Abubuwan ban mamaki da suke faruwa a Afcon a Ivory Coast

Afcon 2024

Asalin hoton, Getty Image

An fara wasannin cin kofin nahiyar Afirka gasa ta 34 da Ivory Coast ke karbar bakuncin tun daga ranar Asabar 13 ga watan Janairun 2024.

Tun daga makon farko manyan kasashe suka fara shan kashi a gasar, bayan da kananan tawagogi ke nuna cewa karfi ya kawo ba tsoro a idanunsu.

Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw ya yi bitar abubuwan ban mamaki da suke faruwa a babbar gasar tamaula ta Afirka.

Rukunin farko ya fara wasa ranar Asabar tsakanin mai masaukin baki Ivory Coast da Guinea-Bissau, inda aka doke Guinea Bissau 2-0.

Hakan ya sa farin ciki a zukatan magoya bayan Ivory Coast da ke shirya wasannin a karon farko cikin shekara 40.

Ranar Lahadi 14 ga watan Janairu a wasa uku da aka yi ne gasar ta dauki wani salon da manyan tawaga suka sha da kyar a karawar da suka yi.

Super Eagles da Equatorial Guinea sun tashi 1-1 a wasan farko a rukuinin farko, kuma minti na 36 da fara wasa Equatorial Guinea ta fara cin kwallo ta hannun, Iban Salvador, bayan minti biyu kuma Victor Osimhen ya farke.

Daga nan rukuni na biyu ya fara wasa, inda aka tashi 2-2 tsakanin Masar da Mozambique, kuma Masar ce ta fara cin kwallo ta hannun Mostafa Mohamed.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Daga baya Mozambique ta farke ta hanun Witi a zagaye na biyu, sannan Clesio Bauque ya kara na biyu.

Daf da za a tashi ne Mohamed Salah ya farke a bugun fenariti da ta kai Masar ta tashi 2-2 da Mozambique.

Daya wasan rukuni na biyu kuwa Cape Verde ce ta doke Ghana 2-1.

Kofin Afcon na hudu da Ghana ta lashe shi ne a 1982 daga nan ta kai daf da karshe a 2012 da 2013 da 2017 da kai wa zagayen karshe a 2015.

Hakan ya sa ake ganin Ghana tana cikin wadanda ake sa ran za ta taka rawar gani a Ivory Coast, duk da cewa ta kasa yin abin kirki a Kamaru a 2021.

Ghana tana fama da kalubale a wasannin da take yi, bayan da ta kasa yin abin kirki a gasar kofin duniya a Qatar a 2022, wadda aka fitar bayan karawar rukuni.

Cape Verde ce ta fara cin kwallo ta hannun Jamiro Gregory Monteiro Alvarenga, sai Ghana ta farke ta hanun Alexander Djiku, bayan hudu, amma daf da za a tashi ne aka kara kwallo na biyu a ragar Ghana ta hannun Garry Rodrigues.

Ranar Litinin 15 ga watan Janairu mai masaukin baki ta fara da kafar dama da cin Gambia 3-0, wadda ta kare karawar da ƴan kwallo 10 a fili, bayan da aka bai wa Ebrima Adams jan kati.

Dan wasan Gambia, Adams shi ne na farko da aka kora a wasa a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta bana.

Daya wasan na rukuni na uku an tashi 1-1 tsakanin Kamaru da Guinea, koda yake Guinea ta karasa wasan da ƴan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka sallami Francois Kamano.

Wasan farko a rukuni na hudu kuwa an tashi 1-1 tsakanin Algeria da Angola, kuma Algeria ce ta fara cin kwallo a minti na 18 da fara wasa ta hannun Baghdad Bounedjah.

Daga baya ne Angola ta farke ta hannun Cristovao Paciencia Mabululo a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Afcon 2024

Asalin hoton, Getty Images

A wasa na biyu ne a rukunin farko Najeriya ta ci Ivory Coasr 1-0, inda William Troost-Ekong ya ci wa Super Eagles kwallon a bugun fenariti.

Hakan ya sa mai masukin baki cikin matsi, bayan da take da maki uku a wasa biyu a rukunin farko, Najeriya ta hada maki hudu.

Sai kuma aka tashi 2-2 tsakanin Masar da Ghana, wannan sakamakon bai yi wa tawagogin biyu dadi ba, wadanda suke da maki bibiyu a wasa biyu a rukuni na biyu.

Ita kuwa Senegal hada maki shida ta yi a karawa ta biyu a rukuni na uku, bayan da ta dura 3-1 a ragar Kamaru.

Bayan da aka ci Indomitable Lions 2-1 ne ta yi ta saka kaimi ko ta zare, kwallo, amma daf da za a tashi wasa Senegal ta kara na uku ta hannun Sadio Mane.

Wata karawar da ba a manta da ita ba a Afcon ita ce wadda Equatorial Guinea ta sharara 4-0 a ragar Ivory Coast ta kuma ja ragamar rukunin farko.

Daya daga karawar da ta ja hankalin masu bibiyar tamaula, wadda aka kara a filin wasa na Ebimpe’s Alassane Ouattara Olympic Stadium.

Equatorial Guinea ta ci kwallon farko ta hannun Emilio Nsue tun kan hutu, sannan Pablo Ganet ya kara na biyu, bayan da suka koma zagaye na biyu.

Daga nan ne Emilio Nsue ya kara na biyu na uku a karawar, sannan Jannick Buyla Sam ya zura na hudu a raga, saura minti biyu a busa tashi.

Wannan sakamakon ya kai Ivory Coast mataki na uku a rukunin farko, yayin da Nageriya ce ta biyu da maki bakwai iri daya da na Equatorial Guinea.

Karon farko da Eguatorial Guinea ta kai zagayen gaba a gasa uku baya, kuma an yi mamaki da ta kare a mataki na daya a rukunin da Super Eagles da Ivory Coast ke ciki.

Emilio Nsue

Kyaftin din Equatorial Guinea, Nsue ya ci kwallo rigis, bayan da kasar ta ci Guinea Bissau 4-2, wadda tauni ta kai zagayen ƴan 16.

Nsue shi ne na farko da ya ci kwallo uku rugus a Afcon a karon farko tun 2008, bayan da ake sa ran irin wannan bajintar da ko dai Sadio Mane ko Mohamed Salah ko Victor Osimhen da sauransu.

Yadda aka kammala samun maki a rukunin farko

  • Equatorial Guinea 3 2 1 0 0 9 3 6 7
  • Nigeria 3 2 1 0 0 3 1 2 7
  • Ivory Coast 3 1 0 2 0 2 5 -3 3
  • Guinea-Bissau 3 0 0 3 0 2 7 -5 0
Afcon 2023

Asalin hoton, Getty Images

A rukuni na uku Cape Verde ta tashi 2-2 da Masar, hakan ya sa ta ja ragamar rukuni na biyu da maki bakwai, yayin da Masar ta yi ta biyu da maki uku.

Karon farko da Masar ta kare wasannin rukuni ba tare da cin wasa ba, bayan da take da kofin Afcon bakwai, ita ce kan gaba a yawan lashe shi.

Ghana kuwa ta ci karo da tasgaro, bayan da ta tashi 2-2 a karawar karshe a rukuni na biyu da Mozambique, hakan ya sa ta samu maki biyu a wasa uku.

The Black Stars ce ta fara cin kwallo biyu a bugun fenariti ta hannun Jordan Ayew, kai kashe Ghana ta hada maki ukun da take bukata.

Sai dai kuma daf da za tashi wasa ne Mozambique ta zare daya ta hannun Geny Catamo a bugun fenariri, sannan Reinildo Mandava ya kara na biyu.

Hakan ya sa Ghana ta yi ban kwana da wasannin bana, kenan ta maimaita rashin kwazon da ta yi a Kamaru a 2021 da aka fitar da ita a karawar cikin rukuni.

Cape Verde

Tawagar da ake kira The Blue Sharks ta fayyace cewar ba ta je Ivory Coast bane domin yawon bude ido, bayan da ta mamaye Ghana a karawar da ta yi nasara da cin 2-1.

Gasa ta biyu kenan da suke buga a Afcon, wadda ta fara da halartar wasannin 2013, wadda ta kai gurbin daf da na kusa da na karshe.

A wasa na biyu a cikin rukuni Cape Verde ta ci Mozambique cikin ruwan sanyi da cin 1-0, kuma tsohon dan wasan Manchester United, Bebe ya ci kwallon mai kayatarwa.

Haka kuma tawagar ce ta farko da kai gurbin zagaye na biyu da jan ragamar rukuni na biyu a jadawalin da take tare da Masar da Ghana, wadanda suka lashe Afcon 11 a tsakaninsu.

Yadda aka kammala samun maki a rukunin na biyu

  • Cape Verde 3 2 1 0 0 7 3 4 7
  • Egypt 3 0 3 0 0 6 6 0 3
  • Ghana 3 0 2 1 0 5 6 -1 2
  • Mozambique 3 0 2 1 0 4 7 -3 2

Senegal ba ta yi karo da wani koma baya ba, bayan da ta yi nasara a dukkan karawa uku da ta yi a rukuni na uku, wadda ta hada maki tara.

Kamaru ce ta biyu a rukuni na uku, bayan da ta ci Gambia 3-2, kuma Indomitable Lions ce ta fara cin kwallo ta hannun Karl Toko Ekambi.

Daga baya Gambia ta farke ta hannun Ablie Jallow, sannan ta kara na biyu ta hannun Ebrima Colley.

Kamaru ta kara sa kaimi da ta kai Gambia ta ci gida ta hannun James Gomez, sannan Christopher Wooh ya zura na uku a raga.

Fafatawar ta yi wa Kamaru tsauri, amma dai ta kai zagayen gaba da kyar da gumin goshi da maki hudu, biye da Senegal mai maki tara.

Lamine Camara

Da yake Senegal ta fara gasar bana da kafar dama da cin Gambia 3-0, maki ukun da tun farko aka sa ran mai rike da kofin za ta hada a fafatawar.

To sai dai kwallo biyun da Lamine Camara ya ci ne a wasan ya ja hankalin masu bibiyar tamaula, wanda shi ne ya lashe kyautar gwarzon ɗan kwallon kafa a fafatawar.

Shekararsa 20, amma kwallon da ya buga kai kace wanda ya dade yana taka leda ne. Teranga Lions na fatan kare kofin da ta dauka a Kamaru, yayin da tawagar ke fatan Camara da Sadio Mane za su kai Senegal ga yin nasara.

Yadda aka kammala samun maki a rukunin na uku

  • Senegal 3 3 0 0 0 8 1 7 9
  • Cameroon 3 1 1 1 0 5 6 -1 4
  • Guinea 3 1 1 1 0 2 3 -1 4
  • Gambia 3 0 0 3 0 2 7 -5 0

Ranar Talata rukuni na biyar ya fara karawa, inda Namibia ta doke Tunisia 1-0, kuma Deon Hotto ya ci kwallon sauran minti biyu a tashi daga fafatawar.

Wasan farko kenan da Namibia da ake kira Brave Warriors ta yi nasara a Afcon a tarihi.

Mauritania ma ta samu wani sakamako mai ban mamaki a gasar kofin Afirka, bayan da ta doke Algeria 1-0 a filin wasa na Stade de la Paixin Bouake.

Wannan sakamakon ya sa an yi waje da Algeria daga gasar Afcon da ake yi a Ivory Coast, yayin da Mauritaniya ta samu kai wa zagaye na biyu.

Wannan shi ne karon farko da Mauritania ta ci wasa a Afcon da kai wa zagaye na biyu a babbar gasar tamaula ta nahiyar Afirka.

Tun farko Algeria na fatan tashi koda canjaras ne, amma kuma ta yi rashin nasara a fafatawar da ta bai wa Mauritania damar zuwa matakin kungiyoyi 16 da za su ci gaba da zagaye na biyu daga ranar Asabar.

Algeria, wadda ta dauki Afcon a 2019 haka ta yi ta karshe a wasannin da aka yi a Kamaru.

Haka kuma tawagar ta kasa samun gurbin shiga gasar kofin duniya a karawar cike gurbi da ta kara da Kamaru.

Yadda aka kammala samun maki a rukunin na hudu

  • Angola 3 2 1 0 0 6 3 3 7
  • Burkina Faso 3 1 1 1 0 3 4 -1 4
  • Mauritania 3 1 0 2 0 3 4 -1 3
  • Algeria 3 0 2 1 0 3 4 -1 2
Afcon 2023

Asalin hoton, Getty Images

Namibia da ake kira Brave Warriors ta shiga Afcon a mataki na 115 a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon kafa a duniya, wadda ta ci Tunisia.

Rashin kirkin tamaula, Tunisia ta bai wa Namibia tazarar gurbi 87, amma hakan bai hana ta yi rashin nasara ba da suka hadu.

A wasan farko Namibia ta yi nasara a kan wadda ta taba lashe Afcon a 2004, kuma wasan farko da ta ci a tarihin gasar.

Bayan da aka kammala wasa uku a rukuni na biyar Mali ce ta daya da maki shida, sai Afirka ta Kudu da maki hudu da kuma Namibia ta uku da maki hudu.

Tunisia ta yi ban kwana da wasannin bana da maki daya daga wasa uku a rukuni na biyar.

Yadda aka kammala samun maki a rukunin na biyar

  • Mali 3 1 2 0 0 3 1 2 5
  • Afirka ta Kudu 3 1 1 1 0 4 2 2 4
  • Namibia 3 1 1 1 0 1 4 -3 4
  • Tunisia 3 0 2 1 0 1 2 -1 2

Rukuni na shida na karshe ba a yi wasu abuwan da suka ja hankalin masu bibiyar tamaula ba.

Kuma tawaga biyu ne suka kai zagayen gaba, bayan da Morocco ta hada maki bakwai da Jamhuriyar Congo mai maki uku.

Tuni Zambia da Tanzaniya suka yi ban kwana da gasar bayan da suka kasa kai bantensu.

To sai dai ana sa ran Morocco za ta kara sa kaimi a zagaye na biyu, wadda ake sa mata tsammni a Ivory Coast, bayan da ta kai daf da karshe a gasar kofin duniya a Qatar a 2022, ita ce ta farko a Afirka da ta yi wannan kwazon.

Yadda aka kammala samun maki a rukunin na shida

  • Morocco 3 2 1 0 0 5 1 4 7
  • DR Congo 3 0 3 0 0 2 2 0 3
  • Zambia 3 0 2 1 0 2 3 -1 2
  • Tanzania 3 0 2 1 0 1 4 -3 2

Yanzu dai tawaga 16 ta kai zagaye na biyu da za a fara daga ranar Asabar, inda duk wadda ta yi ta daya da ta biyu a kowanne rukuni suka kai zagayen gaba kai tsaye, kenan su 12.

Dada nan aka zakulo hudu da suka yi mataki na uku da maki mai kyau, inda aka dauko Guinea arukuni na uku da Mauritania a rukuni na hudu da Namibia a rukuni na biyar da kuma Ivory Coast mai masaukin baki.