Ɗan Aliyun Arewa ya buge Dogon Mai Takwasara a Maraba

Damben gargajiya
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan Aliyu ya buge Dogon - Dogon Mai Takwasara a damben gasa ranar Lahadi a Marabar Nyanya a jihar Nasarawa, Najeriya.

Wasan da aka buga tsakanin Ɗan Aliyu daga Jamus da Dogon - Dogon Mai Takwasara Guramada na gasa ne, domin lashe naira 100,000.

A turmin farko Ɗan Aliyu ya yi nasara a damben da aka yi ajon Dogon Mai Takwasara Guramada.

Tun kan nan an fara wani na gasar naira 100,000 tsakanin Garkuwan Kurma Guramada da Sola, Shagon Autan Ɗan Bunza daga Arewa.

Garkuwan Kurma ne ya yi nasara a damben a turmin farko.

Ɗaya damben gasar shima na naira 100,000 ne, an fafata ne tsakanin Buhari Shagon Yalo Guramada da Dogon Messi daga Jamus.

Dogon Messi ne ya lashe damben shima a turmin farko.

Tun kafin nan an buga damben kasuwa a gidan damben Idris Umar Bambarewa da ke Ƴan tifa a karamar hukumar Karo a jihar Nasarawa, Najeriya.

Sakamakon wasannin damben kasuwa:

Wasannin da aka yi canjaras

  • Shagon Tula da Bahagon Ilele
  • Tuturuna da Korona Birus
  • Ɗan Yalon Dijango da Aljanin Dutsen Marri
  • Garkuwan Dan Aliyu da Shagon Ɗan Shariff

Damben da ya yi kisa

  • Aljanin Jirgi Bahago ya buge Bahagon Alasan
  • Fasto na Mai Takawasara ya yi nasara a kan Shagon Ɗan Aliyu
  • Ilele ya doke Shagon Alhazai