Shugabannin duniya na ci gaba da alhihin rasuwar Alexei Navalny

Shugabannin ƙasashen duniya na ci gaba da alhinin rasuwar jagoran adawar Rasha Alexei Navalvy.

Alexei Navalny ya mutu a wani gidan yari da ke wani yanki mai tsananin sanyi kamar yadda kamfanonin dillancin labarai suka ruwaito, abin da hukumar kula da gidan yarin ƙasar ta ce.

Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya ce ga alamu jagoran adawar Rashan ya rasa ransa ne saboda jarumtakarsa.

Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak, ya ce Mista Navalny ya kasance na gaba wajen hanƙoron kawo da Dimokradiyya a Rasha.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa, shugabannin ƙasashen kungiyar tarayyar Turai sun ce sannu a hankali gwamnatin Putin ta kashe Mr Navalny.

Hukumar kare hakkin ɗan'dam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta kaɗu da samun labarin mutuwarsa, ta na mai cewa idan har mutum ya mutu a lokacin da ake tsare da shi to ana danganta mutuwar tasa da laifin gwamnatin ƙasar da yake tsaren.

Ana kallonsa a matsayin ɗan adawar da yake yawan sukar Shugaba Vladimir Putin.

Yana zaman gidan yari na tsawon shekara goma sha tara saboda laifukan da ake ganin bi-ta-da-ƙulli siyasa.

A ƙarshen shekarar da ta gabata ne aka mayar da shi gidan yarin da ke yankin Arctic da ake gani a matsayin mafi azabtarwa.

Hukumar gidan yarin da ke lardin amalo-Nenets ta ce tana bincike kan abin da ya janyo mutuwar tasa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tass ya bayyana.

Gwagwarmayar siyasa

A tsawon shekaru, Alexey Navalny ya zame wa gwamnatin Rasha, alaƙaƙai.

An soma jin sunansa ne a shekara ta 2011 lokacin zanga-zanga a Moscow bayan an tafka maguɗi a zaɓukan majalisun dokokin ƙasar.

A wajen zanga-zangar jami’an tsaro suka kamashi, kuma tun daga lokacin ya zama madugun ‘yan adawa.

Yana da dubban magoya baya a shafukan sada zumunta kuma yana yawan bankaɗo abubuwan rashawa, lamarin da ya sa shi tsule idon hukumomi a Rasha.

A bara ne, aka saka mishi guba, bayan ya ji ba ya jin daɗi a cikin jirgin lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa Siberiya. Daga bisani an garzaya da shi zuwa Jamus, inda a nan ƙwararru suka gano cewa akwai gubar Novichok a cikin jininsa.

A lokacin dai fadar Kremlin ta Rasha ta musanta cewa tana yunƙurin kashe shi, amma kuma bayan kammala jinya a Jamus, yana komawa Moscow a watan Junairun bara sai aka kama shi aka tisa ƙeyarsa zuwa gidan yari.

An yi zanga-zanga a faɗin ƙasar, bayan an wallafa wani bidiyo da ke zargin shugaba Vladmir Putin da cin hanci da rashawa.

Alexie Navalny ya mutu ya bar matarsa da ‘ya’ya biyu.