Abin kunya ne Buhari ya mika wa jam'iyyar da ba APC ce ba mulki a 2023 - Abdullahi Adamu

Abdullahi Adamu
Bayanan hoto, Abdullahi Adamu Shugaban jam'iyyar APC ta Najeriya

Jam'iyyar APC a Najeriya ta yi watsi da sukar da wasu ke yi cewa shugaba Muhammadu Buhari na janye jiki daga tafiye-tafiyen da ake yi na yakin neman zaben dan takarar shugaban ƙasa na jam`iyyar, Bola Ahmed Tinubu.

Jam'iyyar ta ce a matsayinsa na shugaban kasa bai dace ya jingine aikin sa na jagorancin al'ummar Najeriya saboda yakin neman zabe ba.

Haka nan shugaban jam'iyyar na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu a tattaunawar da ya yi da BBC, ya ce sun gamsu da yakin neman zaben, kuma ba su shakkar abokan hamayya.

"Abubuwa na tafiya yadda muke so, domin idan ba za mu sa rashin godiya ga Allah ba ne, dukkan wanda ke bin tafiyarmu, alamomi da ke zahiran ba badilan wadanda Allah ke nuna mana, muna ganin nasara."

Ya ce mutane sun riga sun karbi sakon jam'iyar APC, "dukkan sauran jam'iyyu sun san mu ke gaba".

Kan ikirarin shugaban kasa Buhari na janye jiki daga tarukan jam'iyyar, ya ce babu kamshin gaskiya kan batun.

"Duk wanda ya gaya maka yana gaban Buhari kan son a ci zabe karya yake yi. Dalilina shi ne abin kunya ne a yi zabe Shugaban kasa ya mika mulki ga wata jam'iyyar siyasa da ba ta shi ce ba".

Ya ce Buhari yafi kowa son APPC ta yi nasara.

"Abin da mutane ba sa la'akari da shi shi ne, Muhammadu Buhari shi ne shugaban kasa, kuma akwai rantsuwa a kanshi cewa kowane dan kasa da ne a gare shi. Haka a wurin fita neman zabe, dole ya yi hattara domin idan bai yi haka ba, masu sukar sa za su zarge shi da yi wa APC aiki ne maimakon yi wa Najeriya aiki.

Kan batun yawan jama'ar da wasu jam'iyyu ke tara wa yayin gangamin yakin neman zabe, shugabn jam'iyyar ta APC ya musanta cewa gabansa na fadi.

"Ni ban gani ba, kuma wannan zancen ba zai ba mu tsoro ba domin abu ne da tafiyar ta gada. Wannan kasa ce mai kimanin mutum miliyan dari biyu, kuma babu inda PDP za ta ta tara mutum miliyan daya."

Ya kuma ce dan takarar jam'iyyar adawa ta PDP ya kasa taka wata rawar gani.

"Shi Wazirin Adamawa mai neman shugabancin Najeriya har yanzu ya kasa hada kan 'ya'yan jam'iyyar."