'Jihohin da aka fi kashe mutane a Najeriya cikin watan Janairu'

Gwamnonin wasu jihohin da ke fama da matsalar tsaro

Asalin hoton, Social Media

Lokacin karatu: Minti 3

Matsalar tsaro ta kasance kan gaba cikin abubuwan da suka fi ajalin mutane a ƙasar.

Rikice-rikice, kama daga na ƴanbindiga masu ɗauke da makamai zuwa faɗan ƙabilanci na daga cikin abubuwan da ke janyo mace-mace a ƙasar, da ke zaman giwar Afirka.

A watan Janairun ne dai aka kai wani mummunan hari Ƙauyen Kasuwan Daji da ke jihar Neja tare da kashe aƙalla mutum 30.

Kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited mai nazarin tsaro a yankin Sahel ya ce kimanin mutum 661 ne suka mutu, yayin da aka sace mutum 475 a watan farkon na sabuwar shekarar 2026.

Beacon Security ya ce a watan da ya gabata, ƙungiyoyin mayaƙa masu riƙe da makamai da sauran masu aikata miyagun ayyuka sun ci gaba da kai hare-hare a yankuna da dama na ƙasar

Cikin rahoton wata-wata da kamfanin ke fitarwa ya nuna cewa an samu ƙaruwar mace-macen mutane a ƙasar idan aka kwatanta da watan Disambar shekarar da ta gabata.

Beacon Security and Intelligence Limited ya zayyano jihohin ƙasar da aka fi samun kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane a ƙasar, da ta fi kowace yawan al'umma a Afirka.

Borno

Wasu ƴanbindiga

Asalin hoton, Getty Images

Jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya ta kasance kan gaba wajen kashe-kashen da aka samu a ƙasar cikin watan Janairun da ya gabata, kamar yadda Kamfanin Beacon Security ya nuna.

Rahoton ya ce an kashe mutum 200 a jihar cikin watan farkon na shekarar 2026.

Haka kuma rahoton ya ce jihar ce ta bakwai cikin jerin jihohin da aka fi sace mutane a watan Janairun da ya gabatan.

Jihar Borno da ke iyaka da ƙasashen Nijar da Kamaru da Chadi ta yi ƙaurin-suna a ayyukan ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi.

Ƙungiyar Boko Haram da ta ISWAP ne kan gaba wajen kai munanan hare-hare a jihar, musamman kan jami'an tsaro da fararen hula.

Neja

gwamnan Neja

Asalin hoton, Umar Mohammed Bago/Facebook

Kamfanin na Beacon Security ya saka jihar Neja a matsayi na biyu cikin jerin jihohin da aka fi kashe mutane a watan Janairu.

Jihar - wadda ke yankin arewa ta tsakiyar Najeriya - na daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren ƴanbindiga a Najeriya.

Rahoton na Beacon Security ya nuna cewa na kashe mutum 81 cikin watan da ya gabatan.

Cikin watan da ya gabatan ne dai wasu ƴanbindiga suka kai wani mummunan hari ƙauren Kasuwan Dawa tare da kashe aƙalla mutum 30.

Benue

Jihar Benue ce ta uku cikin jerin jihohin da aka fi kashe mutane cikin watan Janairun da ya gabatan, kamar yadda rahoton kamfanin Beacon Security ya nuna.

Rahoton ya nuna cewa an kashe mutum 48 a jihar cikin wajan Janairun da ya gabata.

Jihar ta Benue - wadda ke tsakiyar Najeriya ta yi iyaka da jihohin Nasarawa da Taraba da kuma jihar Kogi masu fama da matsalolin tsaro.

Benue ta yi ƙaurin-suna wajen rikicin ƙabilanci da faɗa tsakanin manoma da makiyaya da ke ɗaukar fansa tsakanin juna lokaci zuwa lokaci.

Yobe

Jihar Yobe - wadda ita ma ke yankin arewa maso gabashin Najeriya - ce ta huɗu cikin jerin jihohin da aka fi kashe mutane a watan Janairu, a cewar kamfanin Beacon Security.

Rahoton ya ce kimanin mutum 41 ne aka kashe cikin watan da ya gabata a jihar.

Jihar Yobe mai makwabtaka da Borno na daga cikin jihohin da ke kan gaba wajen fuskantar hare-haren mayaƙan Boko Haram da na ISWAP.

Filato

Jihar Filato da ke yankin arewa ta tsakiyar Najeriya ce ta biyar cikin jerin jihohin da aka fi samun kashe-kashe a watan Janairu, a cewar Kamfanin Beacon Security.

Rahoton ya ce cikin watan farkon an 2026 an kashe mutane 31 a jihar.

Jihar Filato ta yi ƙaurin-suna wajen rikicin ƙabilanci da na manoma da makiyaya, waɗanda a lokuta da dama kan yi sanadin rasa rayuka masu yawa.