Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda dokar haraji ta raba kan yan APC a Najeriya
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Tun bayan zaɓen fitar da gwani na shugabancin Najeriya babu wani abu da ya rarraba kan 'yan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya kamar batun gyaran dokokin haraji da gwamnatin Bola Tinubu ke son yi a yanzu.
Yanzu dai ƙudirin dokokin huɗu sun tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa, amma ba su wuce ba sai da aka tafka muhawara tsakanin masu goyon baya da kuma masu sukar ƙudirin.
Gwamnonin arewacin Najeriya baki ɗayansu ne suka nuna adawa da ƙudirorin, suna masu cewa sabon salon rarraba harajin Value Added Tax (VAT) zai dakushe yankinsu saboda yadda kamfanoni suka fi yawa a jihar Legas da ke kudancin ƙasar.
Ckin gwamnonin da ke adawa da sabon tsarin na APC ne suka fi yawa. Sai dai gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na cewa sauye-sauyen za su rage wa ɗaiɗaikun 'yan ƙasa kuɗin haraji, da kuma buɗe sabbin ƙofofin tara kuɗaɗe daga harajin.
"Zuwa yanzu jam'iyyar APC ba ta fitar da wata matsaya ba game da wannan batu da ke jawo rarrabuwar kai," kamar yadda mai magana da yawun jam'iyyar Bala Ibrahim ya shaida wa BBC.
Zazzafar adawa daga gwamnonin APC
A farkon watan Oktoban wannan shekarar ne Bola Tinubu ya aike da wasu ƙudurorin huɗu gaban majalisar dokokin ƙasar domin neman amincewarta.
Jim kadan bayan haka ne kuma gwamnoni – na PAC da na adawa - da ma wasu ‘yan ƙasa da dama suka fara nuna adawa.
Yayin wani taro da ƙungiyar gwamnonin arewacin ƙasar ta yi a Kaduna a ƙarshen watan Oktoba, sun ce sabon ƙudirin ya saɓa wa muradun jihohinsu, kuma suka yi kira ga ‘yan majalisar yankin su yi watsi da shi a zauren majalisar dokokin ƙasar.
“Abin da ya sa ba mu yarda ba shi ne, ana karɓar harajin VAT ne a hedikwatar kamfanonin maimakon inda sauran rassan kamfanonin ke gudanar da ayyukansu ko sayar da kayayyakinsu,'' in ji shugaban ƙungiyar Gwamnan Gombe Muhammad Inuwa Yahaya – wanda ɗan APC ne.
''Don haka ne ƙungiyarmu ta yi watsi da wannan sabon ƙudiri, kuma muke kira ga 'yan majalisar dokokinmu su yi watsi da shi saboda babu abin da ya ƙunsa ban da cutar da al'ummarmu.”
A makon nan ma Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya jaddada wannan matsaya a hirarsa da BBC, inda ya gargaɗi Bola Tinubu game da ƙuri'un da zai iya rasawa daga yankin a zaɓe na gaba..
"Mun yi tir da wannan dokar da aka kai majalisa saboda zai kawo wa Arewa koma-baya...idan wannan ƙudirin ya wuce (nasara) ko albashi ba za mu iya biya ba," in ji shi.
"Ya kamata Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya duba wannan lamari, saboda kashi 60 cikin 100 na ƙuri'un da ya samu daga Arewa ne. Idan an yi mana abin da muke so to shikenan; abin da muke so yanzu shi ne a jingine maganar wannan haraji."
Shi ma Farfesa Muhammad Muntaqa Usman na Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya ya ƙarfafa wannan fargabar ta gwamnonin Arewa.
''Idan ka duba inda ake karɓar harajin za ka ga cewa a hedikwatar kamfanonin ne, kamar bankuna da sauransu. Duk VAT ɗin ana tara shi ne a hedikwatar kamfanonin, to kuma yawancinsu suna Legas ne," a cewarsa.
Zazzafar muhawara tsakanin 'yanmajalisar APC
Makonnan cike yake da zazzafar muhawara a majalisar tarayyar Najeriya - ta wakilai da ta dattawa.
Sai dai babbar muryar da aka fi ji wajen adawa da wannan ƙudiri ita ce ta Sanata Ali Ndume mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu a majalisar dattawa. Zuwa yanzu an fi jin adawa daga sanatan na APC game da batun sama da 'yan jam'iyyar adawar ma kansu.
Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta a ranar Laraba ya nuna yadda gogaggen sanatan na jam'iyyar APC ya dinga musayar kalamai da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin (wanda ya jagoranci zaman a ranar) kan ƙudirin.
Sun yi musayar ce saboda matakin da shugabancin majalisar ya ɗauka na sauya jadawalin abubuwan da za a gudanar a zauren majalisar tare da cusa batun bai wa mambobin kwamatin gyaran harajin damar yi wa 'yanmajalisar jawabi a kan ƙudirin.
Jim kaɗan bayan gama magana kuma sai Sanata Mohammed Tahir Monguno mai wakiltar Borno ta Arewa - wanda shi ne ya maye gurbin Dume a matsayin babban mai tsawatarwa na majalisa - ya tashi, inda ya kare ƙudirorin a matsayin "wanda za su taimaki talaka".
A wannan zaman ne kuma majalisar ta yi wa ƙudirorin karatu na biyu, sannan ta miƙa shi hannun kwamatin harkokin kuɗi domin ci gaba da aiki a kansu.
Ita ma Majalisar Wakilan Najeriya ta auka ciki ruɗani da hayaniya a ranar Alhamis yayin wani zaman sirri da suka yi ba tare da 'yanjarida ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wani ɗanmajalisa da ya nemi jaridar sakaya sunansa ya ce "an tafka muhawara cikin ɓacin rai" musamman daga ɓangaren 'yanmajalisar Arewa.
Me APC ke yi kan lamarin?
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta fara mulkin Najeriya ne tun daga 2015, bayan Muhammadu Buhari ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa, kafin daga bisani ta sake yin nasara da Bola Tinubu a matsayin ɗantakararta a zaɓen 2023.
Tun a lokacin yaƙin neman zaɓe Tinubu ya yi alƙawarin ɗaukar matakan gyara tattalin arzikin Najeriya, waɗanda yake aiwatarwa a yanzu - da suka haɗa da cire tallafin mai, da sauya tsarin canjin kuɗi, da kuma batun harajin.
Mai magana da yawun APC, Bala Ibrahim ya ce za ta ji ra'ayin jama'a kafin ta ɗauki wata matsaya.
"Da yake jam'iyya ce mai son cigaba, za ta ji ra'ayin jama'a tukunna kafin ta ɗauki wata matsaya. Kawo yanzu ba a kai ga wannan gaɓar ba tukunna," in ji shi.
To ko yaushe za a yi hakan?
"Ba na jin za a yi wani abu na gaggawa daga yanzu zuwa ƙarshen shekara, saboda akwai abubuwa na gaggawa da ake so a kammala domin rufe shekarar."