Kocin Man Utd na son Marcus Rashford ya tsaya a kungiyar

Asalin hoton, Reuters
Kociyan Manchester United Erik ten Hag ya ce yana son ganin Marcus Rashford ya ci gaba da zama a kungiyar a kakar nan.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa wakilan Rashford sun gana da kungiyar Paris St-Germain, ta Faransa, wadda ta dade tana son dan wasan.
Amma kuma Ten Hag yana son dan gaban na Ingila mai shekara 24 ya ci gaba da zama a Old Trafford.
Kociyan ya ce, "Yana da amfani sosai, kun gani tun daga ranar farko da na zo nan, ina matukar farin ciki da shi, ba na son na rasa shi, ba shakka yana cikin tsarinmu a Manchester United."
Rashford ya yi fama a kakar da ta gabata, inda ya kasa yin wani abin a zo a gani bayan da ya ji rauni a kafadarsa a farkon kakar.
Ya ci kwllo hudu a wasan Premier 25, kuma ya rasa gurbinsa a tawagar kasar Ingila.
An sa shi tun a farkon wasan da Brighton ta je ta doke Manchester United a gida 2-1 a karawar farko ta wannan gasar ta Premier
Yadda al'amura suka daburce wa kungiyar a makon da Brighton ta doke ta, United ta janye daga tattaunawa da tsohon dan wasan gaba na Stoke da West Ham Marko Arnautovic.
Amma kuma ta yi nisa a tattaunawa da dan wasan tsakiya na Juventus Adrien Rabiot.
Kociyan na United ya tabbatat Anthony Martial da Victor Lindelof ba za su buga wasan ranar Asabar ba a gidan Brentford.
Amma ya ce Cristiano Ronaldo na nan cikin shiri.











