Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasu manyan duwatsu huɗu da za su iya faɗowa duniya daga sama
- Marubuci, Yemisi Adegoke
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Yawanci mutane suna sanin wani abu game da manyan duwatsun da ke sama ne idan suna kallon fim ɗin kimiyya, ko kuma idan suka ji labarin cewa wani dutsen zai iya faɗowa duniya daga sararin samaniya.
To amma a duniya ƙungiyoyi da dama da sauran cibiyoyin nazari na kimiyya da fasaha suna sa ido a kan irin waɗannan duwatsu tare da nazari a kansu saboda dalilai da dama.
Su dai irin waɗannan duwatsu da ke yawo a samaniya saura ne na abubuwan da suka yi duniyarmu kusan shekara biliyan 4.6 da ta wuce.
Akwai irin waɗannan duwatsu sama da miliyan ɗaya da aka sani, kuma yawanci suna nan suna shawagi a tsakanin rana da duniyar Mars da Jupiter da kuma duniyarmu, kuma za su iya taimaka mana fahimtar asalin rayuwa in ji Monica Grady, farfesa a fannin ilimin taurari da sararin samaniya a jami'ar karatu daga gida( Open University) da ke Birtaniya.
Yayin da wasu duwatsun na sama ba su da wani haɗari, kusan ma suna shawaginsu a sama ba tare da an nuna wata damuwa a kansu ba, wasu kuwa na buƙatar a lura da su.
Akwai buƙatar sanya ido da mayar da hankali kan duk wani abu da zai tunkaro duniyarmu.
Su waɗannan duwatsu ana lura da su sosai har sai an san falaƙinsu sosai, an tabbatar da cewa ba su da wata illa, har ma wani lokaci a iya hasashen tasirin da za su yi.
Nesa da duniya muna dubawa mu ga abubuwan da suka ƙunshi wasu abubuwa na daban a halittarsu in ji Agata Rozeck, mai bincike a kan ilimin sifa (physics) da sararin samaniya a jami'ar Edinburgh da ke Birtaniya.
Idan ana maganar girman waɗannan duwatsu na sama ne to wannan ba abin damuwa ba ne.
''Mun san ainihin inda suke da kuma inda za su,'' in ji masaniyar. ''Muna da ilimi sosai a kan yadda suke tafiya da duk wani motsinsu sannan muna nazari a kan duk wani abu da ya zama na daban a kansu domin ƙara fahimtarsu.
"Kawai waɗanda suke zaman matsala su ne 'yan ƙananan da ba a kai ga gano su ba, har sai an san falaƙinsu."
A dalilin haka yanzu akwai wasu manyan duwatsun na sama da ake sa ido a kansu, kamar yadda masana kimiyya suka bayyana - da kuma ƙarin wani guda ɗaya mai muhimmanci, wanda hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka ta ƙaddamar da wani shiri na nazari a kan dutsen.
1. Dutsen Apophis
Shi dai wannan dutse da ke sama wanda aka yi wa laƙabi da suna Apophis, daga sunan ubangijin hatsaniya da lalata abubuwa na Masar (na zamanin da), Apophis, an gano shi ne a 2004.
Da farko an ga alamun cewa akwai yiwuwar cewa zai iya bugun duniyarmu, amma kuma daga baya hukumar kula da sararin samaniyar Amurka (Nasa) ta sanar da cewa babu haɗarin cewa zai bugi duniya aƙalla nan da shekara 100 masu zuwa.
"A yanzu mun san cewa dutsen zai wuce ta kusa da duniya lami lafiya ranar 13 ga watan Afirilu na 2029," in ji Rozeck.
Tsakiyar dutsen ta kai mita 340 - wato kusan tsawon filin wasan ƙwallon ƙafa uku, kuma zai wuce tsakaninsa da duniya kilomita 32,000, wanda hakan na nufin za a iya ganinsa da ido ƙarara.
2. Dutsen 2024 YR4
Hukumar kula da sararin samaniyar Amurka, Nasa ta ƙiyasta girman wannan dutse daga mita 53 zuwa 67 – wato kusan girman bene mai hawa 15 - An gano wannan dutse ne mai suna 2024 YR4 a shekarar 2024, kuma ya ɗauki hankalin duniya a kwanan nan lokacin da aka ga cewa da alamun zai iya faɗa wa duniya a 2032.
Sai dai daga baya hukumar ta Amurka Nasa ta kawar da hasashen yiwuwar cewa dutsen zai faɗo duniyarmu.
To amma kuma duk da haka har yanzu ana ganin akwai yiwuwa kashi 3.8 cikin 100 cewa dutsen zai bugi wata, sai dai Nasa ta ce ko da ma ya bugi watan, hakan ba zai sauya yadda duniyarmu da sauran taurari (rana da wata da sauran duniyoyi ) ke tafiya ba.
3. Duwatsun Didymos da Dimorphos
Didymos, wanda ke nufin tagwaye a harshen Girka shi ma wani dutsen ne na sama, shi kuwa Dimorphos wani ɗan ƙaramin dutse ne da ke kewaya shi.
Dukkanninsu biyu ana ganin ba su da wani haɗari ga duniya, duk da cewa suna wucewa ta kusa da ita sosai.
A 2022, hukumar Nasa ta tsara za ta yi gwajin kawar da su daga hanyar da suke bi, a matsayin wata hanya da za a iya amfani da ita ta kawar da irin waɗannan duwatsu da ke shawagi a sama waɗanda ake ganin za su iya zama barazana ga duniya.
An zaɓi waɗannan tagwayen duwatsu biyu - Dimorphos da Didymos domin yi wannan gwaji.
To amma daga baya aka gano cewa babu ɗaya daga cikinsu da zai yi karo a duniya.
4. Dutsen Psyche
Wannan dutse ne, da ke tsakanin duniyar Mars da Jupiter kamar yadda aka zana hotonsa a nan yana da nisa da duniyarmu, to amma abubuwan da ya ƙunsa ne suka ɗauki hankalin masana kimiyya
Hukumar Nasa ta bayyana wannan dutsen a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi sarƙaƙiya da ɗaukar hankali a tsakanin irin waɗannan duwatsu da ke yawo a sama.
An gano wannan dutse ne a shekarar 1852, kuma an yi masa wannan laƙabi ne na Psyche wanda suna ne na ubangijin rayuwa na Girka.
Wannan dutse yana nesa da duniyarmu sosai, kuma yana kewayawa ne tsakanin duniyar Jupiter da Mars.
Sannan an yi amanna ya samu ne daga abubuwan da suka ƙunshi ƙarfe da dutse.
Masana kimiyya na ganin yawancin ɓurɓushin ƙarfan da dutsen ya ƙunsa sun samu ne daga ainihin tubalan da suka zama ƙashin bayan duniyoyi, kuma nazari a kanshi ka iya sa a gano ainahin yadda can cikin tsakiyar duniyarmu yake da ma tsakiyar sauran duniyoyi.
A shekara ta 2023 hukumar kula da sararin samaniyar Amurka ta ƙaddamar da shirin nazari a kan wannan sinadari.
Sababbin abubuwan da aka gano a sama
A farkon watannan cibiyar nazarin sararin samaniya ta Vera Rubin ta bayyana cewa sabuwar na'urarta ta hangen nesa ta gano duwatsun sararin samaniya sababbi sama da 2,000 da kuma wasu abubuwa na sararin samaniya bakwai da ke kusa da duniyarmu a cikin sa'a goma kaɗai.
A duk shekara ana gano aƙalla irin waɗannan duwatsu na sama 20,000, daga ƙasa da kuma can sararin samaniya gaba ɗaya.
Farfesa Grady na cewa na'urar hangen nesa irin ta cibiyar nazarin samaniya ta Vera Rubin ake buƙata domin nazarin fili mai faɗi a samaniya.
Cibiyar ta ce tana sa ran gano sababbin miliyoyin duwatsu na sama a shekarun farko na aikin, inda ta hakan za ta sama wa masana kimiyya ƙarin duwatsun sama da za su gani da nazari, tare da ƙara gano sirrin duniyarmu da sauran duniyoyi da taurari.