Sauya sheƙa da mambobinmu ke yi zuwa APC ko a jikinmu - PDP

pdp

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Ana ta bayyana fargaba tare da gargadi, cewa babbar jam'iyyar adawar Najeriya, wato PDP na iya rushewa kafin zaɓen shekara ta 2027. Idan har ba a ɗau aniyar warware matsalolin da ke ta kokarin kassarata ba gadan-gadan.

Hakan dai ya biyo bayan yadda rikicin shugabanci ya tanrake jam'iyyar shekara da shekaru, da kuma irin yadda 'ya'yanta da dama ake ta ficewa daga jam'iyyar, suna komawa jam'iyyar APC mai mulkin kasar.

Fitar farin dango da ake ta yi daga babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, ana komawa jam'iyyar APC mai mulkin kasar, da kuma rikita-rikita da dai sauran rigingimu da suka dabaibaiye jam'iyyar ta PDP.

Tun kimanin shekaru goma da suka gabata, duk sun sa ana ta hasashen za su iya yin ajalin jam'iyyar, kafin ma a kai ga zaben shekara ta 2027.

Sai dai jiga-jigan jam'iyar irin su Sanata Umaru Tsauri, tsohon sakataren jam'iyyar ta PDP na kasa, a yanzu kuma dan kwamitin amintattu da kwamitin zartarwa da sauran kwamitoci na jam'iyyar, suna kallon wannan fargaba da ake ta bayyanawa a matsayin wani merere ne kawai.

Ya ce wannan ba shi ne karo na farko da ake shiga wannan yanayi ba na turka-turka, an sha kuma a fita lafiya.

"Kuma masu fita fa mutane ne da ake jefawa kuri'a ba wai wandada za su jefa kuri'a ba.

"Tabbas yanayi akwai tada hankali amma fa ba kamar yaddda ake tunani ba.

"Kwadayi da barazana da neman mukami ke sa mutane na barin PDP, don haka lokaci zai warware komai

"Da zarran an zo lokacin zabe komai sai sauya kuma babu wani fargaba da muke yi, saboda akwai sauran kallo a gaba."

Me masana ke cewa?

Amma kuma duk da wadannan bayanai irin na karfafa gwiwa, masana na ganin ko da jam'iyyar PDP za ta tsallake siradin wannan hasashe da ake yi mata, sai fa shugabaninta sun yi namijin kokari ta hanyoyin da suka dace.

Farfesa Kamilu Sani Fage, na tsangayar nazarin kimiyyar siyasa ta jami'ar Bayero ta Kano ya ce idan ba daukan mataki aka yi ba na tsarin dimokuradiyya, kishin kasa ya zama jigo ba son rai ba, to ana iya ganin sauyi.

"Amma idan aka cigaba da tafiya a haka, gaskiya babu inda PDP za ta je, komai zai sukurkuce mata."

Tun bayan kubucewar mulki daga hannun jam'iyar ta PDP a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, jam'iyyar ta auka cikin rikincin shugabanci, wanda ya hana ta sakat har ya zuwa yanzu.

Al'amarin da ake ganin yana yi mata illa ta hanyoyi daban-daban, har abin na ta kokarin durkusar da ita.