Dangote ya mayar da martani a kan mallakar hannun-jari a kamfanin simintin Obajana

Siminti

Asalin hoton, Other

Kamfanin simintin Dangote da ke Najeriya, ya ce tun a shekarar 2002 ne ya mallaki hannayen jarin kamfanin siminti na Obajana da ke jihar Kogi, wanda a wancan lokacin bayan rijistar da gwammnatin jihar ce ta yi wa kamfanin, ba ta fara aiwatar da komai da sunan kafa kamfanin da gudanar da harkar siminti gadan-gadan ba.

Kamfanin na Dangote, ya ce jari ya zuba a kamfanin simintin na Obajana, kuma ya bi dukkan ka`idoji kafin ya fara harkar siminti a jihar.

Kamfanin dai ya mayar da martani ne ga gwamnatin jihar Kogi, wadda ta rufe kamfanin simintin bisa zargin cewa bai bi ka`ida wajen mallakar hannun jarinsa ba.

A cewar kamfanin Dangoten, ya ci gaba da sauke duk wani wajibi da ke wuyansa, kama daga biyan haraji na biliyoyin naira zuwa kyautata wa al`ummomin da ke kewaye da shi.

Alhaji Sada Ladan Baki, shi ne babban darakta a kamfanin Dangoten, ya shaida wa BBC cewa, gayyatar su aka yi a kan su je su sanya jari a kamfanin simintin na Obajana, kuma sun sanya.

Ya ce,” Mu ba mu sayi kowane kamfani ba, an gayyace mu mu sanya jari ne a kamfanin simintin Obajana, kuma muka yi hakan, sannan duk wasu ka’idoji da ya kamata mu cika mun cika, baya ga kiyaye duk wasu sharudda na zuba jari a kamfanin, amma ba mu san me ya faru ba mahukunta a jihar Kogi suka dauki matakin rufe kamfanin wai saboda zargin cewa mun yi almundahana wajen mallakar hannun jarin kamfanin simintin.”

Alhaji Sada Ladan Baki, ya ce “ Tun daga lokacin da gwamna Yahaya Bello ya hau Mulki kawo yanzu mun biya haraji da kudin wasu abubuwa da ya kai naira biliyan 16.”

Ya ce ai ba a fito na fada ba.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun a makon jiya ne majalisar dokokin jihar Kogin ta dauki matakin rufe kamfanin, bisa ikirarin cewa ta samu korafi daga wasu al`ummomin jihar wadanda ke zargin cewa kamfanin Dangoten bai bi ka`ida wajen mallakar hannayen jarin kamfanin simintin Obajana ba.

Kuma wannan ne ya sa mahukunta a jihar suka ce sai kamfanin ya nuna shaida.

Gwamnatin jihar dai ta bakin sakataren yada labaranta Mohammed Onogu, ta ce abin da take yi a cikin shekaru biyar da suka wuce shi ne kokarin ganawa da kamfanin Dangote, na kafa kwamitoci daban daban da suka duba hanyar da aka bi ta shari’a wajen mallaka wa kamfanin Dangote ragowar kashi 10 cikin 100 na hannun jarin kamfanin simintin da ke hannun gwamnatin jihar Kogi amma hakan bai yi wu ba.

Ya ce a duk a lokacin da aka zauna sai kamfanin Dangote ya ce zai kawo takardunsa amma shiru har aka kai lokacin da majalisar dokokin jiha ta dauki matakin rufe kamfanin simintin.

Matakin da majalisar dokokin jihar Kogin na ba da umarnin rufe kamfanin simintin Dangoten, ya haddasa yamutsi a kamfanin, saboda wasu rahotanni sun nuna cewa an samu wasu da suka jikkata.

A yanzu haka dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta shiga tsakani da nufin sasanta bangarorin biyu.