Kroos ya yi ritaya da lashe Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Toni Kross ya yi ritaya daga buga wa ƙungiya tamaula, bayan wasan Champions League ranar Asabar a Wembley.
Real Madrid ta doke Borussia Dortmund 2-0 ta ɗauki Champions League kuma na 15 jimilla.
Sun tashi zagayen farko ba ci, sai da suka koma zagaye na biyu ne Real Madrid ta zura ƙwallo ta hannun Dani Carvajal.
Saura minti bakwai a tashi daga karawar Real ta zura na biyu ta hannun Vinicius Junior, wanda hakan ya sa ta lashe Champions League na 15 a tarihi.
A kakar bana, Kroos ya buga wa Real Madrid wasa 49 da cin ƙwallo ɗaya da ƙarbar katin gargadi shida.
Haka kuma ɗan kwallon tawagar Jamus, zai dai na buga wa ƙasar tamaula da zarar an kammala gasar nahiyar Turai ta Euro 2024,
Kofunan da ya ɗauka a Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Lokacin da Kroos zai koma Real Madrid an kammala shirin cewar Manchester United zai je, bayan da aka cimma ƙwantiragi da David Moyes.
To sai dai United ta kori Moyes ta maye gurbinsa da Louis van Gaal, wanda shi kuma bai amince a ɗauko masa ɗan wasan tawagar Jamus ɗin ba.
Daf da kofin duniya ne Carlo Ancelotti ya kira Kroos a 2014.
Ranar 17 ga watan Yulin 2014 Real Madrid ta sanar da cewar ta cimma yarjejeniyar ɗaukar Kross kan kaka shida.
Hakan ya sa Kross ya zama na tara daga Jamus da ya koma Real Madrid da taka leda, bayan Günter Netzer da Paul Breitner da kuma Uli Stielike.
Sauran sun haɗa da Bernd Schuster da Bodo Illgner da Christoph Metzelder da Mesut Özil da kuma Sami Khedira.
Ya fara buga wa Real wasa a karawa da Sevilla a 2014 a UEFA Super Cup ranar 12 ga watan Agusta da ɗaukar kofin farko a ƙungiyar.
Ya zama wanda aka zaɓa cikin FIFPro World 11 da kuma ƴan wasan UEFA 11 karo uku.
An kuma zaɓe shi gwarzon IFFHS a ƙyautar World's Best Playmaker a 2014 da gwarzon ɗan wasan Jamus a 2018.
La Liga: 2016–17, 2019–20, 2021–22, 2023–24
Copa del Rey: 2022–23
Supercopa de España: 2017, 2019–20, 2021–22, 2023–24
UEFA Champions League: 2015–16, 2016–17, 2017–18, 2021–22, 2023 - 24
UEFA Super Cup: 2014, 2017, 2022
FIFA Club World Cup: 2014, 2016, 2017, 2018, 2022
Kyautukan da ya lashe a Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images
Kroos ya fara buga wa Bayern Munich wasan farko a 2007 yana da shekara 17.
An kuma bayar da aronsa wata 18 a Bayern Leverkusen, wanda ya zama kashin bayan ƙungiyar daga nan Bayern Munich ta kira shi a 2010
A ƙungiyar ta Bayern Munich, Kross ya lashe kofin UEFA Champions League da DFB-Pokal biyu da sauransu da yawa.
A shekarar 2014 Real Madrid ta dauke shi kan €25 million.
Bundesliga: 2007–08, 2012–13, 2013–14
DFB-Pokal: 2007–08, 2012–13, 2013–14
DFL-Supercup: 2012
UEFA Champions League: 2012–13
UEFA Super Cup: 2013
FIFA Club World Cup: 2013
Kofunan da ya lashe a tawagar Jamus

Asalin hoton, Getty Images
A Janairun 2010 tawagar Jamus ta kira Kross a karon farko a lokacin atisaye a Sindelfingen daga nan aka gayyace shi wasan sada zumunta da Argentina ranar 3 ga watan Maris din 2010.
Daga nan ya ci gaba da bugawa tawagar wasanni, inda Joachim Löw ya gayyce shi cikin ƴan wasa 23 zuwa gasar kofin duniya a 2010 FIFA a Afirka ta Kudu.
Ranar 19 ga watan Mayun 2021 aka zabe shi cikin masu buga wa Jamus Euro 2020.
Kwana uku tsakani bayan da Jamus ta yi rashin nasara da ci 2-0 a hannun Ingila a zagaye na ƴan 16 ranar 29 ga watan Yuni, sai Kroos ya sanar da yin ritaya.
Sai dai 22 ga watan Fabrairu, Kross ya sanar da cewar zai sake komawa buga wa Jamus wasanni, bayan da koci, Julian Nagelsmann ya tuntube shi.
Haka kuma Jamus ta gayyaci Kroos cikin watan Maris ɗin 2024.
Ya lashe kofin duniya a 2014 da tawagar Jamus











