Garkuwan Kurma ya buge Ƴar mage a damben gasar Maraba

Ranara Lahadi aka kammala damben gasa tsakanin jihar Nasarawara da ta karɓi bakunci ta Katsina da aka dambata a Marabar Nƴanya.
An buga wasa biyar a safiyar Lahadi, sannan aka karkare da uku a yammacin ranar a Ƴan tifa a karamar hukumar Karo a jihar Nasarawa, Najeriya.
An fara da wasan da Saƙaƙo daga jihar Katsina, wato Garkuwan Sanin Guramada, wanda ya yi nasara a kan Aljanin Nokia daga jihar Nasarawa, wadda ya dunga fita daga da'irar fili har sau 12.
Daga nan aka yi wasa mai zafi tsakanin Garkuwan Kurma daga Nasarawa da Ƴar Mage daga Katsina, kuma turmi uku suka dambata.
Wasan ya kayatar matuka, bayan da kowanne ɗan wasan ya nuna jarumta, sai dai a turmi na uku ne Garkuwan Kurma ya buge Ƴar Mage na Katsina.
Sai kuma canjaras da aka yi tsakanin Sabon Gundumi daga Nasarawa da Garkuwan Duna daga jihar Katsina a turmi ukun da suka fafata.
Damben gaba shi ne wanda Ɗan Aliyu na Arewa mai wakiltar Nasarawa da ya doke Bahagon Gambo daga Katsina a turmin farko.
An karkare da dambe na biyar a safiyar Lahadi tsakanin Bahagon Ramadan daga Katsina da Autan Na Aisha daga jihar Nasarawa, waɗanda suka tashi canjaras.











