Ko nuna finafinai a gidajen gala zai inganta masana'antar Kannywood?

Bangon fim ɗin Gidan Badamasi

Asalin hoton, Falalu Dorayi

Bayanan hoto, Wasu 'yanwasan fim ɗin Gidan Badamasi kenan, wanda Falalu Dorayi (na farko daga hagu) ya bayar da umarni
Lokacin karatu: Minti 3

A daidai lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin inganta harkokin kasuwancin finafinan Kannywood, an fara tunanin a yi waiwaye domin duba wasu hanyoyin da aka bi a baya domin ƙara wa masana'antar tagomashi.

A yanzu dai masana'antar ta fi karkatar da akalar kasuwacinta ne kan haska finafinan a manhajar YouTube, inda mutane suke kallo, su kuma masu shirya finafinan suna samun kuɗin shiga.

Tun bayan da kasuwancin CD ya taɓarɓare ne masana'antar ta shiga tsilla-tsilla, inda mafi yawan furodusoshi suka koma gefe.

Sai dai masana'antar ta fara farfaɗowa a lokacin da aka koma amfani da sinima domin haska fina-finan, lamarin da ya zama sai a hankali saboda ba a cika samun kuɗin da aka yi hasashe ba.

Bayan rashin nasarar sinima, sai kuma aka fara kama hanyar komawa gida jiya a harkokin kasuwancin masana'antar. Ana cikin haka ne kuma sai aka fara komawa YouTube.

Duk da cewa ana ganin akwai damarmaki a YouTube, wasu suna ganin hanya ɗaya tilo ta yi kaɗan ta riƙe masana'antar baki ɗaya, wanda hakan ya sa wasu suke tunanin ɓullo da wasu hanyoyin zai yi kyau, wanda hakan ya sa ake tunanin komawa haska fim a gidan gala.

Haska fim a gidan gala

A game da batun komawa haska fim a gidan gala, malami a Jami'ar Cologne da ke Jamus, kuma mai sharhi kan harkokin finafinai, Dokta Muhsin Ibrahim ya ce dama asali akwai gidajen kallon finafinai a baya, wanda a cewarsa cigaba ne sosai idan an koma yadda ake yi a baya.

A cewarsa, "Ai dama akwai ƙananan gidajen kallo tun a da. Wasu na kallon ƙwallon ƙafa ne, amma wasu ana nuna finafinai, musamman na Kannywood. Don haka, idan an dawo da wannan, zai taimakawa masana'antar Kannywood."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Muhsin ya ce duk wata hanya da Kannywood za ta samu riba, "bayan YouTube, ko kuma ƙari kan YouTube, abu ne mai kyau ga masana'antar. Dogaro da abu guda, wato YouTube, na da hatsari. Me zai faru idan suka canja tsari (policy)? Kuma ai ba kowane mai tasha ɗin da take kawo kuɗin shiga ba."

"A takaice, hakan cigaba ne ga masu gidan gala da ƴan fim," in ji Dokta Muhsin a zantawarsa da BBC.

A nasa ɓangaren, Furodusa Nazir Auwal, wanda aka fi sani da Ɗanhajiya ya ce abu ne mai wahalar gaske a yanzu a koma haska fim a gidajen gala.

Ya ce, "a baya can lokacin da ake finafinai ba masu dogon zango ba, mukan shirya finafinanmu, sai mu je a kalla a gidajen dirama, kuma an samu tagomashi ba laifi," in ji shi.

Sai dai fitaccen mai shirya finafinan ya ce yanzu lokaci ya canja, ''yanzu ai fim masu dogon zango ake yi. Shi ya sa gaskiya nake tunanin zai yi wahala a iya komawa amfani da gidajen dirama wajen haska finafinai,'' in ji shi.

A game da alaƙar da ke tsakanin gidan gala da Kannywood, Naziru ya ce suna da alaƙa da fahimta mai kyau.

Ya ce, "a baya suna fim ne na dirama da ake hawa dandamali. Amma yanzu sun fi yin rawa. Amma har yanzu idan muna neman ƴan rawa waɗanda suka ƙware, muna zuwa wajensu mu ɗauko."

Asalin gidan gala

Gidan gala ko gidan dirama ko gidan solo wani daɗaɗɗen salon gidan nishaɗi ne a ƙasar Hausa aka daɗe zuwa domin kallo dirama ko rawa.

Asali jarumi a masana'antar Kannywood, Shuaibu Lilisco ne ne ya fara gida gala bayan kafin nan akwai gidan diramar daɓe da kuma rawar ƙoroso da aka saba yi ana zuwa ana kallo.

Daga baya ne harkar ta riƙa canja salo daga finafinan daɓe har aka koma raye-raye har gidajen suka samu karɓuwa a arewacin Najeriya, har suka faɗaɗa zuwa yankunan Najeriya da ma wasu ƙasashen Afirka ta Kudu.