Yadda hare-haren mayakan Houthi ke tilasta jiragen ruwa yin dogon kewaye

Asalin hoton, Getty Images
Tashoshin jirgin ruwa na Afirka ta Kudu na fuskantar hadarin tafka babbar asarar kudi a kullum sakamakon yadda daruruwan jiragen ruwa ke sauya akalarsu zuwa wasu hanyoyin da ke kewaye da tsaunin Cape of Good Hope da ke Afirka ta Kudun sakamakon hare-haren mayakan Houthi.
Jiragen dakon kaya da ke bin mashigar ruwa ta Suez da ke dakon kusan kaso 12 na al'amuran kasuwanci na duniya na yin zagayen mil 4000, tun bayan hare-haren jirage maras matuka da makamai masu linzami da mayakan Houthis suka kaddamar kan jiragen dako a tekun maliya
Jirage 35,000 ke bin hanyar a kowace shekara. To sai dai yanzu zagayen ya kara yawan kwanakin bulaguro da kimanin kwana 10 zuwa 14 sannan manyan jirage suna fuskantar karin kudin mai na dala miliyan daya a kowace tafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Kamar dai yadda ake da gidan mai, haka jiragen ruwa suke shan mai a tashoshi a lokacin da suke tsaka da balaguro, inda wasu jiragen ke shayar da wasu man.
To sai dai cunkoso a tashar jirgin Durban da kuma wasu 'yan matsaloli daga jami'an shigi da fici ya sa tashoshin jiragen na Afirka ta Kudu ba sa iya shayar da jiragen man.
Shugaban cibiyar hada-hadar ruwa, Unathi Sonti ya ce "idan aka kalli batun gyaran jirage da shayar da su mai da ma zaman otal da ma'aikatan jiragen ke yi, rashin wadannan abubuwa a yanzu haka na matukar taba tattalin arzikin Afirka ta Kudu".

Asalin hoton, Getty Images
“Yanzu ba za a iya yi wa jiragen duk irin wadnnan abubuwan a birnin Durban ba - tashar jirginmu mafi girma saboda batutuwan da suka shafi cunkoso, duk da cewa hukumomi na aiki a kan hakan," in ji Mr Sonti.
A bara tsakanin 23 zuwa 30 na watan Nuwamba, an samu cunkuso a wajen tashar ruwan ta Durban kamar yadda kamfanin Clyde & Co ya ce kasancewar an samu jirage kimanin 79 da kuma fiye da kwantenoni 61,000 da aka tilastawa tsayawa a wajen tashar saboda wasu matsaloli da suka hada da lalacewar kayan aiki da rashin kyawun yanayi.
Hukumar tashoshin jiragen ruwan Afirka ta Kudu da ake kira Transnet National Ports Authority, (TNPA) ta tabbatar da samun karuwar jirage a Cape Town da Durban, inda jiragen ke tsayawa domin shan mai da kuma gyara.
“Hukumar ta kaddamar da wani tsarin kawar da cunkoso na kwantenoni," in ji mai magana da yawun hukumar.

Asalin hoton, Reuters
Rikici kan haraji
Batun rikici kan haraji ma na kara janyo cunkuso musamman tsakanin hukumar tattara haraji ta kasar Afirka ta Kudu da kamfanin kula da jiragen ruwa da ke Algoa Bay a Eastern Cape.
“Ayyuka a Algoa Bay ka iya zama wadanda suka fi dacewa to amma yanzu an tsayar da hakan saboda 'yan matsaloli da hukumar harajin ta Afirka ta Kudu."
Asarar da ake tafkawa
Matthew Mitchell, kwararren mai kayyade farashin kayan dako a kamfanin da ke kula da hada-hadar kayayyaki na duniya wato Argus Media, ya ce tsadar jigilar gangar danyen mai miliyan daya daga yankin Gulf zuwa tekun baharrum ta hanyar mashigar ruwa na Suez Canel "ya karu da kaso 60 cikin dari tun bayan da aka kai wa jirgin ruwa na Strinda hari."
Tashin farashin na nuni da karin inshora da sauran tsarabe-tsarabe, in ji Mr Mitchell, baya ga matsalar rashin tabbas dangane matsalar tsaro.
Maersk, daya daga cikin manyan kamfanonin dako na duniya, ya riga ya fadi cewa jiragensa na zagaye tashoshin jirgin ruwa na kasar Afirka ta Kudu.

Asalin hoton, Getty Images
Eleanor Hadland, babbar mai fashin baki kan tashoshin jiragen ruwa a Drewrey ya ce mafi yawancin jiragen ruwan da suke yin zagaye ta tsuburin Cape ba sa son tsayawa a tashoshin jirgin ruwa na Durban da sauran tashoshin kasar Afirka ta Kudu.
Ta ce akwai rahotanni da ke nuna samun tsaiko ga jirage da ke bukatar shan mai a wadannan tashoshin na Afirka ta Kudu, sai dai kuma hakan zai shafi kadan ne daga cikinsu.
Ta kara da cewa manyan jiragen za su iya jure zagaye ta hanyar samar da wuraren shan mai a kan hanyarsu kamar a Singapore da Fujairah da kuma Gibraltar.











