Abin da muka sani kan tura ƙarin sojojin Amurka 200 zuwa Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin tura sojojinta 200 zuwa Najeriya a ci gaba da yunƙurin Amurkar na taimaka wa Najeriya wajen yaƙi da matsalar tsaro.
Tuni hukumomin Najeriya suka tabbatar da batun, inda mai magana da yawun shalkwatar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Sama'ila Uba ya tabbatar wa BBC hakan.
Uba ya ce "bisa ga buƙata da gwamnatin Najeriya ta miƙa da kuma shawarwarin kwamitin haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka, Amurka ta turo tawagar sojoji da za su taimaka a ɓangaren horaswa da kula da na'urori domin taimakawa da kuma bayar da shawara a wurare daban-daban na Najeriya.
"Waɗannan sojoji ba za su shiga fagen daga ba kuma ba za su fafata ba kai-tsaye," a cewar Janar Uba.
Jaridar Amurka ta US Daily ta ce ana sa ran ƙarin dakarun na Amurka za su isa Najeriya a makonni masu zuwa, kuma cikin ayyukan da za su yi har da taimaka wa sojojin Najeriya wajen tsara ayyukan da suka haɗa da hare-haren sama da na ƙasa.
Najeriya na ci gaba da fuskantar matsi na diflomasiyya daga Amurka kan matsalar tsaro a ƙasar, wanda shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a matsayin 'musgunawa' da kuma ''kisan'' Kiristoci.
Sai dai Najeriya ta musanta zargin, inda ta ce ana kashe mutane a Najeriya ba tare da la'akari da addininsu ba.
Bayanai da ƙungiyoyin bincike kan rikice-rikice suka fitar sun sha bamban da iƙirarin na Donald Trump.
Masana sun fi Kallon matsalar tsaron ta Najeriya a matsayin gazawar hukumomi wajen kawar da matsalar ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a yankuna marasa tsaro na Najeriya.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da saɓanin da aka samu tsakanin Najeriya da Amurka, ƙasashen biyu sun samu damar cimma matsaya, ta hanyar kafa kwamitin aiki tare da kuma ƙarfafa alaƙa ta tsaro.
A watan Disamban shekarar da ta gabata Amurka ta kai hari kan sansanin ƴan bindiga masu alaƙa da ƙungiyar IS a jihar Sokoto ta arewa maso yammacin Najeriya, wani mataki da Najeriya ta ce ya samu sahhalewarta.
Haka nan Amurka ta kuma ce sojojinta za su riƙa taimaka wa Najeriya da bayanan sirri da kuma sauƙaƙa sayen makamai.
A cikin watan Janairu wani jirgi ya kai makamai Najeriya, inda Amurkar ta ce hakan na cikin ƙoƙarinta na yauƙaƙa alaƙa da Najeriya.
Najeriya, wadda it ace ƙasa mafi yawan al'umma a Najeriya na fama da matsalar tsaro ta masu tsattsauran ra'ayi addini a arewa maso gabashin ƙasar, haka nan tana fama da ayyukan ƴan bindiga a arewa maso yammaci, wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
A yankin tsakiyar asar kuwa rikici tsakanin manoma da makiyaya ya yi sanadiyyar rasa rayuka masu ɗimbin yawa, masana na alaƙanta lamarin da fafutikar neman abin rayuwa.











