Muhimmancin zuma ga rayuwar dan Adam

Asalin hoton, Getty Images
Daga maganin kwari zuwa kara tsawon rai, alfanun zakin zuma ya zarce kawai ciyar da kwarin da suka aikatu.
Hakan ba abin mamaki ba ne ganin cewa kudan zuma ya san abubuwa da dama kan zuma.
Ba wai suna samar da zuma ba ne kadai, su ma masu amfani da ita ne.
Idan ka mika wa kudan zuma da yake fama da rashin lafiya nau'ukan zuma, misali, zai zabi wanda ya fi dacewa da irin rashin lafiyarsa.
Mutane kuma na bukatar su dage idan aka zo batun sinadaran da ke tattare dazuma.
Shekaru da suka gabata, galibin kayan abinci masu gina jiki sun gaza ambaton haka, in ji kwararriya kan kwari, May Berenbaum ta Jami'ar Illinois.
Inganta Lafiyar Kudan Zuma
Tun lokacin, wasu jerin bincike da aka gudanar sun nuna cewa zuma cike take da sinadaran da ke da tasiri kan lafiyar kudan zuma.
Wasu sinadaran da ke cikin zuma na kara wa kudan zuma tsawon rai da kare shi daga yanayi na matsanancin sanyi da ba su ikon yakar kwayoyin cuta da waraka daga ciwo.
Binciken ya nuna yadda za a taimaki kudan zuma da ke fuskantar kalubale a shekarun baya-bayan nan daga kwari da rashin wajen zama.

Asalin hoton, Getty Images
Kwayoyin halitta na Enzymes da sinadaran vitamin da mineral
Zuma na kara wa shayi ko gasasshen burodi da nama dandano amma zuma ta sha gaban kara wa abu zaki.
Tabbas, ruwan zuma yana da zaki abin da suke amfani da shi domin inganta rayuwarsu amma tana tattare da kwayoyin halitta (enzyme) da sinadaran bitamin da ke bambanta zumar ya kuma inganta lafiyar kudan zuma.
Akwai kwari da dama da ke iya samar da zuma amma kudan zuma ne kadai yake iya samar da zumar da ake samu a kantina.
Wannan ba a dare daya ya faru ba, an dauki miliyoyin shekaru.

Asalin hoton, Getty Images
Kudan zuma ya banbanta da sarkin kwai kusan shekaru miliyan 120 da suka gabata a lokacin sauyin halitta da bazuwar tsirrai masu furanni.
Wannan sauyin da kuma sauyi a dabi'un zuma sun juyar da halittar dangin kudan zuma kusan 20,000 da aka sani a yanzu.
Kariya ta Lafiya

Masu bincike sun gano tasirin sinadarin da ke kare zuma daga lahanin bakteriya.
Sinadarin Abscisic na kara wa zuma kariya ta lafiya, da ke kuma warkar da raunuka a kan lokaci da daidaita yanayi na sanyi, a cewar bincike.
Sauran sindarai na rage barazanar wasu kwari. Alal misali, daya daga cikin abin da ya janyo karewar kudan zuma shi ne bai wa wasu kudajen zuma da suka samu lahani sinadarin abinci daga ‘ya’yan itatuwa.
Wasu sinadarai da ke kare zuma daga kamuwa da cutuka, da kuma nau’in bakteriya na foulbrood, inda nau’in ke da hadarin gaske, har ma aka ba da shawarar kona wajen adana zuma don rage yaduwarta.
Sinadaran dai na taimakawa wajen kara kariya ta lafiya musamman ga kwayoyin halitta.
Idan zuma suka ci nau’ukan abinci daga jikin itatuwa, suna kara wa kwayar halittarsu lafiya, kamar yadda aka ruwaito cikin mujallar tattalin arziki da ilimin kwari a 2017.

Asalin hoton, Getty Images
Kudan zuma na kuma iya zabar hanyar lafiya da suke so idan suka kamu da cutuka.
Wani masanin ilimin kwari, Silvio Erler da tawagarsa sun gabatar da kudajen zuma da suka harbu da cutuka har nau’i guda hudu. “Zabi kawai muka ba su,” a cewar Erler, wanda yanzu ke Cibiyar Julius Kuhun da ke Jamus.
Shin zuma na warkarwa?

Duk da irin alfanu na lafiya da zuma ke da shi, yana kuma cike da hadari.
Masu kiwon zuma a Amurka sun rasa kashi 45 cikin dari na zumar da suka tara tsakanin watan Afrilun 2020 zuwa Afrilun 2021, wanda shi ne rashi mafi muni a cikin shekara tun bayan binciken da wasu masu bincike ba don riba ba suka fara a 2006.
Yayin da masu kiwon zuma ke rage sauran zuma a ma’adana, adana zuma mai yawa na da muhimmanci.
Bincike ya nuna cewa zuma daban-daban da ake samu a kan bakaken itatuwan fure da wasu itatuwa, suna kare kai daga wasu nau’o’in baktériya.
Erler ya kwatanta hakan da kantin magani, inda ya ce muna bukatar hakan don ciwon kai da kuma ciwon ciki, sannan a cikin kantin maganin, muna wadannan duka.’’
Duk da irin alfanu na lafiya da kudan zuma ke da shi, yana kuma da hadari
Zuma na samun damar kirkiro da kantinsu muddin suka samu ganyayyaki da suka kamata – ba wai yawansu ko warwatsuwa da suka yi ba, amma daukacin lokacin girmansu, a cewar Berenbaum, wani wanda ya wallafa rahoto kan ilimin kwari a 2021 kan tasirin lafiya da zuma ke da shi .
Ana samun bambancin halittu musamman inda zuma ke rayuwa a kowace shekara.

Habaka nau’in furen na haifar da kudan zuma masu koshin lafiya, in ji Arathi Seshadri, wani mai ilimi kan kwari a sashin aikin gona mai kula da zuma a Davis, da ke jihar California, kuma sashin na karfafa wa masu filaye canza sassan filayen da gonaki suke zuwa gandun daji ta hanyar kirkiro da shirin kula da dabbobi.
‘Dole ne a ci gaba da aikin gona,’’ a cewar Seshadri,’’ amma dole ne a kiyaye wuraren.
Kantin magani na Zuma

Asalin hoton, Reuters
Ingantaccen abincin kudan zuma ba zai magance dukkan matsaloli da zuma ke fuskanta ba.
Amma ta hanyar tabbatar da kudan zuma na samun maganinsa zai taimaka matuka, a cewar Erler, wani mai kiwon zuma.
Ya kuma bada shawarar cewa ya kamata a rika adana zuma da ake samu saboda maganin kudan zuman ya yawaita a tsawon shekara.

Berenbaum, wacce ta soma bincike tsawon shekaru da suka gabata, ta ce ba ta tunanin cewa ana gudanar da sahihin bincike kan zuma yadda ya kamata, inda ta ce ilimin bincike kan kudan zuma hanya ce mai kyau.
‘Ina cike da murna ta ganin yanzu ana bai wa zuma bincike da ya kamata.’’ A










