Sakwara ya buge Bahagon Mai Takwasara a damben Maraba

Damben Gargajiya
Lokacin karatu: Minti 2

Ranar Lahadi da safe an buga wasa da yawa a gidan dambe da ke karamar hukumar Karo a jihar Nasarawar Najeriya.

Cikin wasannin har da na gasa guda biyar da aka yi, inda Sakwara daga Arewa ya doke Bahagon Mai Takwasara Guramada a turmin farko.

Dambe naira 100,000 ne da Idris Bambararewa shugaban ƙungiyar Dambe ta jihar Nasarawa ya saka daga fafatawa biyar.

Shi ne wasa na karshe da aka buga a ranar, inda makadin ƴan dambe, Labaran Ɗan Gwamba ya fara kuranta Bahagon Mai Takwasara daga baya ya kira Sakwara.

Ana shiga fili ne alkali, Shagon Amadi ya busa usur da cewar an fara damben, kuma a turmin farko Sakwara ya doke Bahagon Mai Takwasara.

Sauran sakamakon wasannin gasa da aka buga, an tashi canjaras tsakanin Kaddaran Autan Ɗan Bunza daga Arewa da Buhari Shagon Yalo Guramaɗa a turmi ukun da suka fafata.

Shima wasan Ƴar Mage daga Kudu da Autan na Aisha Guramaɗa ya kayatar, amma bai yi gwani ba, haka ma fafatawa tsakanin Ɗan Aliyu daga Arewa da Ɗan Kanawa daga Kudu.

Damben Yalon Tula daga Jamus da Bahagon Ali Kawoji Guramaɗa, shima turmi uku aka buga, amma babu kisa, kuma kowa da tsoro ya buga wasan, kuma bai yi armashi ba.

Sakamakon wasannin damben kasuwa da aka buga

Wasannin da aka yi kashe-kashe

  • Shagon Inda daga Arewa ya buge Autan Makada Guramaɗa
  • Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa ya doke Mabilu Shagon Na Balbali daga Kudu
  • Shagon Mustapha wato Tuturuna daga Arewa ya yi nasara a kan Shagon Ɗan Shariff daga Kudu
  • Dogon Shamsu daga Arewa ya buge Shagon Mai masauki Guramaɗa

Wasannin da aka yi canjaras

  • Sabon Gundumi Guramaɗa da Aljanin Nokiya daga Jamus
  • Shagon Sojan Ƙyallu Guramaɗa da Garkuwan Autan Ɗan Bunza daga Arewa
  • Garkuwan Kurma Guramaɗa da Shagon Fatalwa daga Kudu
  • Shagon Sanin Ɗan Kande daga Jamus da Mai kacau-kacau daga Kudu
  • Shamsun Ɗan Bunza daga Arewa da Dogon Sarka Guramada
  • Bahagon Autan Kudawa daga Kudu da Garkuwan Ramadan daga Arewa
  • Autan Korona daga Kudu da Shagon Lawwalin Gusau daga Jamus
  • Shagon Fatalwa daga Kudu da Garkuwan Autan Ɗan Bunza daga Arewa.