'Yan Najeriya sun harzuƙa kan kisan Goni Aisami da ake zargin sojoji sun yi
Daga Umar Mikail

Asalin hoton, Aliyu Bulama
Kisan malamin Musulunci Sheikh Goni Aisami, ɗan Jihar Yobe da ke arewacin Najeriya, ya ja hankalin 'yan ƙasar musamman ma'abota shafukan zumunta.
A cewar rundunar 'yan sanda ta Jihar Yobe, yanzu haka an kama mutum biyu da suka yi iƙirarin sojoji ne da ke aiki da bataliya ta 241 a garin Nguru na jihar.
Ana zargin John Gabriel da Adamu Gideon da harbin fitaccen malamin sau biyu, inda ya mutu nan take, kuma maharan suka yi yunƙurin guduwa da motarsa, kamar yadda kakakin 'yan sandan Yobe ya shaida wa BBC Hausa.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare a ranar Juma'a.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC Hausa cewa lamarin ya ɗan jawo fargaba a zukatan mutane saboda sojoji ne ake zargi da kisan malamin.
"Wajibi ne a gurfanar da azzaluman a gaban kotu kuma dole ne gwamnati ta biya iyalan sa cikakkiyar diyya," in ji Barista Audu Bulama Bukarti, fitaccen lauya kuma mai kare hakkin ɗan adam, ɗan asalin jihar ta Yobe - a shafinsa na Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Yadda maharan suka kashe Goni Aisami

Asalin hoton, Aliyu Bulama
Shehin malamin yana tuƙa motarsa ne a kan hanyar zuwa Gashua daga Nguru lokacin da wanda ake zargi, sanye da kayan gida, ya roƙe shi da ya rage masa hanya zuwa Jaji-Maji - duka a cikin jihar ta Yobe.
"Jim kaɗan kafin su isa Jaji-Maji, malamin ya tsaya zai yi fitsari," a cewar kakakin 'yan sandan Yobe DSP Dungus Abdulkarim.
"Dawowarsa cikin mota ke da wuya sai mutumin ya zaro bindigar AK-47 kuma ya harbe shi sau biyu."
Abdulkarim ya ƙara da cewa mutumin ya yi yunƙurin guduwa da motar malamin amma suka gaza saboda ta maƙale a cikin taɓo.
"Sai ya kira ɗaya wanda ake zargin wanda ya tuƙo wata motar daban zuwa wurin don ya taimaka masa. Cikin rashin sa'a sai birkin motarsa ya karye.
"Mutanen sun nemi taimakon wasu jami'an tsaro na sa-kai a Jaji-Maji. Lokacin da suka isa wurin sai suka tarar da gawar Goni Aisami."
DSP Abdulkarim ya ce 'yan sa-kai ɗin ne suka sanar da 'yan sanda halin da ake ciki kuma sun tarar da motocin da gawar lokacin da jami'ansu suka isa wurin.
Shi ma Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana kisan a matsayin "abin takaici" kuma ya ce "za a yi cikakken bincike don tabbatar da cewa waɗanda aka samu da laifi sun fuskanci hukunci".
'Abin mamaki waɗanda ya kamata su kare mu sun zama makasanmu'
Da safiyar Asabar ce aka samu labarin kisan Goni Aisami, wanda aka yi jana'izarsa da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin Asabar.
Shafukan sada zumunta sun cika da alhinin rasuwarsa, da kuma nuna ɓacin rai da abin da aka ce jami'an tsaro ne suka aikata.
"Abin tsoro ne a ce mutanen da ya kamata su tsare mu sun koma masu kashe mu. Muna buƙatar a yi wa Sheikh adalci. Wannan abu ya yi yawa," kamar yadda wata mai suna Amina Iliyasu ta bayyana a Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Kazalika, akwai kiraye-kirayen a hukunta waɗanda ake zargin.
Adamu Garba, wanda ɗan siyasa ne a jam'iyyar APC mai mulki ya ce: "Mutanen banza, waɗannan ba wakilan Rundunar Sojan Najeriya ba ne. 'Yan fashi ne da suka shiga aikin soja. Saboda haka ya kamata a yi musu shari'ar soja, a hukunta su bisa doka."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
__________________________________________________________________
Sheikh Goni Aisami fitaccen malami ne ɗan asalin garin Gashua a Jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Kafin a kashe shi, malamin yana gudanar da karatuttuka a wurare daban-daban, ciki har da tafsirin Al-Ƙur'ani a fadar Mai Martaba Sarkin Gashuwa Abubakar Umar Sulaiman.
Ana yi masa laƙabi da Baba Gwani Ustaz.











