suka lalata wa amfanin gona na Faransa, to sai dai ba Faransa ce kaɗai ƙasar da ta talauta Haiti ba.

A shekarar 1915, kamfanin jiragen ruwan Amurka ya aike da wakilai zuwa birnin Port-au-Prince domin kare muradun kamfanonin Amurka a ƙasar, wani abu kuma da ya ƙara dagula rikicin siyasar ƙasar a lokacin.

A shekarar 1922, Amurka ta tilasta wa Haiti karɓo bashi daga bankin Wall Street, lamarin da ya sake jefa ƙasar cikin matsalar bashi.

A mother with two children in Haiti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Talauci da yunwa sun jefa ƙananan yara a Haiti cikin mayuwacin yanayi, inda da dama suka fuskanci cuutukan da suka shafi yunwa.

4. Talauci

Yayin da ake tsaka da matsalar rikicin siyasa, da na 'yan daba a gefe guda kuma talauci na kara samun wurin zama a ƙasar.

Haiti ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa talauci a yankin latin da na Caribbean, kuma ɗaya daga cikin ƙasashe matalauta a duniya.

Arzikin da ƙasar ke samu a cikin gida shi ne dala 3,306 a shekarar 2022, kamar yadda alƙaluman Bankin duniya suka nuna, yayin da mafi tsaka-tsakin da ƙasar yankin Latin da na Caribbean ke samu shi ne dala 12,269.

Ƙasar ce ta 163 cikin kasashen 191 da Majalisar Dinkin Duniya ta ce aka fi samun ci gaban ɗan'adam

Fiye da rabin al'ummar ƙasar ne ke rayuwa cikin tsananin talauci, inda mafi yawan al'ummar ƙasar ke mutuwa a shekarun 64 saboda rashin kyawun yanayin rayuwa a ƙasar.

Yunwa da rashin abinci mai gina jiki sun kai maƙura a ƙasar, lamarin da ke barazana ga rayuwar mafi yawan al'ummar ƙasar, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

A shekarar 2023, yara miliyan uku ne suka buƙaci tallafin jin ƙai a ƙasar, inda aƙalla yaro guda cikin yara huɗu ya kamu da cutar yunwa, adadi mafi yawa da aka taɓa samu a duniya.

Haka kuma ƙasar na ɗaya daga cikin ƙasashen da cutukan tarin tibi da kwalara suka yi ƙamari.

A lokacin girgizar ƙasar 2010 an samu kusan mutum 10,000 da suka mutu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a ƙasar

Haka kuma kashi 1.7 na matasan ƙasar na ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDs, kamar yadda alƙaluman Hukumar Majalisar dinkin duniya da ke kula da cutar AIDs.

Wanna kari ne kan bayanan da ake da shi a ƙasa cewa kusan kashi 40 na mutanen ƙasar marasa ilimi ne, kamar yadda alƙaluman Bankun Duniya suka nuna, kuma rabin yaran ƙasar ne ke zuwa makaranta, kamar yadda alƙaluman hukumar kula da ilimin yara ta Majalisar ta dinkin duniya, Unicef, suka nuna.

Matsalar bala'o'in da suka shafi Haiti da rashin kyawun abubuwan more rayuwa da rashin ƙarfinta, ya sa ƙasar ta ƙara dogara da tallafin da ƙasashen duniya ke aika mata.

An yi ƙiyasin cewa tsakanin shekarar 2011 zuwa 2021, ƙasar da ke yankin Caribbea ta samu tallafin aƙalla dala biliyan 13.

A woman is crying in the ruins of her house

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kashi 96 cikin 100 na al'ummar Haiti sun fuskanci matsalar bala'o'i.

5. Aukuwar bala'o'i a ƙasar

Ƙasar Haiti ta fuskanci matsalolin bala'o'i da suka haɗa da girgizar ƙasa, sakamakon yanayin yankin da ƙasar take.

Haiti na wani wuri da ke kan layin ' Atlantic hurricane' sannan kuma tana tsakanin layuka biyu da take cikin hatsarin samun girgizar ƙasa.

To sai dai, wasu daga cikin waɗannan bala'o'i na aukuwa ne sakamkon ayyukan ɗan adam.

Talauci da kusan durƙushewar ƙasar sun sanya al'ummar ƙasar sare dazuka, lamarin da ya ƙara yi wa muhalli bazarana, ta yadda take samun matsalar munanan guguwowi a ƙasar, wani abu kuma da ke ƙara yin barazana ga samun girgizar ƙasar.

Kusan kashi 96 na al'ummar ƙasar, wato kusan miliyan 12 ne suka fuskanci munanan bala'o'in.

Bankin Duniya ya yi ƙiyasin cewa kashi 98 cikin 100 na dazukan Haiti ne aka sare, domin samun itacen girki da gawayi, wanda kuma ke janyo zaizayewar ƙasa, da ƙarancin ruwan sha.

Ba fannin noma kawai zaizayewar ke yi wa illa ba, lamarin na ƙara jefa ƙasar cikin hatsarin guguwa da ke shafar ƙasar a wasu lokuta, lamarin da ke haifar da ambaliyar ruwa da zaizayewar ƙasa.

Alal misali a shekarar 2016 guguwar Hurricane Matthew ta haddasa asara ga kusan kashi 32 na arzikin da ƙasar ke samu.

Wannan ya haifar da ƙarin munanan girgizar ƙasa a shekarun baya-bayan nan, kamar guguwar nan mai maki 7 da ta razana ƙasar a 2010, inda mutum 250,000 suka mutu, kamar yadda bankin duniya ya bayyana.

Lamarin da ya haifar wa ƙasar asarar kusan kashi 120 na arzikin da ƙasar ke samu a cikin gida.

A yayin da a wasu ƙasashen duniya irin su Chilke da Japan, aka samu girgizar ƙasa irin wannan ko wadda ta zarta wannan muni, amma ba ta kashe mutanen da suka kai waɗanda suka mutu a Haiti ba.

A shekarar 2021 ƙasashen biyu sun fuskanci munanan girgizar ƙasa da suka kai maki 7.2 da ta kashe mutum 2,000.

Masana na gargaɗin cewa illolin sauyin yanayi, zai iya dagula yanayi a ƙasar da ta fuskanci munanan bala'o'i a duniya.