Raunin Kudus ya sa Tottenham neman sabon ɗan gaba, Liverpool ta ƙi sayar da Chiesa

Mohammed Kudus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mohammed Kudus
Lokacin karatu: Minti 3

Newcastle United za ta yi gogayya da Tottenham idan ta koma wurin kungiyar Wolves a kokarin da take yi domin siyan dan wasan NorwayJorgen Strand Larsen mai shekara 25. (ChronicleLive)

Tottenham za ta sayi wani sabon dan wasan gaba a watan nan na Janairu saboda raunin da dan wasan Ghana Mohammed Kudus, mai shekara 25 ya ji , ya yi muni fiye da yadda suka yi tunani tun farko. (Telegraph)

Darektan kungiyar Roma, Ricky Massara ya ce halin da ake ciki game da duk wani yunkuri na siyan dan wasan gaban Manchester United Joshua Zirkzee, mai shekara 24, ya sauya saboda korar da aka yi wa kocin kungiyar ta Old Trafford, Ruben Amorim (Sky Sports)

Fatan da Juventus take da shi na siyan dan wasan Italiya Federico Chiesa, mai shekara 28, daga Liverpool ya dogara ne kan ko dan wasan Masar Mohamed Salah, mai shekara 33, zai ci gaba da taka leda a Anfield. (La Gazzetta dello Sport)

Ita ma Napoli na son Chiesa sai dai Liverpool ba ta sami wani tayi a hukumance ba daga wata kungiya ba kuma abu ne mai wuya ta sayar da shi a watan Janairu. (Sky Sports News)

Dan wasa mai kai hari na Poland Robert Lewandowski ba ya son ya bar Barcelona a watan Janairu duk da cewa akwai kungiyoyi da dama da ke zawarcin dan wasan mai shekara 37. (Sky Sports)

Bayern Munich ta tsawaita kwantaragin dan wasan bayan Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 27 wanda wa'adinsa a kungiyar zai kare a bazara. (Sky Sports)

AC Milan na zawarcin dan wasan Bayern Munich Kim Min-jae, mai shekara 29, sai dai za ta nemi taimakon kungiyar ta Jamus ta bada gudummawa kan albashin dan wasan kasar Koriya ta Kudu domin su iya kulla yarjejeniya. (La Gazzetta dello Sport)

Dan wasa mai kai hari na Real Madrid, Endrick mai shekara 19 wanda ya je Lyon a matsayin aro ya ce kocin Brazil Carlo Ancelotti ne ya ba shi shawarar barin kungiyar ta Sifaniya domin ya kara samun kwarewa wajen buga tamaula . (Goal)

Yarjejeniyar da Leicester City ta gabatar wa dan wasa mai kai hari Michail Antonio, kuma tsohon dan wasan West Ham, ta wargaje sakamakon raunin da ya ji. Dan wasan Jamaica mai shekara 35 bai buga wasa ba tun bayan hadarin motar da ya yi a watan Disambar 2024, amma yana tattaunawa kan kwantaragin gajeren zango (Talksport)

Dan wasan Koriya ta Kudu Yang Min-hyeok, mai shekara 19, na gab da komawa South Coventry City a matsayin aro daga Tottenham. (Fabrizio Romano)