Abubuwan da suka faru a Premier a karshen mako na hudu

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

Ranar 27 ga watan Agusta aka fara wasannin mako na hudu a gasar Premier League, inda aka yi wasa bakwai.

An kammala wasa uku ranar Lahadi 28 ga watan Agusta a babbar gasar tamaula ta Ingila kakar 2022/23.

Kawo yanzu an buga fafatawa 40 da cin kwallo 118, inda dan wasan Manchester City Erling Haaland ke kan gaba da shida a raga.

A wasannin sati na hudu an yi karawa 10 an ci kwallo 30 a raga, inda wasan da Liverpool ta saharara tara da ba ko daya a ragar Bournemouth ranar Asabar, shi ne kan gaba a yawan zazzaga kwallaye a gasar bana.

Wasannin da aka buga ranar Asabar

Southampton 0-1 Manchester United

Bruno Fernandes

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta kawo karshen koma-bayan da take fama da shi na wasannin da take bugawa a waje a Premier, bayan ta sha da kyar a gidan Southampton.

Kocin kungiyar Erik ten Hag ya kara fitowa da ‘yan wasan da ya doke Liverpool da su, domin samun damar gina tawagar mutum 11 da zai rika fara wasanni da ita.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A minti 10 da dawowa daga hutun rabin lokaci ne Bruno Fernandes ya jefa kwallo daya tilo da ta bai wa United nasara a wasa, ta samu maki uku.

Saints, wadda ta tsallake rijiya da baya da kwallon ta tsaya a daya, domin kuwa tun a minti 45 din farko an buga wata kwallo sau uku yan bayan kungiyar na hana ta shiga, Anthony Elanga ya buga Armel Bella-Kotchap ya tare ta sai kuma Christian Eriksen shi ma.

Dan wasan bayan United Diogo Dalot ne ya kwaso kwallon ta sauka a kafar Bruno, shi kuma ya bugata har cikin zare.

Tun lokacin da Fernandes ya fara yi wa United wasa a Fabrairun 2020 ya zura kwallo 37 a gasar Premier, wadanda ke gabansa tun daga lokacin sun hada da Mohamed Salah mai 54 da Harry Kane mai 49 da kuma Son Heung-Min da ya ci 45.

A karo na biyu a jere kyaftin din kungiyar Harry Maguire bai buga wasan ba, kuma bai fara da Ronaldo ba duk da dai ya sanya shi daga baya kuma da wuri, ba kamar yadda ya sanya shi a wasan Liverpool ba a kurarren lokaci.

Ten Hag ya sanya sabon dan wasan da ya sayo daga Real Madrid, Casemiro wanda aka saya kan kudi fan miliyan 60.

Chelsea 2-1 Leicester City

Raheem Sterling

Asalin hoton, Reuters

Chelsea ta yi nasarar doke Leicester City 2-1 a wasan mako na hudu a gasar Premier League ranar Asabar a Stamford Bridge.

Raheem Sterling ne ya fara ci wa Chelsea kwallo na farko kenan tun bayan da ya koma Stamford Bridge da taka leda a bana daga Manchester City.

Haka kuma Sterling shi ne ya kara na biyu a raga a wasan na hamayya.

Tun kan Chelsea ta fara cin kwallo aka bai wa Conor Gallagher jan kati - Thomas Tuchel bai ja ragamar wasan ba, sakamakon hukuncin hutun wasa daya.

An bai wa Tuchel jan kati, bayan da ya yi hatsaniya da Antonio Conte a wasan da Chelsea da Tottenham suka tashi 2-2 a gasar Premier League.

Haka kuma dan wasan Chelsea, Kalidou Koulibaly shima ya karbi jan kati a kakar bana.

Leicester ta zare kwallo daya ta hannun Harvey Barnes minti uku tsakani da Sterling ya ci na biyu.

Wasa na 11 da Leicester ta ziyarci Chelsea a bayan naa, sau daya ta yi nasara daga ciki, wadda ta sha kashi a karawa shida da canjaras hudu.

Liverpool 9-0 Bournemouth

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool ta ci Bournemouth 9-0 a wasan mako na hudu a gasar Premier League da suka kara a Anfield ranar Asabar.

Karon farko da Liverpool ta zazzaga kwallo tara a raga a wasa a Premier tun bayan da ta taba cin Crystal Palace 9-0 a 1989.

Haka kuma a karon farko da Jurgen Klopp ya ci kwallo tara a wasa a tarihin sana'arsa ta horar da tamaula.

Minti uku da fara wasa Liverpool ta fara zura kwallo ta hannun Luis Diaz daga baya Harvey Elliott ya kara na biyu a minti uku tsakani.

Karon farko da Liverpool ta ci kwallo biyu a raga cikin minti shida a Premier League tun bayan Maris din 1996 da ta yi wa Aston Villa haka.

Boberto Firminho ne ya bayar da dukkan kwallayen biyu aka zura a raga cikin minti shidan, ya zama na biyu a wannan bajintar a Premier tun bayan Islam Slimani a Disambar 2016 a wasan Leicester da Man City.

Trent Alexander-Arnold ya kara na uku a ragar Bournemouth kuma Firminho ne ya bashi kwalon, sannan dan wasan Brazil din ya zura na hudu tun kan hutu.

Virgil van Dijk ne ya ci na hudu, minti daya tsakani Chris Mepham ya ci gida, sai Roberto Firmino ya kara na biyu a wasan kuma na bakwai da Liverpool ta ci.

Kungiyar Anfield ta zura na takwas a raga ta hannun Fabio Carvalho, sannan Luis Diaz ya ci na tara a wasan.

Kwallon da Liverpool ta sharara da yawa a raga a Premier har da cin Rotherham Town 10-1 a shekarar 1896.

Liverpool ta fara yin 2-2 a gidan Fulham a gasar Premier ta bana, sannan ta yi 1-1 a Anfield da Crystal Palace ta kuma yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Manchester City.

Ranar 31 ga watan Agusta Liverpool za ta karbi bakuncin Newcastle United a wasa na biyar a Premier League.

Karo na hudu da aka ci kwallo tara a Premier League:

Liverpool 9-0 Bournemouth (2022)

Manchester United 9-0 Southampton (2021)

Leicester City 9-0 Southampton (2019)

Manchester United 9-0 Ipswich Town (1995)

Manchester 4-2 Crystal Palace

Erling Haaland

Asalin hoton, Getty Images

Manchester City ta doke Crystal Palace da ci 4-2 a wasan mako na hudu a gasar Premier League da suka fafata ranar Asabar a Etihad.

Palace ta fara cin kwallo bayan da John Stones ya fara cin gida, sai Joachim Andersen ya kara na biyu tun kan hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Bernardo Silva ya zare daya, sai Erling Haaland ya farke na biyu.

Daga nan Haaland ya kara na uku da kuma na hudu a wasan - ya zama na farko da ya ci kwallo shida a wasa hudu a Premier, bayan bajintar Sergio Aguero..

Haka kum dan wasan ya zama na hudu da ya zura kwallo shida ko fiye da haka a wasa hudu da fara Premier League tun bayan Diego Costa mai bakwai a 2014.

Ranar 7 ga watan Agusta Haaland ya fara cin West Ham United kwallo biyu a wasan makon farko da City ta yi nasara a kan West Ham 2-0.

Haka kuma ranar 21 ga watan Agusta City ta tashi 3-3 da Newcastle, inda Haaland ya ci daya daga ciki.

City ta ci gaba da dora tarihin cin wasa 47 da canjars biyu a karawa 55 da ta yi ranar Asabar da karfe uku na yammaci da rashin nasara biyu kacal.

Wasa biyun da ta yi rashin nasara shi ne wanda Palace ta doke ta.

Ranar 31 ga watan Agusta City za ta karbi bakuncin Nottingham Forest a wasan mako na biyar a gasar Premier League.

Brighton 1-0 Leeds United

Graham Potter

Asalin hoton, Getty Images

Brighton ta yi nasarar cin Leeds United 1-0 a wasan mako na hudu ranar Asabar a gasar ta Premier League.

Pascal Gross ne ya ci kwallon a minti na 66 da ya bai wa kungiyar maki ukun da take bukata a fafatawar.

Leeds ba ta yi ci Brighton ba a wasa takwas baya a Amex, sun yi canjaras 13 a dukkan haduwa, Leeds ta yi nasara a wasa 17, ita kuwa Brighton ta yi nasara a 19.

Brighton ta kafa tarihin yin wasa tara a jere ba tare da an doke ta ba a tarihin kungiyar, bayan da take da bajintar takwas a 1981.

Brentford 1-1 Everton

Brentford vs Everton

Asalin hoton, Getty Images

Brentford da Everton sun tashi kunnen doki 1-1, kuma Everton ce ta fara cin kwallo ta hannun Anthony Gordon a minti na 24 da fara wasa.

Karon farko da dan wasan da Chelsea ke zawarci ya ci kwallo, bayan buga kwallo ya nufi raga ba tare da ya ci ba har karo 10 a bana tun kan wasan ranar Asabar.

Saura minti shida a tashi daga wasan Brentford ta farke ta hannun Vitaly Janelt.

Everton ba ta taba doke Brentford a a babbar gasa ba - har da rashin nasara a fafatawa hudu daga shidan da suka fuskanci juna.

Arsenal 2-1 Fulham

Arsenal team

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal ta doke Fulham 2-1 a wasan mako na hudu a gasar Premier League ranar Asabar a Emirates.

Kungiyoyin biyu sun je hutu ba tare da an ci kwallo ba - daga baya Fulham ta zura daya a raga ta hannun Aleksandar Mitrovic na hudu da ya ci kenan a bana.

Daga baya ne kyaftin din Arsenal, Martin Odegaard ya farke, sannan Gabriel Magalhaes ya kara na biyu.

Wasa na hudu da Arsenal ta yi nasara a jere a kakar bana kenan, tana nan a mataki na daya a kan teburi da maki 12.

Karo na 31 da Arsenal ta fuskanci Fulham a gida ba tare da rashin nasara ba a dukkan fafatawa da ta yi da kungiyar.

Wannan shi ne wasa na 100 da Mikel Arteta ya ja ragamar Arsenal a Premier League - ya yi nasara 53 da canjaras 16 da shan kashi a wasa 31.

Karo na 34 da Gunners ta fuskanci sabuwar kungiyar da ta hau Premier League tun bayan da ta yi rashin nasara a hannun Newcastle da ci 1-0 a Nuwambar 2010.

Cikin wasa 34 da Arsemal ta yi da sabbin kungiyoyin da suka hau babbar gasar tamaula ta Ingila, Gunners ta ci 29 da canjaras biyar.

Wasannin ranar Lahadi 28 ga watan Agusta

Aston Villa 0-1 West Ham

Declan Rice

Asalin hoton, Getty Images

'Pablo Fornals ne ya ci wa West Ham kwallo a karon farko da kungiyar ta ci wasa a kakar bana, bayan wasa hudu.

Kungiyar ta sha kashi a karawa uku a Premier League ta bana, Inda Manchester City ta yi nasara da ci 2-0 a wasan makon farko.

West Ham ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Nottingham Forest a karawar mako na biyu, sannan Brighton ta doke ta 2-0 a fafatawar mako na uku.

Karo na biyar a jere da West Ham na doke Aston Villa a haduwa da suka yi kwanan nan.

Wasa na 1,000 kenan da West Ham ta buga a Premier Plreamier League ta zama ta tara cikin kungiyoyin da suka yi karawa 1,000 a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Wolverhampton 1-1 Newcastle

Newcastle United

Asalin hoton, PA Media

Wolves ce ta fara cin kwallo ta hannun Ruben Neves a minti na 33 da fara wasa, sai dai Newcastle United ta farke daf da za a tashi ta hannun Allan Saint-Maximin.

Newcastle ta fara da cin Nottingham Forest 2-0 a wasan mako farko, sai ta tashi ba ci da Brighton ta kuma yi 3-3 da Manchester City mai rike da kofin a karawar mako na uku.

Ita kuwa Wolverhampton ta fara da rashin nasara da ci 2-1 a gidan Leeds United da 0-0 da Fulham, sannan Tottenham ta doke ta 1-0 a wasan mako na uku.

Nottingham Forest 0-2 Tottenham

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

Tottenham ta je ta doke Nottingham Forest 2-0 a wasan mako na hudu a gasar Premier League da suka fafata ranar Lahadi.

Harry Kane ne ya ci kwallayen biyu ya kuma barar da bugun daga kai ssai mai tsaron raga, inda Tottenham ta yi wasa hudu a jere ba tare da rashin nasara ba.

Kawo yanzu Kane ya ci kwallo 201 tun fara sana'ar tamaula, kuma 187 a gasar Premier League, ya yi kan-kan-kan da Andrew Cole a mataki na uku a jerin mafiya cin kwallaye a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Alan Shearer ne kan gaba mai 260 da kuma Wayne Rooney mai 208 a raga a wasa 491, ya kuma bayar da 103 aka zura a raga.

Kane dan wasan tawagar Ingila ya buga wasa 286 a Premier League mai kwallo 187 a raga, yana tarihin shi ne ya ci kwallaye da yawa a kungiya daya a Premier League.

Bayan kwallo 187 da ya zura a raga a Premier League, ya kuma ci tara a Championship da kuma biyar a League One.

Tottenham ta yi wasa hudu a jere ba tare da rashin nasara ba a kakar nan, bayan da ta fara cin Southampton 4-1 da yin 2-2 da Chelsea da kuma nasara a kan Wolves 1-0.

Ranar 31 ga watan Agusta, Tottenham za ta karbi bakuncin West Ham United a wasan mako na biyar, sannan ta je gidan Fulham ranar 3 ga watan Satumba.

Wasannin mako na biyar da za a buga:

Ranar Talata 30 ga watan Agusta

Fulham da Brighton

Crystal Palace da Brentford

Southampton da Chelsea

Leeds United da Everton

Ranar Laraba 31 ga watan Agusta

Arsenal da Aston Villa

Manchester City da Nottingham Forest

Bournemouth da Wolverhampton

West Ham United da Tottenham

Liverpool da Newcastle United

Ranar Alhamis 1 ga watan Satumba

Leicester City da Manchester United

Jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Premier League:

  • Erling Haaland Manchester City 6
  • Harry Kane Tottenham 4
  • Rodrigo Leeds United 4
  • Aleksandar Mitrovic Fulham 4
  • Pascal Gross Brighton 3
  • Martin Odegaard Arsenal 3
  • Wilfried Zaha Crystal Palace 3
  • Luis Diaz Liverpool 3
  • Ivan Toney Brentford 2
  • Pelenda Joshua Da silva Brentford 2
  • Che Adams Southampton 2
  • Raheem Sterling Chelsea 2
  • Ilkay Gundogan Manchester City 2
  • Bernardo Silva Manchester City 2
  • Gabriel Jesus Arsenal 2
  • James Maddison Leicester City 2