Wace dabara ta rage wa Iran idan tattaunawa da Amurka ta gaza aiki?

Asalin hoton, OMAN'S FOREIGN MINISTRY ON X
- Marubuci, BBC Monitoring
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
- Lokacin karatu: Minti 6
Iran da Amurka sun fara tattaunawa a Muscat, babban birnin Oman ranar 6 ga watan Fabrairu. Tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da barazanar yaƙi tsakanin Amurka da Iran ke ƙaruwa.
Zaman fargaba ya ƙaru cikin sauri yayin da aka tura dakarun Amurka zuwa Gabas Ta Tsakiya sannan yaƙin cacar baka ta ƙaure tsakanin ɓangarorin. Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana son cimma yarjejeniya da Iran sannan ya yi gargaɗin cewa "abubuwa mara kyau" za su iya faruwa idan hakan bai yiwu ba.
Duk da cewa ba a bayyana yadda tsarin tattaunawar za ta kasance a hukumace ba, sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana ƙarara cewa ba wai Washington na son tattaunawar ta tsaya kan shirin nukiliyar Iran ba, amma har da batun makaman linzamin ƙasar da taimakawa ƙungiyoyin mayaƙa da kuma yadda gwamnatin ƙasar ke musgunawa jama'a.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi ya sha yin watsi kan tattaunawa ga batun ƙarfin makaman linzamin ƙasar, inda ya nanata cewa a shirye Iran take ta koma tattaunawa kan fagen nukiliya, muddin ba za a musgunawa ɗaya ɓangare ba.
Jamhuriyar Musuluncin ta shiga wannan sabuwar tattaunawar diflomasiyya a lokacin da take fuskantar ƙarin matsalin lamba a cikin gida da kuma waje.
A watannin baya bayan-nan, Iran ta fuskanci gagarumar zanga-zanga wadda ta fara kan batun ƙaryewar darajar kuɗin ƙasar da kuma ƙaruwar hauhawar farashi, inda daga bisani ta riƙiɗe zuwa ta kin jinin gwamnati a faɗin ƙasar - ta kuma kawo karshe ne bayan murkushe masu zanga-zanga abin da ba a taɓa gani a tarihin ƙasar.
Tattaunawar karkashin jagorancin ministan wajen Iran Abbas Araqchi da kuma jakadan Amurka na musamman Steve Whittaker, ba za a iya cewa za ta hana afkuwar rikici tsakanin ƙasashen.
A baya, Tehran da Washington sun gudanar da tattaunawa har sau biyar wanda Qatar ta jagoranta a Oman a watan Afrilu da Mayun 2025, sai dai an soke tattaunawa ta shida bayan ɓarkewar yaƙi na kwanaki 12 tsakanin Isra'ila da Iran.
Tattaunawa a yanki mai cike da fargaba
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Zuwa yanzu, shugabannin Jamhuriyar Musulunci sun mayar da hankali kan tattaunawar diflomasiyya, inda suka ce harin Amurka zai janyo yaƙi a yankin, sun kuma buƙaci sauran jagororin yankin da su shawarci Donald Trump kada ya kuskura ya kai hari.
Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Jordan sun ki amfani da yankinsu da kuma sararin samaniya ga duk wani hari da za a iya kai wa Iran, abin taƙaita zaɓin da Amurka ke da shi.
Iran ta yi gargaɗin cewa za ta afka wa sansanon sojin Amurka da Isra'ila da kuma kayayyakinsu idan har aka kai mata hari, wata barazana da ke nufin cewa za ta iya kai hari Iraqi, Bahrain, Qatar, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Kuwait, Jordan da kuma Syria.
A wasu rikice-rikice na baya da Amurka, Iran ta mayar da martani mai muni. Bayan harin Amurka kan makaman nukiliyar Iran a lokacin da yaƙi ya ɓarke tsakanin Isra'ila da Iran a 2025, Tehran ta sanar wa Washigton tun da wuri niyyarta na kai hari sansanin sojin Udeid da ke Qatar.
A watan Janairun 2020, Iran ɗin ta faɗa wa Amurka kafin kai hari sansanin sojinta na Ain al-Assad da ke Iraqi, a matsayin martani a kashe kwamandan dakarun juyin juya-hali Qassem Soleimani.
Sai dai, yanzu Iran na ganin duk wani hari da Amurka za ta kai a matsayin barazana ga ɗorewarta. Donald Trump ya faɗa lokacin zanga-zanga ta baya bayan-nan cewa lokaci ya yi da za a buƙaci "sabon jagoranci a Iran".
An ruwaito cewa yana duba yiwuwar amfani da matakin soji kan Iran, abin da zai ƙara ingiza zanga-zanga da kuma buɗe hanyar hamɓarar da gwamnatin Jamhuriyar Musulunci.
Yayin da rikici ke ƙara bazuwa, Iran ta yi gargaɗin cewa duk wani hari da Amurka za ta kai, zai zama a matsayin taƙalar yaƙi.
Me Iran za ta yi idan tattaunawa ta gaza aiki?
Harba makaman linzami
Marco Rubio ya bayyana ranar 28 ga watan Janairu cewa an girke dakarun Amurka 30,000 zuwa 40,000 a sansanoni takwas zuwa tara a Gabas Ta Tsakiya, "waɗanda za su iya tare makaman linzami da na jirage marasa matuki na Iran. "An kiyasta cewa Iran na da makaman linzami 2,000, ciki har da masu cin karami da matsakaicin zango waɗanda za su iya faɗa wa wasu wurare.
Lokacin yaƙi na kwanaki 12, Iran ta harba makaman linzami da dama zuwa Isra'ila, har ta kai wasu sun shata na'urar kakkaɓe makamai na Isra'ila. Amurka na da na'urorin kakkaɓe makamai a yankin, sai dai idan yaƙi ya ɓarke, za su iya cin dogon zango fiye da na Isra'ila.
Iran ta ce ta sake ginawa da kuma ƙarfafa makaman linzaminta bayan yaƙin da ta yi da Isra'ila. An ruwaito cewa Rasha da China sun taimaka wajen ƙara wa sojin Iran ƙarfi tun watan Yunin bara.
Amfani da dabarun ciki gida
Ƙarfin sojin Iran bai kai na Amurka ba, musamman ma a ɓangaren fasaha. Kan wannan dalili ne, Tehran za ta yi amfani da dabaru na cikin gida. Waɗanda suka haɗa da kai hare-hare ta hanyar amfani da jiragen ruwa masu saurin gaske da yawa da kuma jirage marasa matuki, domin wargaza shirin abokan gaba.
Iran za ta iya amfani da irin waɗannan dabaru da jiragen ruwanta da ke yankin Gulf da da kuma jirage marasa matuki na Shahed -136, wadda aka ruwaito cewa Rasha ta yi amfani da shi sosai a yaƙin Ukraine.
Yayin da zaman fargaba ke ƙaruwa, wasu kafofin yaɗa labaran Iran ciki har da waɗanda ke kusa da daakrun juyin juya-hali, sun nanata cewa za a yi amfani da dabarun. Sojojin Iran ma sun sanar ranar 29 ga watan Janairu cewa sun karɓi jirage marasa matuki 1,000 "masu muhimmanci."
Girke ƙungiyoyin mayaƙa a yankin
A tsawon gomman shekaru, Iran ta samar da makamai tare da taimakawa ƙungiyoyin mayaƙa waɗanda aka fi sani da "Jajirtattu." Wannan ya kunshi ƙungiyoyi a Iraqi, Hezbollah a Lebanon, ƴan Houthi a Yemen da sauransu.
A tsawon shekaru biyu da suka wuce, Isra'ila ta yi wa waɗannan ƙungiyoyi mummunan illa, abin da ya rage wa Iran nuna iko fiye da iyaƙarta. Sai dai, duk da haka, tsara kai hare-hare kan shingayen Amurka tare da taimakon irin ƙungiyoyin zai janyo babbar barazana.
Ba a fafata da waɗannan ƙungiyoyi ba lokacin da yaƙi ya ɓarke tsakanin Isra'ila da Iran a 2025, amma idan Amurka ta far wa Iran, lissafin Tehran da waɗannan ƙungiyoyi zai iya sauyawa.
Zuwa yanzu, wasu ƙungiyoyin mayaƙa Iran da ke mara wa baya a Iraqi, sun sanar da cewa za su kare ƙasar.
Ƙungiyar Kata'ib Hezbollah ta yi kira ga waɗannan ƙungiyoyi da su shirya kare Iran, sauran ƙungiyoyi irinsu Badr ma sun ayyana goyon bayansu ga duk wani yunkurin kai wa Iran hari.
Yayin da yake ayyana goyon bayan ƙungiyar Hezbollah ga Iran, Naim Qassem, sakatare-janar na ƙungiyar a Lebanon, ya ce idan Amurka ta far wa Iran, ƙungiyar za ta tsara lokacin da ya fi dacewa wajen mayar da mummunan martani.
Sai dai waɗannan ƙungiyoyi da ke Iraqi da Lebanon na cikin matsin lamba na ganin sun ajiye makamai, kuma wannan matsi zai ƙaru idan suka shiga rikicin.
Ƴan Houthi za su iya komawa kai hare-hare kan jiragen ruwan Amurka a tekun Maliya idan Amurka ta far wa Iran.
Ranar 26 ga watan Janairu, ƙungiyar ta fitar da wani bidiyon da ke nuna wani jirgi yana ci da wuta tare da rubutu mai cewa "Muna zuwa nan ba da jimawa ba." Sai dai, za su iya yanke shawarar kin taimakawa Iran domin ƙauce wa saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma da Amurka a watan Mayun, 2025.
Rufe Mashigar Hormuz
An sha tattauna wannan barazana na tsawon shekaru a Iran, a duk lokacin da tashin hankali ya taso tsakaninsu da ƙasashen yamma.
Wannan mashiga da ke Mashigin Gulf na da muhimmanci sosai saboda kashi biyar na mai da ke fita duniya na bi ta wajen. Rufe Mashigar Hormuz zai faru ne ta hanyar dasa naƙiyoyi masu tarwatsa jiragen ruwa, makaman linzami da kuma amfani da jirage masu saurin gaske.
Wannan mataki zai zama zaɓin Iran na karshge, saboda hakan zai iya kawo tarnaki ga ɓangaren kasuwancin ƙasar da babbar ƙawarta ta kasuwanci, wato China, kuma zai shafi ƙasashen yankin Gulf waɗanda suka yi koƙarin dakatar da ɗaukar matakin soji kan Tehran a rikicin baya bayan-nan.
Wannan shi ya sa manyan jami'an Jamhuriyar Musulunci ba su gabatar da matakin ba a hukumance, kuma a rikici na bayan nan, ƴan majalisar dokokin ƙasar da kafafen yaɗa labarai sun yi barazanar rufe Mashigar ta Hormuz.
Duk da cewa Iran da Amurka sun ce sun fi son tattaunawar diflomasiyya don samun mafita, babban giɓi da ke tsakanin ɓangarorin biyu a tattaunawar da ake ci gaba da yi, ya sanya wahala wajen cimma yarjejeniya.
Idan gwamnatin Trump ta koma ga zaɓin amfani da ƙarfin tuwo, Iran za ta iya sauya shawara nan take, tare da sadaukarwa ga Washington domin samun tsirar Jamhuriyar Musulunci.
A ɗaya gefen, Iran za ta iya janyo mummunan lahani a rikicin don ganin Amurka ta koma teburin tattaunawa.











