Ya kamata a sauya yadda ake yi wa ƙiba kallon cuta - Rahoto

    • Marubuci, Philippa Roxby
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health reporter
  • Lokacin karatu: Minti 4

Wani rahoto daga ƙwararru ya ce akwai haɗari game da yadda ake gano mutane na fama da matsananciyar ƙiba yayin da ake buƙatar sake nazari kan ma'anar kalmar.

Ya kamata likitoci su duba lafiyar mutanen da ke da kitse da yawa a jiki, a maimakon kawai gwada nauyin jikinsu, in ji rahoton.

Ya kamata a bambance masu matsananciyar ƙiba tsakanin waɗanda ke da wata cuta da ta tsananta sakamakon nauyinsu da waɗanda ba su da wata matsala ta lafiya.

An ƙiyasta fiye da mutum biliyan ɗaya na fama da matsananciyar ƙiba a faɗin duniya kuma ana yawan bayar da maganin rage ƙibar.

Rahoton, da aka wallafa a mujallar The Lancet Diabetes & Endocrinology, ya samu gudummawar fiye da ƙwararrun likitoci 50 daga sassan duniya.

'Sauya ma'ana'

"Matsananciar ƙiba wani nau'i ne," in ji Farfesa Francesco Rubino na kwalejin Kings da ke London wanda ya shugabanci tawagar likitocin.

"Wasu na da ita kuma suna rayuwa daidai ba tare da wata matsala ba.

"Wasu kuma ba sa iya tafiya sosai ko yin numfashi yadda ya kamata ko ma sun kasance kan kujerar guragu da matsalolin lafiya da dama."

Rahoton ya nemi a sake nazarin matsananciyar ƙiba domin bambance masu matsananciyar ƙiba da ke fama da cuta da waɗanda suke da lafiya, amma suna cikin haɗarin kamuwa da rashin lafiya a gaba.

A yanzu, a galibin ƙasashe, ana bayyana matsananciyar ƙiba idan nauyin jikin mutum ya zarce 30 - abin da ke ƙiyasta kitsen da ke jikin mutum bisa la'akari da tsayinsa da kuma nauyinsa.

Samun magungunan rage ƙiba kamar Wagevy da Mounjaro, galibi ana taƙaita wa masu matsananciyar ƙiba yin amfani da su.

A yawancin sassan Birtaniya, hukumar inshorar lafiya NHS na bayar da maganin ne kawai ga mutanen da suke da wata matsalar lafiya da ta danganci ƙiba.

Sai dai nauyin jiki ba komai yake ganowa ba game da lafiyar mutum, in ji rahotonm kuma ba ya bambance tsakanin tsoka da kitsen jiki.

Ƙwararrun sun ce ga wani sabon tsari da yake duba alamomin matsananciyar ƙiba da ta shafi gaɓoɓin jiki kamar ciwon zuciya da rashin numfashi da kyau da ciwon suga nau'i na biyu ko ciwon gaɓoɓi - da kuma tasirinsu ga rayuwar yau da gobe.

Wannan na nuna cewa matsananciyar ƙiba ta zama cutar da ta tsananta kuma take buƙatar magani.

Waɗanda suke da matsananciyar ƙiba amma ba su da matsalar lafiya sai dai a maimakon magunguna da tiyata, ya kamata a ba su shawarwarin rage ƙiba, da kuma bibiyar yanayinsu don rage yiyuwar fuskantar matsalolin lafiya. Shi ma yana buƙatar magani.

Maganin da bai zama dole ba

"Matsananciyar ƙiba na da haɗari ga lafiya - bambancin shi ne ita ma cuta ce ga wasu," in ji Farfesa Rubino.

Sake ma'anarta ya yi kyau, in ji shi, don fahimtar irin haɗarin da take da shi ga mjama'a, a maimakon yadda a yanzu ake kallonta.

Ƙwararriya kan matsananciyar ƙiba a tsakanin yara, Farfesa Louise Bau, daga jami'ar Sydney, wadda ta ba da gudummawa a rahoton, ta ce sabon fasalin zai bai wa manya da yara da suke fama da matsananciyar ƙiba damar samun kulawa sosai yayin da za a rage yawan mutanen da ake gano suna da matsananciyar ƙiba ana kuma ba su magungunan da ba su zama dole ba.

A lokacin da ake bayar da magungunan da ke rage nauyin jiki da kusan kashi 20 cikin 100, rahoton ya ce "sake bayanin matsananciyar ƙiba" yana da muhimmanci saboda zai inganta tsarin gano cututtuka.

Ƙarancin kuɗi

Kwalejin koyar da ilimin Physics ta ce rahoton ya samar da wani babban tubali "na maganin matsananciyar ƙiba kamar sauran cututtuka da suka tsananta".

Bambance tsakanin matsananciyar ƙiba mara barazana ga lafiya da kuma wadda take barazana ga lafiyar mutum sakamakon nauyin jikinsa zai zama wani muhimmin mataki da zai bayyana buƙatar ganowa da kuma fara magani da wuri yayin da zai samar da kulawar da ta dace ga waɗanda lafiyarsu ta taɓu sosai, in ji kwalejin.

Amma akwai fargabar da ake cewa matsin lamba kan kasafin lafiya na iya nufin ƙarancin kuɗi ga waɗanda suke matakin da bai kai a ce suna da matsananciyar ƙiba ba.

Farfesa Sir Jim Mann, mataimakin daraktan cibiyar nazari kan ciwon suga ta Edgar a Otago da ke New Zealand, ya ce akwai yiwuwar a ba da fifiko ga buƙatun waɗanda aka bayyana suna da matsananciyar ƙiba da kuma yiwuwar ƙarancin kuɗin za shafe su.