Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda matsalar tsaro ta ‘yan bangar siyasa ta mamaye jihar Bauchi
A Najeriya, yayin da babban zaben kasar ke kara karatowa, al’ummar jihar Bauchi na kokawa kan matsalar tsaro da ta sake kunno kai a wasu unguwannin babban birnin jihar.
A shekarun baya dai Bauchi, jihar ta yi kaurin suna wajen yawan matasa ‘yan bangar siyasa da ake kira ‘yan sara suka wadanda ke far wa mutane, amma matakan da hukumomi suka dauka sun ladabtar da matasan.
To amma a yanzu matsalar ta sake kunno kai da wani sabon salo da kuma suna.
‘Yan shara ko kuma masu tokara, su ne sababbin sunayen da ake kiran wadannan matasa da ke yawo da makamai cikin unguwanni walau da dare ko da rana.
Sara suke yi babu saurarawa har sai bukatarsu ta biya ko kuma idan aka fi karfinsu.
Hakan ya sa al'ummar garin ke ganin da ‘yan shara na wannan zamani da kuma ‘yan sara suka na shekarun baya duk Danjuma ne da Danjummai.
A wata ziyara da BBC ta kai zuwa wasu daga cikin unguwannin garin na Bauchi, ta yi kicibis da wasu da suka hadu da tsautsayin wadannan matasa.
Unguwar Rilwanu kwatas, daya ce daga cikin unguwannin Bauchi da wadannan matasa kan je, kuma BBC ta tattauna da mai unguwar wato Malam Umar Nurudden, inda ya shaida mata cewa, yara ne matasa ke shiga unguwar cikin dare su shiga gidan mutane su wulakanta mai gida a gaban iyalansa.
Ya ce, "Wannan abu ya dame mu ba kadan ba, domin akwai ma mutumin da suka shiga cikin gidansa suka yanke shi a kunne.”
BBC, ta je har gidan mutumin da aka yanke wa kunne, inda ya ce cikin dare kawai ya ji shigowar wadannan matasa ‘yan shara.
Ya ce, ‘’ Ni na dauka motsin mage ne, amma da na fito sai na ga matasa su hudu sun shiga har sun kwashi wayoyin salula, sun juya za su fita ke nan sai na cafki daya daga cikinsu, ban yi aune ba sai naji an rufe ni da duka har da kai mini sara a kunne, na sha wahala sosai.”
Baya ga wannan unguwar, wasu da ke tsakiyar gari ma ba su tsira ba domin kuwa a wasu lokuta ma ababen hawa ake sulalewa da su da rana tsaka.
A lokacin da BBC ta nemi jin abin da rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ke yi kan wannan matsalar da ke barazana ga al’umma, da kyar ta samu kakakinta Ahmed Wakili, ya daga waya, sannan ya ce ba BBC ba ce ya dace mutanen unguwannin da ke fuskantar wannan matsalar su sanar mata ba, ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su ya dace suje su kai korafinsu.
To amma a binciken da BBC ta yi ta gano ba dukkan unguwannin garin ne suke da ofishin ‘yan sanda ba.
Sannan duk kokarin jin ta bakin kwamishinan ‘yan sanda na jihar ba a yi nasara ba.
Sau da dama dai ana zargin ‘yan sanda a Najeriya da jan kafa wajen kai dauki idan bukatar hakan ta taso - zargin da sukan musanta.