An fi kashe mutane a zamanin Buhari tun dawowar Najeriya mulkin dimokuradiya – Rahoto

A yayin da Najeriya ke shirin tunkarar babban zaɓen a watannin farkon shekara mai zuwa lokaci yana kurewa wajen tabbatar da an yi zaɓen lami lafiya kuma da inganci, a cewar wani rahoto da cibiyar Tony Blair ya fitar.

Cibiyar ta Burtaniya ta yi tsokaci kan irin barazanar da zaɓen ke fuskanta kan irin yadda zaɓen zai iya samun cikas daga rikicin Boko Haram, da masu fafutukar a-ware ta haramtacciyar ƙungiyar IPOB.

Akwai kuma kungiyoyin 'yan bindiga da 'yan bangar siyasa da kuma masu yaɗa labaran karya a shafukan sada zumunta da muhawara.

Gargaɗin na kunshe ne a cikin rahoton mai taken "dimokuradiya tana fuskantar barazana".

Cibiyar tayi tsokaci kan mahukuntan Najeriya da kawayenta na ketare kan daukan matakan tabbatar da cewa an yi zaɓe mai zuwa ta shugaban ƙasa da mataimaka da sanatoci da 'yan majalisa da gwamnoni cikin kwanciyar hankali da sahihanci.

Rahoton da wani babban jami'i a cibiyar, Bulama Bukarti ya rubuta na cewa Najeriya ita ce kasa mafi karfi ta fuskar tattalin arziki da dimokuraɗiya a Afirka da kuma yawan al'umma, don haka zaɓenta da za a yi a cikin watanni Fabarairu da Maris din baɗi na da muhimmaci sosai ga makomarta da kuma yankin Afirka baki ɗaya.

Me Rahoton ya kunsa?

Cibiyar ta ce yin zaɓe cikin kwanciyar hankali zai kafa tarihi irin na dimokuraɗiya, shekara 24 bayan komawa ƙasar tafarkin dimokuradiya.

Amma zaɓen da ke zuwa ko rigingimu ke mamayewa, ko wanda ake da shaku kan sahihancinsa, zai kasance babbar barazana da abin alla-wadai ga kasa da ke cikin kangin barazanar tsaro, rarrabuwar kawuna da matsalolin tattalin arziki.

Lokaci na kurewa - kasa da watanni uku a gudanar da babban zaɓen Shugaban kasa da Mataimakin shugaban kasa da Sanatoci da majalisar wakilai a ranar 25 ga watan Fabarairu.

Sai dai har yanzu ana iya daukan masu muhimmanci musamman ga wadanda hakkin tsaron kasa ya rayata wuyansu, da kuma tafiyar da harkokin zaɓen.

Cibiyar ta ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta habbaka kokarinta wajen 'yantar ko kare ƙauyuka da garuruwa da hare-haren 'yan ta'adda ke shafa kafin lokacin zaɓuka.

Akwai kuma bukatar tabbatar da cewa an tura jami'an tsaro domin sa ido kan zaɓukan da cigaba da murƙushe duk wani ko ƙungiyoyi masu hassada husuma.

Tabbatar da hukunta wadanda aka samu da laifukan zaɓen – yaɗa labaran boge – zai kasance jan-kunne ga duk wanda yake da tunanin zagon kasa ko tada husuma ga tsarin dimokuraɗiya.

Rahoton ya kuma ce akwai bukatar dole ƙasashen ƙetare su marawa Najeriya a wannan yanayi mai matuƙar wahala.

Rahoton ya taɓo ƙasashen Amurka da Burtaniya da Tarayyar Turai da su aike sakonni gargaɗi da goyon-bayan sahihin zaɓe da matsa lamba kan manyan kamfanonin fasaha su sanya ido kan shafukansu domin daƙile yada labaran boge ko ƙarya.

Zaɓukan baya da asarar da aka tafka

Rahoton na musamman da aka aikewa BBC ya nuna cewa asarar rayuka mafi yawa a aka tafka a lokacin zaɓe shi ne 2011, da mutum 800 suka rasa rayukansu.

Sai kuma a 2007 da rigingimun zaɓe suka yi sanadin rayuka 300, sai kuma a 2019 mutum 145 da 2015 mutum100.

A cewar rahoton, a tsawon mulkin Shugaba Buhari daga 29 ga watan Mayun 2015 zuwa 29 ga watan Mayun 2022, mutum 55,430 suka mutu a hare-haren ta'addanci da 'yan fashi a faɗin ƙasar.

A zaɓen 2003, mutum 100 suka mutu yayinda a 1999 lokacin da ƙasar ta koma tafarkin mulkin dimokuraɗiya mutum 80 ne aka kashe a lokacin zaɓe.

Bincike ya nuna cewa lokacin da aka fi tafka asarar rayuka shi ne bayan zaɓen 2011, lokacin da aka yi tsanmanin cewa shugaban mai ci a yanzu shi ne ya yi nasara.

A wannan lokaci bayan sanar da cewa babban abokin hamayya a wannan lokaci, Buhari ya faɗi zaɓe, na shafe kwanaki uku ana tafka rikicin da ya yi sanadin rayuka 800, sannan dubu 65,000 suka rasa muhallansu.

Duk da cewa babu takardu ko bayanai da ke kunshe da bayanan rikici da aka yi a 2015 da 2019, masu sa ido kan zaɓe na Tarayyar Turai sun ce rikici da tsangawama ya mamaye zaɓen 2019, inda "jami’na INEC da masu kaɗa kuri'a suka rinKa fuskantar barazana daga magoya-bayan jam’iyyu".

EU ta bada rahoton cewa aƙalla mutum 145 aka kashe a rikicin da ke da alaƙa da zaɓe a 2019, adadin da ya haura abin da aka gani a zaɓen 2015, na mutum 100.

A zaɓen 2019, manya 'yan takara, Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar, dukkaninsu Fulani ne kuma Musulmai daga Arewacin Najeriya, abin da ya rage tashin hankali a wannan lokaci.

Hakazalika, a 2015, amsa shan kaye da tsohon Shugaba Jonathan ya yi tun kafin a bayyana sakamakon karshe ya taimaka wajen kaucewa sake maimaita abin da ƙasar ta gani a zaɓen 2011.

Sai dai a manyan masu takara a zaɓen shugaban kasa na 2023, Tinubu da Atiku, duk Musulmai ne, kabilarsu ba ɗaya ba hakazalika yankin da suka fito kamar lokacin Buhari da Atiku.

Sannan wani abin la'akari shi ne, zaɓen da ke tafe akwai karin 'yan takara biyu masu karfi, Peter Obi, Kirista daga Kudu maso gabashi, da Rabi'u Kwankwaso, Musulmi daga Arewa maso yamma, dukkaninsu na da magoya baya masu karfi.

Masu sa ido na ganin dole a lalubo hanyar tabbatar da zaman lafiya tsakanin wadannan 'yan siyasa domin mutunta sakamakon zaɓe, domin tun yanzu ana hasashen abubuwa da dama zasu biyo bayan zaɓen 2023 kusan makamancin abin da aka gani a 2011.

Sharhi - Umaymah Sani Abdulmumin

Masu sharhi kan harkokin zaɓe na ganin babban kalubalen da ke zamewa zaɓen 2023 tarnaki shi ne batun tsaro, inda ake ganin kamar gwamnati ba ta shirya sosai ba, wajen tunkarar matsalolin tsaro a kan gaɓa.

Tun dawowar tafarkin dimokuraɗiya a 1999, kowanne zaɓe na tattare da nashi kalubale da barazana don haka a kowani lokaci ana hasashen abubuwan da za su iya faruwa da kuma matakan tufke warwara tun a kan lokaci.

Sai dai kusan a wannan lokacin abubuwan sun bambanta saboda manyan kalubale ko yanayin da ƙasar ke ciki.

Akwai fargaba ganin tun ba a je ko ina ba, ana samun rahotannin mace-mace sakamakon kananan ringingimu, kamar irin wanda aka gani a Osun da Ogun, abin da ya sa ake ganin barazanar ta wannan lokaci ta sha bamban.

Ko a ranar 17 ga watan Nuwamba, Babban Sufeta na kasa, Usman Baba, ya ankarar da cewa an samu rikice-rikice 52 a cikin kwanaki 50, yana mai gargadin cewa rashin daukan matakan da suka dace cikin gaggawa domin dakatar da irin waɗannan ringingimu na iya tasiri ga babban zaɓe da ke tafe.

Shawarwari daga cibiyar Tony Blair

Rahoton Tony Blair ya bada wasu shawarwari kan matakan da hukumomin Najeriya za su iya dauka cikin gaggawa domin tabbatar da tsaro da zaɓe cikin sahihanci, shawarwari sun kunshi:

  • Gwamnati ta yi azzamar 'yantar ko kare ƙauyuka da garuruwa kafin zaɓen 2023.
  • Daidaita yawan jami'ain tsaro da za su ke sa ido kan zaɓe da cigaba da murƙushe ƙungiyoyin da ke tada zaune tsaye.
  • Rashin nuna son-kai daga hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC da 'yan sanda.
  • Bunƙasa tsarin gudanar da zaɓe har zuwa ga mutanen da rikici ya raba da muhallansu domin tabbatar da cewa na dama da kowa.
  • Faɗaɗa yarjejeniyar kwamitin zaman lafiya na kasa na masu takarar shugaban ƙasa zuwa ga gwamnoni da masu takarar kujerar majalisu.
  • Gaggauta hukunta masu haddasa rikici da yaɗa labaran ƙarya domin ya zama darasi ga kowa.
  • Shugabanni addinai da sarakuna su taimaka wajen wayar da kawuna kan zaɓen cikin zaman lafiya.