Me masu zanga-zangar Take It Back Movement ke buƙata?

Ƙungiyar Take It Back Movement

Asalin hoton, @TIBmovement

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Litinin ne wasu matasa a ƙarƙashin ƙungiyar Take It Back Movement suka gudanar da zanga-zanga a wasu jihohin Najeriya da babban birnin tarayya Abuja.

Cikin jihohin da aka gudanar da zanga-zangar akwai jihohin Legas da Oyo da kuma Rivers.

Omoyele Sowore - wanda shi ne ɗantakarar jam'iyyar AAC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 - shi ne shugaban ƙungiyar Take it Back wanda ya jagoranci zanga-zangar.

Matasan sun fito zanga-zangar ne duk da shawarar da rundunar ƴansanda ta ba su cewa su dakatar da yunƙurinsu., wani abin da ya sa su yin arangama da ƴansanda.

Masu zanga-zangar ƙarƙashin jagorancin Omoyele Sowore sun sha taƙaddama da 'yansanda a kan titi kafin daga baya su ci gaba da macinsu.

To amma abin tambaya shi ne me ƙungiyar ke buƙata, sannan me ya sa ta fito zanga-zangar?

Mene ne buƙatun masu zanga-zangar?

Ƙungiyar Take It Back Movement

Asalin hoton, @TIBmovement

Ƙungiyar Take it Back da Omoyele Sowore ke jagoranta ba baƙuwa ba ce a harkokin zanga-zanga a Najeriya.

Ita ce ta ƙirƙiro zanga-zangar nan ta #RevolutionNow da aka yi a wasu sassan Najeriya a shekarar da ta gabata da manufar "yaƙi da rashin shugabanci nagari".

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A wannan karon ma, masu zanga-zangar na ɗauke da wasu kwalaye da ke cewa "a kawo ƙarshen mummunan shugabanci".

Wasu daga cikin kwalayen kuma na neman a soke dokar laifuka ta intanet wato Cyber Crime Act.

Kazalika, wasu kuma na ɗauke da ƙyallaye masu neman 'yancin faɗin albarkacin baki.

"Muna son kuma gwamnati ta janye dokar ta-ɓaci da ta ƙaƙaba a jihar Ribas saboda salon mulkin kama karya ne," a cewar kodinetan ƙungiyar ta Take It Back Movement, Junwo Sanyaolu.

Ƙungiyar ta kuma ce ta fito zanga-zangar ne domin matsa wa gwamnati ta mayar da wasu haƙƙokin ƴan ƙasa da ta janye.

"Muna zanga-zanga ne kuma domin tabbatar da ƴancin ƴan ƙasa, don ganin sun nuna ra'ayinsu kan rashin adalci da kuma rashin shugabanci nagari wanda ya mamaye gwamnatin yanzu."

A ɗaya gefen, Omoyele Sowore da ke jagorantar ƙungiyar, ya ce ci gaba da zama kan kujera da babban sufeton ƴansandan Najeriya, Kayode Egbetokun ke yi ya saɓa wa doka, don haka ya kamata ya sauka.

"Dole ne Egbotekun ya yi ritaya daga hukumar ƴansanda bayan kammala wa'adin aiki na shekara 35 kamar yadda wasu suka yi bayan kammala nasu shekarun aiki," in ji Sowore.

Jerin zanga-zanga a Najeriya
Zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

Akasarin zanga-zangar da ake yi a ƙasar ana yi ne domin adawa da wani tsari na gwamnati ko kuma nuna rashin goyon baya ga wani mataki da gwamnatin ta ɗauka ko kuma take shirin ɗauka.

Wasu daga cikin zanga-zangar sun yi tasiri wajen kawo sauyi, wasu kuma an yi su ne kawai an tashi ba tare da samun sauyi ko kuma cimma burin waɗanda suka fito zanga-zangar ba.

Irin waɗannan zanga-zanga sun tayar da kura da kuma rikita gwamnatoci a baya. kamar waɗannan:

Zanga-zangar tsadar rayuwa ta #RevolutionNow

A ranar 1 ga watan Agusta ne na 2024 matasan Najeriya suka fara zanga-zangar nuna fushi kan tsadar rayuwa, wadda suka ce za su kwashe kwana 10 suna yi a lokacin.

Zanga-zangar ta gudana ne a jihohi 26 na faɗin ƙasae, inda masu zanga-zangar suka riƙe alluna masu ɗauke da saƙonni daban-daban.

Sai dai wani abu shi ne yadda aka samu tashe-tashen hankula a wasu jihohi, musamman na arewacin Najeriya.

Wannan lamari ya kai ga rasa rayuka da kuma sanya dokar hana fita a kimanin jihohi biyar.

Zanga-zangar #ENDSARS

Wannan ita ce zanga-zanga ta baya-bayan nan wadda ta fi jan hankali a ƙasar wadda kuma ta nemi girgiza ƙasar a shekarun mulkin tsohon shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan zanga-zangar dai ta fara ne tun tuni a shafin Twitter, sai dai daga baya tura ta kai bango, inda matasa suka bazama kan tituna don gudanar da zanga-zangar.

Garuruwan Abuja da Legas ne kan gaba wurin wannan zanga-zangar inda daga baya jihohi kamar irin su Oyo da Kaduna da dai sauransu suka biyo baya.

Sai dai bayan shafe lokaci ana wannan zanga-zangar, gwamnatin ƙasar ta rushe rundunar ta SARS tare da maye gurbinta da SWAT.

Zanga-zangar #BringBackOurGirls

Zanga-zangar BringBackOurGirls ta samo asali bayan da 'yan ƙunigyar Boko Haram suka sace sama da mata 200 a wata makarantar sakandare da ke Chibok a jihar Borno.

Wannan zanga-zanga ta ja hankalin ƙasashen duniya da shugabanninsu da dama, ciki har da Michelle Obama, matar tsohon shugaban Amurka, sakamakon sace matan masu yawa haka wani abu ne da ba a saba gani ba a duniya.

Mutane da dama musamman mata 'yan gwagwarmaya sun fito a manyan titunan Najeriya domin neman gwamnatin ƙasar ta karɓo waɗannan 'yan matan.

Duk da alƙawarin da gwamnatin Goodkuck Jonathan ta yi na ceto 'yan matan, hakan bai sa an daina wannan zanga-zangar ba a ƙasar.

Sa dai mutane da dama na ganin cewa waɗannan zanga-zanga ba su da wani tasiri ko kuma alfanu saboda rashin yin abin da ya kamata daga ɓangaren gwamnati. Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam sun sha sukar gwamnati kan yadda take murkushe masu fitowa znaga-zanga ta karfin tuwo, inda ta ce hakan bai dace ba.