Hotunan Afirka: Bikin al'adun Yarabawa da gangamin adawa da kamfanin Total

    • Marubuci, Cecilia Macaulay
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Zaɓaɓɓun hotunan wannan mako daga sassan Afirka da 'yan nahiyar daga sauran kasashen duniya:

A jihar Oyo kuma da ke Najeriya, a dai ranar ta Asabar, an yi karin bukukuwan al'adun Yarabawa yayin da wata mai bautawa Sango ke bajekolin kayan jikinta yayin da ta shiga bikin al'adu na Sango da ake yi duk shekara.

Asalin hoton, Emmanuel Adegboye/Shutterstock/EPA

Bayanan hoto, A jihar Oyo kuma da ke Najeriya, a ranar Asabar, an yi ƙarin bukukuwan al'adun Yarabawa yayin da wata mai bauta wa Sango ke bajekolin kayan jikinta a bikin al'adu na Sango da ake yi duk shekara.
Wata mai nuna kayan kawa a Kenya ranar Asabar cikin wajen wasan yan dambe gabanin wata gasa don bikin ranar matasa ta duniya a Mathare da ke Nairobi, babban birnin kasar.

Asalin hoton, Daniel Irungu/Shutterstock/EPA

Bayanan hoto, Wata mai nuna kayan kawa a Kenya ranar Asabar cikin da'irar wasan dambe gabanin wata gasa don bikin ranar matasa ta duniya a Mathare da ke Nairobi, babban birnin kasar.
An yi wani gangami da masu fafutuka kan sauyin yanayi suka shirya a Afirka ta Kudu ranar Talata don neman a dakatar da ayyukan kamfanin Total a Afirka.

Asalin hoton, Brenton Geach/Gallo Images/Getty Images

Bayanan hoto, An yi wani gangami da masu fafutuka kan sauyin yanayi suka shirya a Afirka ta Kudu ranar Talata don neman a dakatar da ayyukan kamfanin Total a Afirka. Babban kamfanin makamashin bai ce komai ba kan gangamin sai dai ya bayyana cewa ya dukufa wajen samar da makamasi mai dorewa.
Mia le Roux, wadda a bara ta zama mai larurar rashin ji ta farko da aka nada a matsayin sarauniyar kyau a Afirka ta Kudu.

Asalin hoton, Frennie Shivambu/Gallo Images/Getty Images

Bayanan hoto, Mia le Roux, wadda a bara ta zama mai larurar rashin ji ta farko da aka nada a matsayin sarauniyar kyau a Afirka ta Kudu, tana murmushi yayin da ake daukar ta hoto ranar Juma'a a Pretoria, babban birnin kasar yayin da ta halarci wani taron tattaunawa na kasa da ke neman zakulo manyan matsalolin da suka addabi kasar.
Akwai yalwar dankali a wannan kasuwar kayan masarufi a ranar Lahadi yayin da wani dan kasuwa ke juye kwandon dankali a Algiers, babban bitrnin Algeria.

Asalin hoton, Billel Bensalem/APP/NurPhoto/Getty Images

Bayanan hoto, Akwai yalwar dankali a wannan kasuwar kayan masarufi a ranar Lahadi yayin da wani dan kasuwa ke juye kwandon dankali a Algiers, babban bitrnin Algeria.
Washegarin ranar a Wasiko da ke Uganda wani na busa abin busa na trombone gabanin wasan kwallo na gasar cin kofin Afirka ta ƴan wasan da ke taka leda a gida wato CHAN inda Uganda ta kece raini da Afirka ta Kudu a matakin rukuni.

Asalin hoton, Badru Katumba/AFP/Getty Images

Bayanan hoto, Washegarin ranar a Wasiko da ke Uganda wani na busa abin busa na trombone gabanin wasan kwallo na gasar cin kofin Afirka ta ƴan wasan da ke taka leda a gida wato CHAN inda Uganda ta kece raini da Afirka ta Kudu a matakin rukuni.
Yan kallo cike da murmushi a ranar Lahadi a birnin Nairobi yayin da suka shirya kallon fafatawar yan wasan kasarsu ta Kenya da Zambia a gasar Chan.

Asalin hoton, Donwilson Odhiambo/Getty Images

Bayanan hoto, Yan kallo cike da murmushi a ranar Lahadi a birnin Nairobi yayin da suka shirya kallon fafatawar yan wasan kasarsu ta Kenya da Zambia a gasar Chan.
A ranar Laraba, wadannan kananan yaran a Legas da ke Najeriya sun shiga bukukuwan ranar Isese da ake nuna al'adun Yarabawa.

Asalin hoton, Adekunle Ajayi/NurPhoto/Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Laraba, wadannan kananan yaran a Legas da ke Najeriya sun shiga bukukuwan ranar Isese da ake nuna al'adun Yarabawa.
A ranar kuma a Detroit, fitaccen mawakin Najeriya Asake ya halarci wani wajen casu a birnin na Amurka.

Asalin hoton, Robert Okine/Getty Images

Bayanan hoto, A ranar kuma a Detroit, fitaccen mawakin Najeriya Asake ya halarci wani wajen casu a birnin na Amurka.
Mawakiya Ahlam daga Dubai kan dandali a ranar Alhamis inda take rera waka a wani biki na kasa da kasa da aka yi a Tunisia.

Asalin hoton, Fethi Belaid/AFP/Getty Images

Bayanan hoto, Mawakiya Ahlam daga Dubai kan dandali a ranar Alhamis inda take rera waka a wani biki na kasa da kasa da aka yi a Tunisia.
Masu iyo a teku da ke Alexandria a Masar suna kallon yadda wani injin daga kaya masu nauyi ya daga wasu manyan duwatsu na tarihi a ranar Alhamis a wani bangare na zakulo wasu kayan tarihi da suka nutse.

Asalin hoton, Khaled Desouki/AFP/Getty Images

Bayanan hoto, Masu iyo a teku da ke Alexandria a Masar suna kallon yadda wani injin daga kaya masu nauyi ya daga wasu manyan duwatsu na tarihi a ranar Alhamis a wani bangare na zakulo wasu kayan tarihi da suka nutse.
A birnin mai tashar jirgin ruwa, wata karamar yarinya tana murmushi yayin da take shan iskar da ke shigowa ta tagar wata bas daidai lokacin da yanayin zafi ke karuwa.

Asalin hoton, Amr Abdallah Dalsh/Reuters

Bayanan hoto, A birnin mai tashar jirgin ruwa, wata karamar yarinya tana murmushi yayin da take shan iskar da ke shigowa ta tagar wata bas daidai lokacin da yanayin zafi ke karuwa.