Rasha: Ƙasar ta zargin Amurka da neman katsalandan a zaɓen majalisar dokokinta

Rasha ta zargi Amurka da katsalandan a cikin harkokinta na cikin gida ta hanyar neman tsoma baki a zaben 'yan majalisar dokokin kasarta da za ta yin a wannan wata.

A karshen mako mai zuwa ne 'yan Rasha za su kada kuri'a, amma kuma a bayyane take cewa hukumomin kasar na cike da fargaba kan yadda zaben zai kasance ga jam'iyya mai mulki ta United Russia.

A ranar Juma'a ma'aikatar harkokin waje ta Rasha ta gayyaci jakadan Amurka a Moscow, inda ta gaya masa cewa suna da kwakkwarar shedar manyan kamfanonin fasahar zamani na Amurkar suna saba dokokin Rasha.

A makon da ya gabata ne hukumar da ke sa ido kan harkokin sadarwar waya, ta gargadi Apple da Google cewa suna karya doka da suka ki cire wata manhaja wadda dan hamayyar Rashar da aka daure Alexei Navalny ke yadawa daga cikin kantinsu.

Manhajar tana gaya maka wanda za ka zaba ne a mazabarka domin kayar da dan takarar jam'iyya mai mulki a zaben majalaisar dokokin na Rasha da za a yi ranar 19 ga watan nan na Satumba.

Gaba daya za a yi zaben kujeru 450 ne na majalisar wakilan Rashar ta Tarayya da ake kira Duma, wadda a wannan karon ita ce ta takwas.

A watan Maris na 2020, gwamnati ta shirya yin zabe na wurwuri a watan Satumba na 2020, saboda sauye-sauyen da ta yi a kundin tsarin mulkin kasar, amma kuma daga baya ta yi watsi da shirin.

Sai kuma a ranar 18 ga watan Yuni na wannan shekara ta 2021, Shugaba Vladimir Putin ya sanya hannu a wata doka, ta yin zabe a ranar 19 ga watan Satumba.

Saboda annobar korona hukumar zabe ta Rashar ta ce za a yi zaben tsawon kwana uku daga ranar 17 zuwa 19 ga Satumba.

Jam'iyyu 15 ne suka gabatar da takardunsu na neman shiga zaben. Daga cikinsu an wanke 14 da ba su damar shiga zaben kai tsaye, yayin da daya ba ta samu dama ba.

Rabin kujerun majalisar wato 225 ana zabensu ne ta hanyar mazabu, yayin da sauran rabin, 225 ake zabarsu ta hanyar jerin sunayen jam'iyya.