Mabaraci mai cutar polio da ya koma makaranta ya kuma zama likita

Hotunan Li a saman tsaunin Tai da a lokacin da yake dalibin likitanci, yana karanta littafinsa.

Asalin hoton, Dr Li Chuangye

    • Marubuci, Benny Lu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Chinese
    • Marubuci, Benny Lu
    • Marubuci, Vibeke Venema
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Marubuci, Vibeke Venema
  • Lokacin karatu: Minti 8

Nakasa ba kasawa ba! Li Chuangye likita ne mai shekara 37- wanda labarinsa ke cike da darasi da ƙarfafa gwiwa, musamman ga masu lalurar nakasa.

Bayan ya kamu da cutar polio, an tilasta masa zama mabaraci - amma ya fara koyon karatu da rubutu yana da shekara 16, domin cika burinsa.

Dr Li a kusa da tambarin tsaunin Henshang, yayin da ruwa ke zuba.

Asalin hoton, Dr Li Chuangye

Bayanan hoto, Dr Li ya hau duka manyan tsaunukan China biyar masu tsarki da kuma tsaunin Huangshan, da kuma babbar katangar China

An haife shi a shekarar 1988 a lardin Henan mai arzikin noma da ke ƙasar China.

Li Chuangye ya kamu da cutar polio a lokacin yana wata bakwai a duniya, lamarin da ya hana shi miƙewa ko tsayawa da ƙafarsa, inda yake tafiya ta hanyar caka hannayensa da ƙafafunsu a tare.

A lokacin da yake ƙarami, babban burin Li shi ne ya rataya jakarsa a baya ya tafi makaranta kamar yadda sauran yara ke yi, to amma ya gamu da cikas bayan d ayara suka riƙa zolayarsa.

Wasu yaran kan ce ba shi da "amfani", sai dai kawai ya ci abinci, amma ba shi da kataɓus".

"Wannan abin ya cutar da ni mataƙa," a cewar Li.

A lokacin da Li ya kai shekara tara, sai iyayensa suka samun labarin cewa akwai wata tiyatar ƙafa da ake yi, wadda za ta ba shi damar miƙewa ya taka da ƙafarsa, lamarin da ya sa suka karɓi ramncen kuɗi domin yin aikin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Li ya cika da fata dangane da aikin tiyatar. ''A lokacin da nake samun sauƙi a ɗakin tiyatar, na ji wasu yaran na kuka, amma ni murmushi kawai nake yi, saboda ina jin cewa na kusa fara tafiya kamar kowane mai lafiya,'' in ji shi.

To amma murnar Li ta koma ciki bayn da aikin tiyatar ya lalace, lamarin da ya jefa shi cikin tsananin damuwa.

Ya ji a ransa kamar rayuwarsa ba ta da amfani, inda ya ri ka faɗa wa mahaifiyarsa cewa shi ya ma fi son ya mutu.

Mahaifiyarsa ta faɗa masa cewa kada ya fitar d arai daga burinsa.

''Muna kula da kai, kuma za mu reneka, ta yadda idan mun tsufa za mu samu wanda zai kula da mu''.

Kalaman mahaifiyar tasa sun sosa masa zuciya. ''Na jinjina yadda iyayena da ƴan'uwa suka sadaukar da komai nasu a kaina, na take hawaye suka cika idanuna. Daga nan na ji a raina ya kamata in rayu, ko in taimaki iyayena da ƴa'uwana,'' in ji Li.

Ba a jima ba bayan haka wani baƙo daga birni ya zo ƙauyensu, yana neman yara masu lalurar nakasa da za su riƙa sayar da turaren wuta a majami'u.

Mutumin ya yi musu alƙawarin cewa idan ya ɗauki Li zai riƙa aika wa iyayensa kuɗin da suka kai daidai da wanda mahaifinsa ke samu a wata.

"Iyayena sun ƙi amincewa da buƙatar, amma sai nake ganin na samu damar da zan samu kuɗi domin rage wa iyayena nauyin da ke kansu.'' kamar yadda Li ya bayyana. Daga nan ya yarda ya bi mutumin zuwa birni.

Li Chuangye na amfaniu da hannayensa domin tallafa wa ƙafafunsa yayin da yake tafiya a tsugune.

Asalin hoton, Dr Li Chuangye

Bayanan hoto, Dr Li has livestreamed his hikes to thousands of fans

Bara a gefen titi

To sai dai kai, alƙawarin aikin da aka yi masa ashe damfara ce.

Dr Li ya ce ashe baƙon nan wani mutum ne da ke gudanar da harkokin bara a birni, ya kuma tilasta wa Li yin bara na tsawon shekara bakwai a gefen tituna tare da sauran ƙananan yara d ama manya.

A ranarsa ta farko da fara bara, ɗaya daga cikin yaran ya gargaɗi Li da cewa ya dage sosai, in ba haka ba zai sha duka. Kuma hakan ce ta kasance.

gari na wayewa aka ajiye Li a gefen titi, babu riga ajikinsa, inda aka ajiye masa roba da ƴan sulalla a ciki tare da naɗe ƙafafunsa a wani zama dai da ke cike da tausayawa.

Mutane kuwa suka yi ta kuɗi a cikin robar da ke gabansa, amma Li bai fahimci dalilin da ya sa suke zuba kuɗin ba, har sai lokacin da wasu masu wucewa suka tambaye shi me ya sa yake bara, maimakon ya tafi makaranta.

"A garinmu, bara abin kunya ne. Kuma ban san abin da nake yi ba kenan. wanna abu ya sosa min zuciya, na ji baƙin ciki da ɓacin rai amma ba yadda na iya dole na ci gaba,'' in ji Li.

A kowace rana Li kan samu ɗaruruwan Yuan - kuɗaɗe masu yawa a shekarun 1990 - amma kuma duk ubangidan nasa ke kwashewa.

"Idan ban samu kuɗin da sauran yara ke samu ba, yakan zarge ni da yin sakaci ko kuskure, inda a wasu lokutanma yakan dokeni, a haka na kwashe shekaru ina cikin wannan uƙuba.'' in ji shi.

Cikin shekaru masu yawa, sauran yaran suka gudu, wasu kuma ƴansanda suka mayar da su gida bayan kama su, amma Li bai koma gida ba, inda ya ci gaba da zama cike da burin tallafa wa iyayensa.

A lokacin da yansanda suka yi masa tayin taimaka masa domin mayar da shi gida, sai ya ƙi, ya kafe cewa shi ɗan'uwan mutumin ne, mutumin kuwa ya ci gaba da tilasta masa yin barar.

Li ya kwashe shekara bakwai rani da damina yana bara a faɗin ƙasar daga wannan gari zuwa wancan.

"Bara na da wahalar gaske. nakan ji kunya, bana iya haɗa ido da mutane, ƙafafuna sun riƙa yi mini ciwo saboda yadda yake ɗaure min su domin na zama abin tausayi.

Na yi ta adduna ba dare da rana Allah ya kawo min ƙarshen barar,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.

A kowace ranar jajiberin sabuwar shekara ubangidan nasa kan kira iyayen Li a waya domin ya haɗa su, su yi magana.

Idan yana waya da iyayen nasa Li kan jaddada musu cewa komai na tafiya yadda ya kamata, kuma kada su damu.

"Amma bayan gama wayar, nakan kulle kaina a ɗaki na sharbi kukana. saboda ba zan iya faɗa musu cewa bara nake a kan tituna ba,'' in ji shi.

Har yanzu kusan shekara 20 bayan gama barar, Li na tare da takaicin abin d aya yi.

"Bara na dankwafar da duk wani buri da kake da shi a rayuwa, har yanzu ina jin takaicin barar da na yi, nakan ji a raina dama a ce a mafarki ne.''

Dr Li ya ɗauki hoto a kusa da tambarin Tsauni Hua

Asalin hoton, Dr Li Chuangye

Bayanan hoto, Dr Li ya ce hawa tsauni na sanya shi nishaɗi

Sabuwar makoma ta hanyar ilimi

Komai ya sauya ne a lokacin da Li ya ɗauki wata jarida a gefen titi, kuma ya fahimci cewa zai iya karanta haruffan sunansa.

A lokacin yana da shekara 16, daga nan ya yanke shawarar komawa gida domin shiga makaranta.

"Ban iya karatu da rubutu ba, kuma ta hanyar ilimi ne kawai zan iya sauya rayuwata,'' a cewarsa.

A daidai wannan lokaci, gwamnati ta ɓullo da sabon tsarin da ya haramta amfani da yara masu nakasa domin yin bara.

Haka kuma Li ya samu labarin cewa tattalin arzikin iyayensa ya inganta.

Sai ya faɗa wa maigidansa cewa yana son ya ziyarci gida, sai ya ba shi dama.

Bayan sakewa haɗuwa da iyayen nasa, sun fahimci yadda ya sha wahalar rayuwa - Sanna Li ya ji takaicin yadda wanda ya ɗauke shi ke tura wa iyayensa kuɗi ƙasa da abinda suka yi alƙawari tun da farko.

Tare da goyon bayan iyayensa, Li ya shiga aji na biyu a makarantar furamare, cikin ƙananan yaran da ya fi su da aƙalla shekara 10.

A ranarsa da farko, yara sun kewaye kujerar da yake zaune a cikin aji, amma hakan bai dame shi ba.

''ban damu ba - saboda a baya na fuskanci abin da ya ma ya fi haka, amma a yanzu da nake ɗalibi abin da ke gabana shi abin da ya kaini makaranta,'' a cewarsa.

Lo ya kasance ɗalbi mafi hazaƙa, duk kuwa da nakasar da yake da ita tana zame masa tarnaƙi a wasu al'amuran karati, kamar zuwa banɗaki.

''Zuwa banɗaki kan bani wahala ƙwarai, don haka na taƙaita shan ruwa a makaranta saboda rage zuwa fitsari,'' in ji shi.

Yakan gayyato yaran kauyen domin yin wasa daga nan sai ya nemi taimakonsu kan yadda zai yi asayimen din da aka ba shi a makaranta.

Ta hanyar jajircewa da ƙwazo, Li ya kammala furamare da sakandire cikin shekara tara.

Da lokacin da zai shiga jami'a ya zo, nakasarsa ta taƙaita masa damarmaki, amma zai iya karanta fannonin kiwon lafiya.

Ya yi tunanin, "Idan na zama likita, wataƙila zan iya bincike akan jinyata, kuma zan taimaka wa iyalina, sannan zan kare rayuka, na kuma taimaka wa al'umma.''

Dr Li a ranar da ya kammala jami'a zaune a kan sukutarsa

Asalin hoton, Dr Li Chuangye

Bayanan hoto, Domin zuwa jami'a, Li kan yi doguwar tafiya a kan babur ɗinsa na nakasassu.

Liya samu gurbin karatu a jami'ar kiwon lafiya a lokacin yana da shekara 25.

Makarantar na da sauƙin zuwa agare shi, amma azuzuwan gwaje-gwaje sun riƙa ba shi wahala.

"A yayin da sauran ƴan ajinmu ke bin malamansu zuwa duba marasa lafiya a asibiti ko ziyara daga wannan ɗaki zuwa wancan a lokacin faratikal, nakasar da nake da ita kan ba ni wahalar yin hakan. Abin da saura za su koya a rana ɗaya, nakan ɗauki lokaci kafin na koya'', in ji shi.

Li ya ji ya kamata ya samu ƙarfi da ƙwari, don haka ya yanke shawarar ya riƙa hawa tsaunuka.

A karon farko da ya fara sai da ya shafe kwana biyarkafin ya isa ƙololuwar tsaunin Tai.

Duk da cewa hannayensa da ƙafafunsa sun kukkurje tare da zubar da jini, hakan bai sa ya saduda ba.

Haka dai ya ci gaba da hawa tsanuka duk a koƙarinsa na ƙarfafa jikinsa.

bayan kammala jami'a Mista Li ya fara aiki a matsayin likita, inda a yanke yake jagorantar wani ƙaramin asibitin ƙauye a Xinjing, inda yake bakin aiki ba dare da rana.

Marasa lafiya kan kira shi ''Ɗanbaiwan likita''.

"Kula da marasa lafiya da hannayena, da inganta lafiyar makwabtana na gamsar da ni fiye da komai,'' in ji shi.

Dr Li na hira da mutanen kauyensu

Asalin hoton, Dr Li Chuangye

Bayanan hoto, Dr Li na kula da asibitin ƙauye dare da rana

Rayuwa cike da ƙwarin gwiwa da kyakkyawan fata

Mutane da dama sun rika tambayar Li abin da ya hana shi kai rahoton mutumin da ya zalunce shi.

Amma shi yakan ce "Ya fi son a bar duk abin da ya wuce, duk da cewa na sha wahala, amma hakan ma yana cikin tarihin rayuwata.''

Rayuwar Li cike take da darussan da har yanzu ke ba shi mamaki. "Bayan na fara zuiwa makaranta, na yarda da maganar masu azanci da ke cewa nakasa ba kasawa ba''.

''Duk abin da ka ga mutum bai zama ba, to ba kaddararsa ba ce, kuma bai saka kansa ba'', in ji shi.

Dr Li Chuangye ya yi hira da shirin BBC Outlook