Galatasaray na zawarcin Ederson, ƙungiyoyi da dama na rububin Nunez

Ederson

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Galatasaray ta miƙa tayin fam miliyan 2.6m kan golan Manchester City da Brazil Ederson, mai shekara 31. (L'Equipe)

Barcelona, da AC Milan, da Al Hilal da Al Nassr suna cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan gaban Liverpool da Uruguay Darwin Nunez, mai shekara 26. (Caughtoffside)

Manchester City na tunanin zawarcin golan Burnley da Ingila James Trafford, mai shekara 22, amma sai idan ɗaya daga cikin manyan masu tsaron gidansu biyu ya tafi. (Fabrizio Romano)

Ɗan wasan tsakiya na Netherlands da RB Leipzig Xavi Simons, mai shekara 22, ya fi son komawa gasar Premier, inda Chelsea da Arsenal su ka sanya ido kan halin da yake ciki a ƙungiyarsa. (Bild)

Ɗan wasan Colombia da Liverpool Luis Diaz, mai shekara 28, ya shaida wa kulob dinsa cewa yana son komawa Bayern Munich. Ƙungiyar ta Anfield dai ta yi watsi da tayin farko da aka yi ma ta a farkon makon nan. (Florian Plettenburg)

Juventus na tunanin yin musayar ƴan wasa da Manchester United inda za ta miƙa ɗan wasan tsakiyar Brazil Douglas Luiz, mai shekara 27 ta kuma karɓo dan wasan gaban Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 22. (Tuttosport)

Jose Mourinho yana sha'awar sayen ɗan wasan Manchester United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, a Fenerbahce. (T24)

Sunderland ta amince ta biya fam miliyan 17.5 kan ɗan wasan Faransa da Sassuolo Armand Lauriente, mai shekara 26. (Sky Sports).

Ɗan wasan tsakiyar Ingila Ethan Nwaneri, mai shekara 18, ya ƙulla sabuwar yarjejeniya ta shekara biyar da Arsenal. (Telegraph)

Tottenham ta fara neman ɗan wasan Bournemouth da Ukraine Ilya Zabarnyi mai shekara 22. (TalkSport)

Ipswich na jiran ingantacciyar tayi daga Brentford kan ɗan wasan gaban Ingila Omari Hutchinson mai shekara 21. (Sky Sports)

Norwich na daf da sayar da ɗan wasan gaban Amurka Josh Sargent, mai shekara 25, ga Wolfsburg kan fam miliyan 21. (Sky Sports)