An yi jana'izar marigayi Sarkin Gusau Ibrahim Bello

Asalin hoton, Fadar Sarkin Katsinan Gusa
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rasuwar Sarkin Katsinan Gusau Dr Ibrahim Bello, wanda ya rasu ranar Juma'a yana da shekara 71 da haihuwa.
Sanarwar ta ce sarkin ya rasu ne a daren Juma'a 24 ga watan Yulin 2025 bayan doguwar jinya a wani asibiti da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Sanarwar da gwamnatin Zamfarar ta fitar ta ce: "Rasuwar mai martaba babban rashi ne ga jihar Zamfara da ma daukacin arewacin Najeriya".
Gwamnan Zamfara Dauda Lawal ne ya jagoranci jana'izar sarkin ranar Juma'a a Babban Masallacin Juma'a na Kanwuri da ke birnin Gusau.
"Da ma ya sha yin rashin lafiya a tsaitsaye yana warkewa," kamar yadda Sakataren Masarautar Gusau Sambo A. Sambo ya shaida wa BBC.
"Ko wannan da zai tafi duba lafiyarsa, da ƙwarinsa ya tafi amma sai muka samu labarin rasuwarsa a daren da ya gabata."
A watan Maris na 2015 aka naɗa marigayi Dr Ibrahim Bello a matsayin sarkin Gusau na 15, inda ya maye gurbin ɗan'uwansa Alhaji Muhammad Kabiru Danbaba bayan rasuwarsa.
Marigayin ya bar mata da 'ya'ya sama da 20, a cewar Sambo.
Wane ne Dr Ibrahim Bello?
Gwamnan Zamfara Lawal Dare ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin "rashi ga Zamafara da arewaci da ma Najeriya baki ɗaya", yana mai bayyana shi a matsayin aboki kuma uba.
"Na yi rashin amini kuma uba, wanda basirarsa ke taimaka mana wajen jagorancin jihar [Zamfara]."
An naɗa Ibrahim Bello sarkin Gusau a ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2015.
Kafin lokacin, marigayin ya shafe tsawon rayuwarsa a aikin gwamnati, inda har ya kai babban sakatare tun kafin a ƙirƙiro jihar Zamfara daga cikin Sokoto.
"Ya yi jagoranci cikin jaijrcewa da ƙwarin gwiwa da kuma ƙarfin imani," in ji Gwamna Lawal.
An taɓa yaɗa jita-jitar mutuwarsa a 2016 bayan wata rashin lafiya da ya yi, amma ya fito da kansa ya musanta hakan bayan kwanaki.
"Ina so mutane su sani cewa ina nan a raye, amma nan gaba kaɗan zan tafi Saudiyya neman magani," kamar yadda ya bayyana cikin wani jawabi ta gidan rediyo a lokacin.










