‘Sun yanka mutane kamar kaji’:Yadda aka kashe fiye da mutum 30 a Neja

Asalin hoton, Zakari Kontagora
Al’ummar ƙauyen Kasuwan Daji da ke jihar Neja sun zama na baya-bayan nan da suka fuskanci cin zarafin ƴanbindiga, waɗanda suka kwashe kimanin shekara 10 suna kai farmaki a ƙauyuƙan arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiyar Najeriya.
Wani ɗanjarida a jihar Neja ya shaida wa BBC cewa "Ƴanbindigar sun shiga garin a kan babura ɗauke da makamai, inda suka tattara mutane kuma daga baya suka riƙa bi suna masu yankar rago, wasu kuma suka harbe su. Wanda kawo yanzu an tattara gawarwaki aƙalla 42.''
Wannan na zuwa ne ƙasa da wata biyu da wasu ƴanbindiga suka sace ɗalibai da malamai sama da 200 a ƙauyen Papiri da ke jihar ta Neja, lamarin da ya tayar da hankulan al’umma.

Asalin hoton, Zakari Kontagora
A baya-bayan nan shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaddamar da hare-hare kan wasu yankuna na arewa maso yammacin Najeriya da sunan murƙushe ayyukan ƴanbindigar.
Sai dai babu wani bayani da ya iya tabbatar da cewa harin na Amurka ya kashe ko illata irin waɗannan ƴanbindiga da ke kai hare-hare cikin ƙauyuka, suna kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
A wani saƙo da rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Neja ta fitar, ta tabbatar da harin na ranar Asabar, tare da bayyana cewa ‘an kashe mutum fiye da 30’ a ƙauyen na Kasuwan-Daji da ke yankin Demo a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar.
Maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mutane da ba a tantance yawan su ba, tare da ƙona kasuwar bayan sun kwashi kayan abinci da sauran kayayyaki.
Yadda lamarin ya faru
Wasu mazauna yankin sun bayyana yadda lamarin ya faru, wanda suka ce ya matuƙar girgiza su.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɗaya daga cikin mutanen yankin da muka sakaya sunansa ya ce yana zaune a gida sai ya samu labarin cewa wani abu na faruwa a Kasuwan Daji.
''Daga ƙauyenmu na riƙa hango hayaƙi na tasowa daga ƙauyen'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa daga baya ne ake sanar da shi cewa Kasuwar Daji aka ƙona.
''Ba ma ƙone kasuwar kawai ba, an shaida mana cewa an harbe mutane da yawa, yayin d aka ɗaure wasu da igiya kafin daga baya a yanka su kamar raguna'', in ji mutumin yayin da yake magana cikin alhini.
Ya ci gaba da cewa ''Ya zuwa yanzu mun ƙirga gawa 42 na mutanen da aka kashe, sannan ga guda ɗaya can mun samu labari yanzu an ganshi a daji na rabaran ɗin garin.''
Shi ma wani mutum da ya shaida lamarin ya bayyana yadda ya ji da mummunan harin.
''Ƴanbindiga sun shigo ƙauyen inda suka riƙa kashe mutane ba ji ba gani tare da ƙona gidaje da dukiyoyi'', in ji shi.
Ya ce babu jami'an tsaro a ƙauyen, don haka ne ya yi kira ga gwamnati ta kai musu ɗauki, saboda ba su san halin da mutanen da aka sace ke ciki ba.
''Muna so gwamnati ta taimake mu, a baya mukan ji labarin wannan matsala a wasu wurare, amma a yanzu tana faruwa a ƙauyukanmu'', kamar yadda ya bayyana, yayin da yake tsaye kusa da gawarwakin mutanen da aka kashe.
Mutumin ya ci gaba da cewa maharan kan fitar da su daga gidajensu. ''Muna mutuwa kamar kaji, anya kuwa gwamnati ta damu da mu?''
''Gwamnati na ji da ganin abin da ke faruwa, amma ba abin da take yi a kai, mu me za mu iya yi a matsayinmu na talakawa''?
Ya ce a ƙauyen aka haife su sannan suka taso a ciki, amma yanzu sun zama tamkar ƴangudun hijira.
'Fiye da mutum 30 aka kashe'
Wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar Neja SP Wasiu Abiodun ya fitar ta ce jami'ansu sun samu kiran waya da misalin ƙarfe 9 na dare, a ranar Asabar 3 ga watan Janairun 2026, inda aka shaida masu cewa "wasu da ake zargin ƴanbindiga ne da ke ayyukan su a dajin Kainji sun afka wa kasuwar ƙauyen na Kasuwan-Daji da misalin ƙarfe 4 na yamma,"
Sanarwar ƴansandan ta ce "Ya zuwa ƙarfe 8 na safiyar ranar Lahadi 04/01/2026, tawagar jami'an tsaro ta isa wajen kuma ta tabbatar cewa an kashe mutum fiye da 30 a yayin harin. An kuma yi garkuwa da wasu."
Sai dai bayanan da BBC ta tattara daga wasu mutanen yankin na cewa mutanen da aka kashen sun zarce yadda rundunar ƴansandan Najeriya ta sanar.
"Akwai kuma wasu mutanen da suka mutu a cikin gidaje da kuma cikin daji, waɗanda har yanzu ba a tantance yawan su ba,'' in ji ɗanjaridar da BBC ta zanta da shi.

Asalin hoton, Zakari Kontagora
Mazauna yankin sun ce ƴanbindigar sun afka wa ƙauyen Kasuwan-Daji ne a kan Babura, da goyon bibbiyu ɗauke da bindigogi da sauran manyan makamai, kuma tun daga yammacin Asabar da suka aikata ɓarnar har zuwa Lahadi da safe babu wani jami'in tsaro ko na gwamnati da ya ziyarci yankin.
SP Wasiu Abiodun ya ce gamayyar jami'an tsaro na bin sahu domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
Wajibi ne a kamo su kuma a hukunta su - Tinubu
Bayan kai harin, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci ministan tsaro na kasar da manyan hafsoshin sojin kasar da sufeta-janar na 'yansandan lasar da kuma shugaban hukumar farin kaya ta DSS da su kamo wadanda suka kai harin na Ksuwan Daji domin gurfanar da su a gaban shari'a.
A cikin wata sanarwa da shugaban kasar ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya ce "wadannan 'yan ta'adda sun kalubalance mu, saboda haka dole ne su dandana kudarsu kan abin da suka aikata.
"Ko su wane ne su, kuma ko da wace aniya suka aikata hakan, wajibi ne a kamo su.
"Su, da duk wadanda suka taimaka musu ta kowace hanya, za a kamo su sannan za su fuskanci shari'a," kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Bugu da kari shugaban kasar ya bayar da umarnin kwato dukkanin mutanen da yan bindigan suka yi garkuwa da su.
Sanarwar ta bayyana cewa ana zargin cewa wadanda suka kai harin 'yan bindiga ne da ke tserewa daga jihohin Sokoto ta Zamfara bayan harin da Amurka ta kai ta sama a yankin a jajibirin Kirsimeti.










