Taron G20: Ƙasashe sun soki Rasha kan mutuwar Alexei Navalny

Manyan ƙasashen duniya sun soki Rasha da kakkausar murya a kan mutuwar Alexei Navalny.

Birtaniya da Faransa da Canada da kuma Jamus, duk sun soki Rasha game da mutuwar Mr. Navalny, a jawaban da suka gabatar wajen taron ƙungiyar G20.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, David Cameron ya shaidawa BBC cewa ƙasashen sun yi amfani da jawaban su a wajen buɗe taron G20 wajen zargin fadar Kremlin da aikata kisan kai.

Mr Cameron ya ce wakilan ƙasashen sun rika bayyana rashin jin daɗin nasu ne a gaban ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov.

Mr Lavrov dai ya musanta zargin, har ma ya yi amfani da damar da ya samu ta yin magana a taron, wajen tambayar wakilan ƙasashen G20 kan ko suna ganin akwai wani abu mai muhimmanci da ya zarce ƴancin ƙasashen su.

Mr Cameron dai ya shaidawa taron cewa dole ne a tilastawa Rasha girbar abin da ta shuka.

Ya kuma bayyana takaicin yadda ana irin wannan magana mai matuƙar muhimmanci, amma Mr Lavrov ya na nuna ko in kula, inda ya mayar da hankali ga latsa wayarsa a madadin sauraron damuwar da ƙasashe ke gabatarwa a kan Rasha.

A wata dambarwar mai kama da wannan kuma, Brazil ta yi amfani da damar jawabi a wajen taron na G20, wajen caccakar kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, saboda gazawarsa wajen kawo ƙarshen yaƙi a Gaza da kuma Ukraine.

Ministan harkokin wajen Brazil Mauro Viera ya gabatar da sukar lokacin da ya yi jawabi a wajen buɗe taron inda ya ce gazawar Majalisar Dinkin Duniya wajen shawo kan rikicin abu ne da bai kamata a lamunta ba.