Champions League: Me kuke son sani kan wasannin ranar Laraba?

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 9

Wasa tara za a yi a Champions League ranar Laraba a wasu daga manyan filaye a faɗin nahiyar Turai.

Karawa ta biyar-biyar da za a ci gaba a cikin rukuni, inda ake sa ran samun waɗanda za su kai zagaye na biyu wato na rukunin ƴan 16 a gasar.

Kawo yanzu ƙungiya uku ce take da maki 12 kowacce - da ta haɗa da Bayern Munich da Arsenal da Inter Milan.

Borussia Dortmunda da Chelsea da kuma Manchester City, kowacce tana da maki 10.

Sauran da ke cikin ƴan takwas ɗin farkon teburi sun haɗa da Paris St Germain mai rike da kofin da kuma Newcastle United masu tara-tara kowacce.

Waɗanda suke na ƙarshen teburi sun haɗa da Keirat da Ajax ta biyun ƙarshe da kuma ta ƙarshe, bayan karawa ta biyar-biyar a cikin rukuni.

Duk ƙungiyar da ta kare daga matakin farko a teburi zuwa ta 16 ne za su je zagaye na biyu a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai ta kakar nan.

Copenhagen da Kairat Almaty

Wannan shi ne karon farko da ƙungiyoyin za su kece-raini, kuma karon farko da Copenhagen za ta fuskanci ƙungiya daga Kazakhstan.

Copenhagen ta ci wasa biyu daga 16 baya a Champions League aka doke ta takwas da canjaras shida, sannan ta yi rashin nasara uku a jere.

Sai dai ƙungiyar Denmark ta zura ƙwallo a wasa 18 a gasar zakarun Turai da ta buga a gida, yayin da wasa ɗaya ne daga 29 baya ta tashi ba ci a babbargasar tamaula ta Turai.

Wasan da Kairat Almaty ta yi a gasar zakarun Turai da ƙungiyar Denmark, shi ne da Esbjerg a zagaye na biyu a Europa League a kakar 2014/15.

Ta tashi 1-1 a gida, sannan ta yi rashin nasara 1-0 a zagaye na biyu a Denmark.

Kawo yanzu Kairat ta yi wasa tara ba tare da yin nasara ba a gasar ta zakarun Turai da ta buga a waje daga ciki ta buga canjaras uku aka doke ta wasa bakwai.

Pafos da Monaco

Wannan shi ne karon farko da za su fafata tsakanin ƙungiyar Faransa da ta Cypros.

Pafos na fatan zama ta farko daga Cyprus da za ta ci wasa biyu a jere Champions League proper. Wadda ta yi rashin nasara ɗaya daga fafatawa 10 a gasar a bana da cin karawa biyar da canjaras huɗu.

Haka kuma ƙungiyar ta yi wasa shida ba tare da ƙwallo ya shiga ragarta ba a karawa tara baya a gasar ta zakarun Turai.

A wasa na hurhuɗu a cikin rukuni da ta fuskanci Bodo/Glimt, Monaco ta kawo karshen kasa cin wasa daga fafatawa shida a Champions League daga ciki aka doke ta uku da canjaras uku, sai dai a wannan lokacin ta ci wasa ɗaya da canjaras biyu daga fafatawa uku bayan nan.

Idan har ƙwallo bai shiga ragar Monaco ba, zai zama karon farko da za ta yi wasa uku da wannan bajintar a Champions League tun bayan wasan cikin rukuni a 2014/15.

Arsenal da Bayern Munchen

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal ba ta ci Bayern Munich ba a karawa biyar baya a gasar zakarun Turai daga ciki aka doke ta huɗu da canjaras ɗaya.

Sai dai kuma Gunners nasara biyu ta yi daga fafata tara da ta fuskanci ƙungiyoyin Jamus daga ciki ta yi canjaras ɗaya aka doke ta shida daga ciki.

Ƙungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama ta ci wasa takwas daga fafatawa 15 baya a gida a karawar cikin rukuni daga ciki wasa 12 ƙwallo bai shiga ragarta ba.

Bukayo Saka ya zura ƙwallo takwas daga wasa 10 baya da ya yi a gasar ta zakarun Turai.

Wasa biyu kacal Bayern ta yi rashin nasara daga fafatawa 12 da ta fuskanci ƙungiyoyin Ingila, inda ta yi nasara takwas da canjaras biyu.

Haka kuma wasa uku aka doke ƙungiyar Bayern Munich daga 52 da ta yi a cikin rukuni a Champions League.

Harry Kane ya zura ƙwallo 15 a wasa 21 da ya fuskanci Arsenal a dukkan fafatawa. Ya kuma ci Arsenal ƙwallo a Emirates a zagayen farko a kwata fainal a Champions League a 2023/24.

Atletico de Madrid da Inter Milan

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wannan shi ne karo na biyar da za su fuskanci tsakanin Atletico da Inter Milan.

Wasan da suka kara a bayan nan shi ne a Champions League a 2023/24 zagayen ƴan 16, inda ta kai da bugun fenariti, kuma Atletico ta yi nasarar cin 3-2.

Atletico ta yi nasara takwas daga wasa 10 baya a gasar zakarun Turai a gida da ta fuskanci ƙungiyoyin Italiya daga ciki ta yi canjaras ɗaya da rashin nasara ɗaya.

Julian Alvarez na Atletico ya zura ƙwallo tara a wasa 13 a Champions League, wanda ya ci takwas a karawa 17 a tsohuwar ƙungiyarsa Manchester City.

Wasa ɗaya aka ci Inter daga karawa takwas a gasar zakarun Turai da ta fuskanci ƙungiyoyin Sifaniya daga ciki ta yi canjaras huɗu da cin uku daga ciki.

Ƙungiyar ta Italiya ta yi rashin nasara ɗaya daga fafatawa 18 a wasan cikin rukuni a Champions League daga ciki ta ci 13 da canjaras huɗu daga ciki.

Lautaro Martinez ya zura ƙwallo 12 a raga a wasa 11 baya a Champions League, haka kuma ya ci ƙwallo a dukkan wasa biyar baya a gasar.

Eintracht Frankfurt da Atalanta

Wannan shi ne wasan farko da za a yi a gasar zakarun Turai tsakanin Frankfurt da kuma Atalanta.

Frankfurt ba ta yi nasara ba a wasa huɗu a gasar da ta kara da ƙungiyoyin Italiya da kasa zura ƙwallo a raga daga cikin fafatawar, wadda aka doke uku daga ciki da yin canjaras ɗaya.

Ita kuwa Atalanta wasa biyu aka doke ta daga 10 baya a gasar ta zakarun Turai da ta fuskanci ƙungiyoyin Jamus daga ciki ta yi nasara biyar da canjaras uku.

Kuma tana fatan cin wasa na uku a jere da ƙungiyoyin da ke buga Bundesliga, bayan cin Leverkusen 3-0 a 2023/24 a Europa League da 2-0 da ta je ta doke Stuttgard a karawa ta hurhuɗu a cikin rukuni a bara a Champions League.

Wasa ɗaya Atalanta ta yi rashin nasara daga 10 baya da ta je ta buga a waje daga ciki ta yi nasara shida da yin canjaras uku.

Liverpool da PSV Eindhoven

Mohammed Salah

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta ci wasa biyar daga bakwai baya a gasar zakarun Turai da ta kece raini da PSV Eindhoven daga ciki aka doke ta ɗaya da canjaras ɗaya.

PSV ta yi nasara a kan Liverpool a haduwar bayan nan da cin 3-2 a Eindhoven a kakar bara.

Idan har Liverpool ta zura ƙwallo zai zama na 500 a gasar zakarun Turai ko dai ta European Cup ko kuma Champions League.

Mohamed Salah na bukatar cin ƙwallo biyu a raga nan gaba, hakan zai zama na farko daga Afirka da zai ci 50 a gasar ta Champions League.

Ba a doke Liverpool ba a wasa tara baya a gasar ta zakarun Turai da ta buga a Anfield da ƙungiyoyin Netherlands daga ciki ta yi nasara bakwai da canjaras biyu - haka kuma ta cinye wasa 16 baya a gida.

Ɗan wasan da aka haifa a Eindhoven, Cody Gakpo ya koma Liverpool daga PSV a Janairun 2023. Mai shekara 26 ya zura ƙwallo 55 a fafatawa 159 a PSV daga nan ya koma ƙungiyar da take buga Premier League.

PSV ta yi nasara ɗaya daga wasa 14 baya a gasar zakarun Turai da ta buga a waje da ƙungiyoyin Ingila daga ciki ta yi canjaras biyar aka doke ta takwas.

Ƙungiyar Eindhoven ta sha kashi a wasa uku daga 17 a cikin rukuni a Champions League da yin nasara bakwai da canjaras bakwai, haka kuma ta zura ƙwallo a dukkan wasa 16 baya.

Ricardo Pepi ya zura ƙwallo a raga a wasa huɗu a Champions League daga ciki har da wadda ya ci Liverpool a karawa ta takwas a cikin rukuni a bara.

Olympiacos da Real Madrid

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Wannan shi ne karo na tara a gasar zakarun Turai tsakaninsu, inda Real Madrid ta ci huɗu da canjaras uku aka doke ta wasa daya daga ciki.

Wasan da Olympiacos ta yi nasara shi ne 2-1 a cikin Disambar 2005 a gidanta - amma kuma Real ba ta yi nasara ba a kanta a karawa huɗu a Girka, wadda ta yi nasara daya da canjaras uku.

Wasa biyu Olympiacos ta yi rashin nasara daga 16 baya da ta fuskanci ƙungiyoyin Sifaniya a Girka, inda ta ci shida da yin canjaras takwas. Haka kuma ba a doke ta ba a wasa tara baya a gasar ta zakarun Turai a gida.

Ƙungiyar ta Girka ta yi nasara biyu daga wasa 24 a Champions League fafatawar cikin rukuni daga ciki ta yi canjaras huɗu aka doke ta 18, sannan ba ta yi nasara ba daga tara.

Real Madrid ba ta ci wasa ba daga fafatawa bakwai a gasar zakarun Turai da ta fuskanci ƙungiyoyin Girka daga ciki canjaras biyu ta yi da rashin nasara biyar - wasa mai yawa da ta je ta buga a wata kasa ba tare da yin nasara ba.

Watakila Federico Valverde ya zama na uku ɗan kasar Uruguayan da zai yi karawa ta 70 a Champions League, bayan Luis Suárez mai karawa 73 da kuma Edinson Cavani da ya yi wasa 70.

Idan kuma Vinícius Júnior ya ci ƙwallo ɗaya zai yi kan-kan-kan da Kaká mai ƙwallo 30 Champions League daga Brazil.

Paris Saint-Germain da Tottenham

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Wasan da suka fuskanci juna a bayan nan tsakanin Paris St German da Tottenham shi ne a 2025 a UEFA Super Cup.

Bayan da aka fara cin ƙungiyar Faransa 2-0 daga baya ta sa ƙwazo ta farke ta kuma lashe kofin a bugun fenariti.

Wasa biyu PSG ta kasa ci daga takwas baya a gasar zakarun Turai da ta kece raini da ƙungiyoyinIngila daga ciki ta yi nasara biyar da canjaras ɗaya.

Haka kuma ƙungiyar Faransa ba ta taɓa rashin nasara biyu ba a jere a Champions League a zagayen cikin rukuni.

PSG ta buga wasa 104 a jere a gasar zakarun Turai tun daga lokacin da ta tashi 0-0 da Real Madrid a 2015/16 karawar cikin rukuni.

Tottenham ba ta yi rashin nasara ba a wasa uku da ta fuskanci ƙungiyoyin Faransa a Champions League daga ciki ta ci biyu da canjaras da canjaras ɗaya.

Haka kuma Tottenham ba a doke ta ba a karawa takwas baya a zagayen cikin rukuni ba a Champions League daga ciki ta yi canjaras huɗu da cin wasa huɗu.

Haka kuma kungiyar Arewacin Landan ta yi wasa biyar daga bakwai ba tare da ƙwallo ya shiga ragarta ba a babbar gasar ta zakarun Turai.

Sporting da Club Brugge

Wasan da suka fuskanci juna a baya a gasar zakarun Turai tsakaninsu, sun yi ne a wasa na shida a cikin rukuni a bara a Champions League, inda ƙungiyar Belgium ta yi nasara a gida da cin 2-1.

Sporting ta yi wasa huɗu a gida ba tare da an doke ta ba da ta fuskanci ƙungiyoyin Belgium daga ciki ta yi nasara uku da canjaras ɗaya.

Ƙungiyar ta Portugal ta yi rashin nasara biyu daga wasa 11 a gasar ta Champions League a gida, wadda ta lashe fafatawa shida da kuma canjaras uku.

Ɗan wasa Geovany Quenda mai shekara 18 da kwana 210 zai zama matashin farko daga Portugal da zai yi wasa na 15 a Champions League, bayan tarihin Ruben Neves ya rike a lokacin da yake shekara 19 da kwana 269.

Club Brugge ta yi nasara biyu daga fafatawa bakwai a gasar zakarun Turai da ta yi a waje da ƙungiyoyin Portugal, inda aka doke ta biyar daga ciki.

Ƙungiyar Belgium ta ci ƙwallo uku ko fiye da haka a wasa biyar daga fafatawa bakwai baya a babbar gasar ta zakarun Turai.