Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan kalaman INEC na yiwuwar ɗage zaɓe a wasu mazaɓu

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ahmad Tijjani Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
A ranar Litinin ne, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Najeriya ta yi gargaɗin cewar babban zaɓen ƙasar da ke tafe kan iya fuskantar babban ƙalubale na yiwuwar soke shi a wasu mazaɓu idan matsalar tsaro ta ci gaba da addabar wasu sassan ƙasar.
Shugaban cibiyar bayar da horo ta hukumar zaɓen, Farfesa Abdullahi Abdu Zuru ne ya yi gargaɗin a ranar Litinin a lokacin duba kayan aikin horaswa na hukumar a Abuja babban birnin ƙasar.
Ya ce ''duka mun san cewa tsaro a lokacin zaɓe abu ne mai muhimmanci ga dimokuraɗiyya, domin tabbatar da samun sahihi da kuma ingantaccen zaɓe a ƙasa''.
Ya kuma ce a cikin shirye-shiryen da hukumar ta yi game da zaɓen 2023, dole su yi iya bakin ƙoƙari domin tabbatar da cikakken tsaro ga ma'aikatan INEC da kayan aikin zaɓe da kuma hanyoyin da za a bi wajen ganin komai ya tafi kamar yadda aka tsara.
Ya ƙara da cewa muddin ba a magance matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta ba, hakan zai haifar da soke zaɓen ko kuma ɗage shi a mazaɓu da dama, lamarin da kuma zai shafi bayyana cikakken sakamakon zaɓen, abin da kuma ka iya haifar da wasu matsaloli da suka shafi kundin tsarin mulki''.
Me gwamnatin Najeriya ta ce?

Gwamnatin Najeriya dai ta sha nanata aniyarta ta ganin an gudanar da babban zaɓen ƙasar da ke tafe lami lafiya ba tare da wata fargaba ba.
A martanin da ta mayar ta bakin ministan yaɗa labaran ƙasar, Lai Mohammed a Abuja kan kalaman da wani babban jami'i a hukumar zaɓen ƙasar ya yi na cewa zaɓen ƙasar na fuskantar barazanar sokewa saboda matsalar tsaro, ya ce matsayar gwamnati ita ce zaɓen 2023 zai gudana kamar yadda aka tsara.
Ya ƙara da cewa ''babu abin da ya faru da ya sauya wannan matsayi. Mun sani cewa INEC na aiki da jami'an tsaro domin tabbatar da samun nasarar gudanar da zaɓen a faɗin ƙasar''.
Ministan ya kuma ce hukumomin tsaro na ci gaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa an gudanar da zaɓukan cikin kwanciyar hankali da lumana, inda ya ce babau wata fargaba.
Hukumar zaɓen ƙasar dai ta saka ranar 25 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya.
Me masana tsaro ke cewa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masana bangaren tsaro ma dai na mayar da martani kan kalaman na Hukumar Zaɓen Najeriya kan barazanar soke zaɓen wasu mazaɓu.
Da yake mayar da martani kan kalaman da INEC ta yi, Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consulting, ya ce da farko dai kafofin ƴaɗa labarai sun yi wa kalaman na jami'in INEC mummunar fahimta saboda shi kira ya yi ga hukumomin tsaro su samar da yanayi mai kyau na ganin an gudanar da sahihin zaɓe wanda muddin ba su yi haka ba, za a samu matsala na jinkirin samun sakamakon zaɓen.
Masanin ya ce hurumin jami'an tsaro ne tabbatar da cikakken tsaro ba hukumar zaɓe, kuma su ne ya kamata a ce sun fito sun bayyana tsari na samun tsaro mai kyau.
Sai dai ya ce batun da gwamnatin ƙasar ta yi na cewa babu barazanar tsaro ba haka bane saboda ana fuskantar matsalar tsaro a sassa daban-daban na Najeriya musamman ma arewa maso yamma da arewa maso gabas da kuma kudu maso gabas.
''A waɗannan yankunan akwai kungiyoyi masu rike da makamai waɗanda sun nuna kuduri da kuma kai hare-hare a baya kan ofishoshin hukumar zaɓe da jami'an tsaro. A zauna a ce babu wani abu da zai shafi zaɓe gaskiya ba a yi wa ƙasa adalci ba,''. in ji masanin.
Shi ma a bangarensa, Auwal Musa Rafsanjani, shugaban gamayyar kungiyoyin masu saka ido kan zaɓe da siyasa mai suna Transition monitoring group, Group ya ce tun da farko ma bai kamata hukumar zaɓen ta yi irin waɗannan kalamai ba saboda ko da a lokacin da ƙasar ke fama da matsalar Boko-Haram ma a 2015 da kuma 2019, an gudanar da zaɓe.
Rafsanjani ya ce ''dole ne INEC ta fito ta janye wannan maganar don za su bai wa waɗanda ba sa so a yi zaɓe damar yin nasara. Alhakin INEC ne da jami'an tsaro na tabbatar da an bayar da cikakken tsaro kan jami'anta da kuma kan kayan zaɓe.''
Martanin 'yan Najeriya
'Yan Najeriya da dama ne dai suka riƙa mayar da martani tun bayan da jami'in na INEC ya fito ya ce akwai yiwuwar soke zaɓe a wasu mazaɓun ƙasar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Wani mai suna Umar Biliya ya ce: Allah ya sa mu ga Alkhairi.

Shi ma Babawo Mato Mai'adua cewa ya yi Allah ya bai wa Najeriya shugabanni na gari.

Mu'azu Kabiru Ci-guminka ya ce suna fatan a yi zaɓe lafiya a kuma kammala lafiya.










