Babu mahalukin da zai hana mu gudanar da babban taron jam'iyyar PDP — Bala

Gwamnan Bauchi Bala Muhammed
Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya, ya ce babu gudu-ba-ja-baya, sai sun gudanar da babban taron jam'iyyar na kasa a watan Nuwambar shekarar 2025.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed, ya bayyana haka ne bayan kammala taron da suka yi a ranar Asabar, 23 ga watan Augustan 2025, a jihar Zamfara Inda ya ce sun amince da ci gaba da shirye-shirye, don gudanar da taron a ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwambar 2025 a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Gwamnan , ya shaida wa BBC cewa tuni suka sanar da hukumar zabe ta INEC, cewa taron yana nan babu wani sauyi.

Ya ce," Ko a taronmu na koli mun tattauna akan yadda taron namu na kasa zai kasance saboda muna ganin cewa akwai wasu bata gari da ke son kawo mana cikas a cikin jam'iyya ganin cewa jam'iyyarmu ta PDP ta dauko hanyar gyara inda ta zamo abin sha'awa sannan kuma ta zamo jam'iyyar da kowa ke son tsayawa Takara a yanzu."

Bala Muhammed, ya ce," A halin da jam'iyyarmu ke ciki a yanzu babu wanda ya isa y ace ba za a yi babban taro ba, ko ni da nake shugaban gwamnonin PDP, ban isa n ace ba za a yi taro don ba a gaya mini ba, ballantana wani kuma."

"Babu wanda ya fi jam'iyya, domin ita ce ta ce za a yi wannan taro don haka ban ga wanda zai hana ba tun da duk wani tsari da za a bi a ga cewa an yi wannan taro an bi, domin an fadawa Hukumar zabe ta INEC, ta sani kuma zamu je babban taron ne tare da yardarm INEC din."In ji Bala Muhammed.

Gwamnan na Bauchi ya ce," A don haka idan mutum Daya dama yana neman ya kawo akasi, to ba zamu yar da ba domin babu wani mutum nan gaba da zai daga mana kara mu bamu karya ba, haka kuma babu wani da za ice mana kule bamu ce masa cas ba kowayeshi a jam'iyya."

Ya ci gaba da cewa," A yanzu ladaftar da mutane ya zame mana tilas domin dama kawai ci muke a baya ba wai tsoron kowa muke ji ba, kuma jam'iyyarmu na da karfi da tsari don haka ba zamu kyale wani ya zo yana nuna mana karfi ba kome goyon bayan da yake samu daga gwamnatin tarayya don muna bin doka."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bala Muhammed ya ce," Yanzu mun kai wani matsayi da zamu yi taro da babu wani mahaluki da zai hana mu in sha Allahu."

A yayin taron gwamnonin PDP da aka yi a Zamfara, gwamnonin sun yi kira ga mambobin jam'iyyar da su jajirce domin tabbatar da yiwuwar babban taron, domin a cewarsu PDP ce kaɗai jam'iyyar da za ta iya mayar da Najeriya turba mai kyau.

Gwamnan na Bauchi dai na mayar da wannan martani ne a game da babban taron na su da za ayi bayan da tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan birnin tarayyar Najeriya Abuja, Nyesome Wike, ya lashi takobin kin amincewa da gudanar da taron.

Wannan adawa da Wike ke yi da taron na da nasaba da rashin jituwa da ke tsakaninsa da gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, wato gwamnan jihar da za a gudanar da taron.

Nyesome Wike, dai jigo ne a jam'iyyar ta PDP, kuma ya ce shi sam ba shi da labarin wannan taro, kuma ba zai amince da shi ba ko da an gudanar da shi, domin akwai matsaloli da yawa da jam'iyyar ta kasa magancewa.

Wike ya ce muddin 'yan tsirarun mutane suka gudanar da taron, to sun yi wa kansu ne kawai, ba zai wakilci taron kwamitin zartaswa na kasa ba, inda ya ce shi da magoya bayansa za su yi tsayin daka domin yaki da rashin gaskiyar da ke cikin PDP.

Akwai dai 'yan Najeriya da dama da ke yi wa Wike kallon kadangaren bakin tulu a jam'iyyar ta PDP.