Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Taurarin Kannywood bakwai da suka yi tashe a 2024
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Lokacin karatu: Minti 3
Shekarar 2024 ta zo da abubuwa da dama, har da a fannin nishaɗi da ya zama ɓangare na rayuwar jama'a wajen kore damuwarsu da kuma shaƙatawa.
Akwai taurari da dama da suka yi fice sosai a 2024 la'akari da yawan fitowarsu a finafinai da kuma karɓuwar da suka samu a wajen ma'abota Kannywood da finafinan Hausa.
BBC ta zaƙulo wasu daga cikin taurarin na Kannywood da suka yi tashe a 2024;
Yakubu Muhammad
Yakubu Muhammad yana cikin daɗaɗɗun masu fim a Kannywood sai dai har yanzu tauraruwarsa tana haskawa kamar yadda aka gani a 2024.
Yana kuma ɗaya daga cikin ƴan fim maza da ba su tsaya a iya Kannywood kaɗai ba, sun tsallaka Nollywood.
Ya taka rawa a finafinai masu girma da suka ja hankalin masu kallo irin su Allura Cikin Ruwa wanda shi ne darakta da Gidan Sarauta da kuma Labarina.
Amina Hassan
Amina Hassan, wadda tsohuwar matar Adam Zango ce, ta fito a finafinai da dama da suka samu karɓuwa a 2024.
Daga cikin finafinan da ta yi akwai Labarina da Garwashi da fim ɗin Unraveled Hearts da Ɗakin Amarya.
Ita ce ta fito a matsayin Jamila kuma ƙawar Maryam wadda Mainasara ya fara so sai dai ta ƙi amincewa da shi.
Fateema Hussain
Duk da cewa ta ɗan jima a harkar Kannywood amma a bana, ta yi finafinai da dama da suka haɗa da Labarina da Jamilun Jidda da Na Ladidi da kuma Manyan Mata.
A fim ɗin Labarina, ta fito a matsayin Maryam inda ta zama matar Mainasara.
Baya ga fim, akwai sukar da ta sha a shafukan sada zumunta bayan wasu kalamai da ta yi da mabiyanta ba su ji daɗi ba, amma daga bisani ta fito ta nemi afuwar mutanen da kalaman nata suka ɓata wa rai.
Saddiq Sani Saddiq
Sadiq Sani Sadiq shi ne jigon fim ɗin Labarina inda ya fito a matsayin Alhaji Mainasara.
A fim ɗin Labarina, a yanzu yana da mata biyu - Maryam da kuma Dokta Asiya.
Ya kuma fito a shirin Manyan Mata da sauransu.
Zahrah Muhammad
An fi saninta da Diamond Zahra a masana'antar Kannywood kuma ta yi fice sosai a 2024.
Zahra Muhammad ta taka rawar gani a finafinan da dama, kamar Labarina.
A cikin fim ɗin ta fito a matsayin Dokta Asiya har kuma ta zama matar Mainasara, wato kishiya ga Maryam a fim ɗin na Labarina.
Maimuna Gombe Abubakar
Maimuna Abubakar wadda a Kannywood aka fi sani da Momee Gombe ta fito a fim ɗin Gidan Sarauta.
Ita ce tauraruwar fim ɗin Gidan Sarauta mai dogon zango wanda yake tashe a 2024.
Ta kuma fito a fim ɗin Manyan Mata da ya tara manyan jarumai masu yawan gaske.
Firdausee Yahaya
Bayan Labarina, Fidausi Yahaya ta fito a manyan finafinai, inda ta kasance wadda ta ja wasu daga ciki.
Daga ciki akwai Manyan Mata da Allura Cikin Ruwa da Garwashi da Jamilun Jiddan wanda za a fara haskawa a Janairun 2025.
Fa'iza Abdullahi
Jaruma Fa'iza Abdullahi ta yi fice a fim ɗin Daɗin Kowa na dogon zango.
An fi saninta da Bilki mai abinci a fim ɗin, wanda ya haskaka ta a harkar Kannywood duk da cewa ta fito a wasu finafinan.