Ƙasashe 10 da kuɗaɗensu suka fi daraja a duniya

Lokacin karatu: Minti 4

Duk da cewa dalar Amurka ne kuɗin da aka fi hada-hada da shi, amma hakan bai sa ya zama mafi daraja ba a duniya.

Mujallar Forbes ta fitar da jerin kuɗin ƙasashe 10 mafiya daraja a duniya, inda aka yi amfani da wani ma'auni bisa ga bayanai da aka tattara a kasuwar hada-hadar canjin kuɗaɗen duniya.

Dinarin Kuwaiti

Ta hanyar amfani da wannan ma'auni, an gano cewa dinarin Kuwait ne kuɗi mafi daraja a duniya, inda ake sayar da dinari ɗaya kan dala 3.25.

A taƙaice, a misali za a iya cewa dalar Amurka ɗaya daidai take da kobo 30 na dinarin.

Kuwait dai na tsakanin ƙasashen Saudiyya da Iraƙi, inda take samun yawan kuɗaɗen shigar ta daga fitar da ɗanyen man fetur.

Dinarin Bahrain

Dinari ɗaya na Bahrain ya kai dala 2.65. Hakan ya sanya dala zama, misali a kobo 37 na kuɗin ƙasar.

Bahrain ƙasa ce da ke yankin Gulf, inda take iyaka da gaɓar tekun Gulf da kuma Saudiyya a ɗaya gefen.

Ƙasar dai na samun kuɗaɗenta daga ɓangarori da dama, inda abubuwan da take samu wanda ba shi alaƙa da mai ya kai kashi 85.9 a 2024.

An fara amfani da dinarin Bahrain ne a shekara ta 1965.

Riyal din Oman

An fara amfani da riyal ɗin Oman a 1970. Riyal ɗaya ya kai aƙalla dalar Amurka 2.60.

A taƙaice, a misali za a iya cewa dalar Amurka ɗaya daidai take da kobo 38 na kuɗin Oman.

Ƙasar na makwabtaka da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Yemen.

Oman na cikin sahun gaba a ƙasashen duniya da ke fitar da man fetur da iskar gas, kamar sauran makwabtanta masu arziki.

Dinarin Jordan

Dinarin na Jordan wanda aka fara amfani da shi a shekarun 1950, ya kai darajar dala 1.41, inda yake matsayi na huɗu a jerin kuɗaɗe mafiya daraja a duniya.

Jordan ƙasa ce da ke yankin Gabas Ta Tsakiya. Ba ta dogara sosai da man fetur ba kamar sauran makwabtanta.

Sai dai, ƙasar ta fuskanci matsalar tattalin arziki da kuma ƙaruwar basuka.

Fam na Ingila

Fam ɗin Ingila ya wanzu tun ƙarni na 15, inda aka sauya tsarinsa a 1971.

Zuwa yau, fam ɗaya ya kai dala 1.34.

Fam ɗin Gibraltar

An fara amfani da fam ɗin Gibraltar ne a shekarun 1920, kuma a yau ana alaƙanta darajarsa da ta fam ɗin Ingila, abin da ke nufin zai ci gaba da tafiya daidai da fam ɗin Birtaniyar.

Gilbraltar wani yanki ne da ke ƙarƙashin Birtaniya a kudancin Sifaniya.

Franc na Switzerland

Franc shi ne nau'in kuɗi da Switzerland da kuma Liechenstein ke amfani da shi a hukumance.

Kuma ana ɗaukar kuɗin a matsayin wanda ba shi da barazanar durƙushewa saboda yadda tsarin siyasar Switzerland ke tafiya cikin tsanaki.

Franc ɗin ya fara wanzuwa ne a shekarar 1850.

Franc ɗaya na Switzerland daidai yake da dala 1.24.

Dalar tsibirin Cayman

Tsibirin Cayman wani yankin Birtaniya ne a yankin Carribbean, kuma an fi sanin yankin kan irin damar da yake bai wa dukkan mutane.

An fara amfani da dalar Cayman ne a shekarun 1970, kuma ana alakanta ta da dalar Amurka.

Ana canja dalar Cayman ɗaya zuwa dalar Amurka 1.24.

Kuɗin Yuro

A shekarar 2002 aka fara amfani da Yuro a hukumance.

Kuɗi ne da ƙungiyar ƙasashen Turai ke amfani da shi, inda ƙasashe aƙalla 20 cikin 27 ke mu'amala da kuɗin.

Ana canja yuro ɗaya kan dalar Amurka 1.16.

Dalar Amurka

Dalar Amurka ta samu shiga cikin jerin kuɗaɗen ƙasashe 10 mafiya daraja a faɗin duniya, .

An fara amfani da kuɗin ne a shekarun 1700, kuma shi ne aka amince da shi a ƙasar, har da wasu yankuna da kuma ƙasashe masu cin gashin kai - ciki har da Ecuador.

Tattalin arzikin kasar Amurka shi ne mafi girma a duniya idan aka yi la'akari da tattalin arzikin cikin gida (GDP) - kuma dalar ita ce wadda aka fi hada-hada da ita a faɗin duniya.

An kuma fi amfani da kuɗin dala wajen cinikayya a kasuwanni, musamman wajen sayen mai, da zinare da kuma ma'adinai.