Ba ni da gida a ƙasar waje kuma haya nake biya a Abuja - Ɗangote

Dangote

Asalin hoton, X/Dangote

Bayanan hoto, Aliko Dangote ya ce gidajensa biyu ne ɗaya a Legas ɗaya kuma a Kano
    • Marubuci, Mansur Abubakar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC

Mutumin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirka, Aliko Ɗangote ya bai wa jama'a da dama mamaki tun bayan da ya sanar da cewa ba shi da gida a ƙasashen waje.

Ɗangote ya kuma sanar da cewa gidajensa biyu ne rak sannan kuma a gidan haya yake sauka a duk lokacin da ya je Abuja, babban birnin Najeriya.

Aliko Ɗangote ne dai attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka kamar yadda mujallar Forbes ta fitar a karo na 13 a jere duk da irin ƙalubalen tattalin arziƙin da Najeriya ke fuskanta.

Dukiyar Ɗangote ta ƙaru da dala miliyan 400 a shekarar da ta gabata, inda yawan arziƙinsa ya kai dala biliyan 13.9 kamar yadda mujallar Forbes ta fitar a lokacin.

Attajirin ɗan kasuwar mai shekaru 66 dai ya samu arziƙinsa ne ta hanyar siminti da sukari duk da a bara ya buɗe matatar mai a birnin Legas.

Ɗan kasuwar dai ya sanar da hakan ne yayin wata tattaunawa da kafafen watsa labarai a matatar man Ɗangote a ranar Lahadi.

Bayanin na ɗan kasuwar dai ya janyo ka-ce-na-ce mussamman a shafukan sada zumunta inda wasu ma ke cewa abin da ya yi shi ne daidai ga harkar kasuwanci domin biyan haya ya fi sauƙi kan gina gidan.

Sai dai kuma akwai waɗanda ke da ra'ayin cewa abin da Ɗangoten ya faɗa yana da ɗaure kai bisa la'akari da irin kimarsa a duniya.

Dalilin yin hakan ga Ɗangote shi ne muradinsa na son ganin Najeriya ta haɓaka.

“Dalilina na rashin mallakar gida a Landan ko Amurka shi ne ina son mayar da hankalina kan cigaban masana'antu a Najeriya.

Ina son ganin Najeriya ta cimma mafarkinta. Kuma idan ban da gidan da nake da shi a Legas sai wanda nake da shi a jihata ta Kano sannan idan na je Abuja haya nake biya" kamar yadda ya faɗa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani mai amfani da kafar sadarwa ta X @Zuzutips ya yaba wa Ɗangote sannan ya ƙara da cewa attajirin ka iya sauya gidan hayar a duk lokacin da ya ga buƙatar hakan.

"Kasancewar Ɗangote yana biyan haya a Abuja bisa la'akari da cewa ya fi sauƙi a biya haya da gina gida ko sayen gidan da da wuya ka zauna a ciki. yanzu aƙalla, zai iya sauya shi a duk lokacin da ya so yin hakan. Kuɗi ba matsala ba ne."

Shi ma wani mai amfani da X ɗin @common_wealthy ya ce bayanin Ɗangote abin a yaba ne kasancewar yana fatan ƙarfafa wa matasa gwiwa ne waɗanda suke son kwaikwayon sa.

Sai dai @PPweshiouz13 da @Homiebishop sun ce bayanin na Ɗangote ya yi kama da mafarki inda suke neman shaidar hakan daga Ɗangoten.

An dia san cewa Ɗangote na da gidan ƙasaita a Legas inda ake kira da "Bananan Island" wanda kuma ya zama masaukin manyan mutane ƴan Najeriya.

Gidansa da ke jiharsa ta Kano a kan titin Lawal Dambazaun road kuma a nan ne yake karɓar baƙi daga ko'ina suke tun dai bayan rasuwar ɗan uwansa, Sani angote a 2021.

Wani mai sharhi Sani Bala wanda aka yawan sauraron sa a rediyo dangane da al'amuran da suka shafi Najeriya ya nemi da a sauya tunanin ƴan ƙasar.

“Na yi wani bincike a baya-bayan nan kuma na gano akwai gidajen ƙasaita na biliyoyin nairori da ba kowa a cikinsu a unguwa a guda, za a iya alkilta kuɗaɗen da aka gina su wajen yin kasuwanci da ka iya bai wa jama'a ayyukan-yi.

“Ƴan Najeriya na buƙatar sauya tunaninsu wajen fahimtar cewa mallakar manyan gidaje na ƙasaita ba burgewa ba ce a lokacin da ake buƙatar saka kuɗin a wasu wuraren.

“Ɗangote ya ce ya sayar da gidansa da ke Landan a 1996 kuma ina da tabbas cewa kuɗin da aka sayar da gidan ya zuba su a kasuwancinsa ne, haka ya kamata a rinƙa yi." In ji Bala.