Kotu ta ci Rubiales tarar dala 10,000 saboda sumbatar ƴarwasa ba da amincewarta ba

Rubiales na sumbatar 'yarwasan Sifaniya

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Babbar kotu a Madrid ta samu tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Sifaniya, Luis Rubiales da laifin sumbatar ƴar wasa ba tare da yardarta ba, a wasan ƙarshe na cin kofin Duniya na mata.

Kotun ta kuma ci tararsa dala 10,000 saboda laifin, sai dai ta wanke shi bisa zargin tilasta wa ƴarwasan.

A makon da ya gabata ne, Mista Rubiales ya faɗa wa kotu cewa Jenni Hermoso ta ba shi damar ya sumbace ta a lokacin da shi ya bayyana da na farin ciki bayan nasarar cin Kofin na Duniya na gasar ta mata.

Wannan ita ce nasara ta farko da ƙasar ta Sifaniya ta yi ta cin kofin na dubniya a karon farko inda ta doke Ingila da 1-0, a wasan da aka yi a Sydeny ranar Lahadi 20 ga watan Agusta na 2023.