Waiwaye: Matasa sun nutse a ruwan Legas, an sace kwamashina a Jihar Nasarawa

A wannan makon da muke bankwana da shi, abubuwa da dama sun faru a Najeriya, ciki har da sace kwamashina a Jihar Nasarawa da sako ƙarin mutane daga cikin fasinjojin jirgin ƙasa da 'yan bindiga ke garkuwa da su.

Kamar kowane mako, mun duba muku wasu daga cikin abubuwan da suka farun.

Matasa sun nutse a ruwan Legas yayin da suke murnar kammala sakandare

SP Benjamin

Asalin hoton, NG Police

Rundunar 'yan-sanda a Jihar Legas ta ce wasu matasa hudu sun nutse a ruwa a yayin da suke murnar cin jarrabawar kammala sakandire.

Lamarin ya afku ne a ranar Talata a tekun Elegushi da ke unguwar masu galihu ta Lekki.

Mai magana da yawun rundunar 'yan-sandan SP Benjamin Hundeyin, ya wallafa a shafinsa na tiwita cewa matasan sun nitse bayan sun karbi sakamakon jarrabawarsu daga makaranta.

Hukumar gudanarwar tekun ta ce mamatan na daga ckin dalibai 10 da suka je wajen don yin murnar samun nasara a jarrabawarsu ta kammala karatun sakandire.

Mai magana da yawun hukumar gudanarwar ya ce yaran sun bijire wa gargadin da jami'an da ke kula da tekun suka yi musu.

Kawo yanzu dai mahukunta ba su bayyana shekarun yaran ba ko kuma daga in da suka fito.

Jihar Legas dai na kewaye da ruwa da kuma wuraren shakatawa abin da ya sa mutane kan je don shakatawa ko kuma gudanar da wani biki a bakin teku.

Maharan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna sun sake sakin mutum huɗu

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rahotanni daga jihar Kaduna a arewacin Najeriya sun ce ƴan bindigar da suka kai hari kan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna a watan Maris sun sake sako mutum huɗu daga cikin fasinjojin jirgin da suke riƙe da su.

Mai shiga tsakani a sasantawa tsakanin maharan da iyalan fasinjojin Malam Tukur Mamu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

“An saki mutane huɗun ne a yau Juma’a da safe kuma sun zo har nan ofishina suka yi min godiyar shiga tsakani da na yi har maharan suka janye barazanar kashe su da suka yi a baya.

“Sun kuma roƙi dukkan masu ruwa da tsaki musamman gwamnatin tarayya da ta tsaurara matakan ceto sauran fasinjojin da ke hannun maharan saboda halin abin tausayi da suka baro su a cikin dajin ,” a cewar Tukur Mamu.

Zuwa yanzu babu tabbaci kan ko an biya kuɗin fansa kafin a sako mutanen, amma rahotanni na cewa fasinjojin na baya da aka saki sai da suka biya miliyoyin naira kafin su samu 'yancinsu.

Daga cikin fasinjojin da aka saka ranar Juma’a 19 ga watan Agustan har da dattijuwar da ta girmi dukkan fasinjojin, Mama Halimatu Atta mai shekara 90.

'Jihohin Sokoto, Kebbi, Borno, Bayelsa, Delta na cikin haɗarin ambaliya'

Ambaliyar ruwa

Hasashen hukumar kula da yanayi ta Najeriya ya nuna cewa za a iya samun ambaliyar ruwa a wasu sassan jihohin Sokoto da Kebbi da Borno da Bayelsa da kuma Delta a kwanakin da ke tafe.

Shugaban hukumar ta NiMet, Farfesa Mansur Matazu ne ya nuna haka a bayanan da ya gabatar a lokacin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, inda ya ce wasu yankuna a jihohin na fuskantar hadarin ambaliya.

Ya ce nazarin ya nuna musu cewa wadannan jihohi suna suka fi kasancewa cikin hadarin samun mamakon ruwan sama da zai iya haddasa ambaliya.

Ya kara bayani da cewa, “Yankunan da suka fi kasancewa cikin hadarin su ne sassan tsakiyar Borno

Jihar Borno da sassan arewacin Jihar Kebbi da na Jihar Sokoto.

Hadi da sassan tsakiyar Jihar Kaduna da wasu bangarorin Jihar Bayelsa da Jihar Delta.''

A cikin kwanakin nan dai ambaliya da mamakon ruwan sama ya haddasa ta janyo asarar rayuka da gidaje da gonaki a wasu jihohin Njaeriyar da suka hada da Kano da Jigawa da Gombe da Sokoto.

Hukumar kula da yanayin ta shawarci jihohin da ke fuskantar wannan barazana da su tashi tsaye wajen fadakar da jama'ar da ke zaune a wadannan yankuna tare da shawartarsu kan sauya matsuguni ko daukar matakan kariya.

'Yan bindiga sun sace Kwamishina a Jihar Nasarawa

Nasarawa

Asalin hoton, NG Police

Rundunar 'yan-sanda a Jihar Nasarawa da ke Najeriya ta tabbatar da sace Kwamishinan Yada Labarai da Al'adu na jihar Yakubu Lawal.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar DSP Ramhan Nansel, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Talata a Lafiya, babban birnin jihar.

A cewar jami'in hulda da jama'ar, da misalin karfe 9 saura minti 15 na daren Litinin 'yan-sandan da ke sintiri suka rinka jin harbe-harben bindiga a karamar hukumar Nassarawa-Eggon, daga nan suka je wajen.

Ya ce da suka je wajen sai suka tarar har wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun far wa gidan Kwamishinan Yada Labarai na jihar tare da yin awon-gaba da shi da karfin tsiya.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan-sandan ya ce tuni aka baza jami'an 'yan-sanda domin ceto kwamishinan.

Ya kuma bukaci dukkan wanda ya samu labari game da inda aka kai kwamishinan da ya taimaka domin kubutar da shi.

A ranar Asabar din da ta wuce ma, rahotanni daga karamar hukumar ta Nassarawa-Eggon suka ce wasu 'yan bindiga sun kai hari makarantar sakandiren kimiyya da ke garin inda suka kashe ma'aikaci daya a ciki.

Jami'an tsaro sun ceto mata shida da aka yi garkuwa da su a Kaduna

Ma'aikatar cikin gida da tsaro ta Jihar Kaduna ta ce jami'an tsaro sun fatattaki sansanin 'yan bindiga a yankunan Kuriga da Manini da ke karamar hukumar Chikun tare da ceto wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su.

Cikin wata sanarwa da ma'aiktar ta fitar mai dauke da sa hannun kwamishinan cikin gidan Samuel Aruwan, ta ce sakamakon wasu rahotanni da aka samu, jami'an tsaron sun dirar wa wasu yankuna da ake tsammanin sansanin 'yan bindiga ne tare da fatattakarsu baki daya.

Sanarwar ta kara da cewa, yayin wannan samamen sun ceto mutum shida da aka yi garkuwa da su wadanda dukkansu mata ne.

A cikinsu akwai wata mai suna Sahura Hamisu da Ramlat Umar.

Sauran sun hada da Saudat Ibrahim da Maryam Shittu da Fatima Shu'aibu da Khadija Muhammad wadda aka ceto da jaririnta.

Samuel Aruwan ya ce jami'an za su ci gaba da kai samame inda duk ake zaton maboyar 'yan bindigar ne.