Ronaldo na son komawa Chelsea, Man Utd na neman Aubameyang

Asalin hoton, OTHERS
Chelsea ta sake nuna sha’awarta a kan dan wasan gaba na Crystal Palace Wilfried Zaha, dan Ivory Coast mai shekara 29, amma kuma har yanzu Pierre-Emerick Aubameyang na Barcelona da Gabon shi ne kungiyar ta fi son saye. (Guardian)
Sai dai kuma Manchester United ma tana son daukar dan wasan na Gabon domin har ma ta yi tuntuba a game da shi. (Caught Offside)
Shi kuwa wakilin tauraron Manchester United, Cristiano Ronaldo ya koma Chelsea inda ya tuntubi kungiyar ko akwai yuwuwar ta dauki dan wasan na Portugal mai shekara 37. (Independent)
Bayan da Ajax ta sallama wa Manchester United dan wasanta Antony, yanzu ta karkata wajen Chelsea domin ta sayar mata da Hakim Ziyech, dan Morocco domin ya maye gurbin dan Brazil din. (Mail)
Chelsea ta yi tayin bai wa Everton dan wasanta na Albania Armando Broja, mai shekara 20, da kuma dan wasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher, mai shekara 22, har ma da kudi Fam miliyan 25 domin ta ba ta dan Ingila Anthony Gordon. (Football Insider)
Ana sa ran dan wasan tsakiya na Barcelona da Holland Frenkie de Jong, ya ci gaba da zama a Nou Camp a bazaran nan duk da sha’awarsa da Manchester United da Chelsea da kuma Liverpool ke yi. (CBS Sports)
Liverpool na dubu yuwuwar sayen dan wasan tsakiya na Sheffield United da Norway, Sander Berge mai shekara 24. (Yorkshire Post)
Leicester da Everton na son gaggauta zawarcin dan gaban Al Hilal, Matheus Pereira dan Brazil mai shekara 26. (Sun)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Valencia na da kwarin gwiwa za ta kasa Real Sociedad wajen daukar Edinson Cavani, kuma ta shirya bashi kwantiragin shekara biyu. (Fabrizio Romano)
Dan bayan Tottenham da Sifaniya, Sergio Reguilon mai shekara 25, ya shirya tafiya Atletico Madrid aro, amma kuma yarjejeniyar ta ce ba damar sayen shi. (Fabrizio Romano)
Dan wasan tsakiya na Spurs da Ingila Harry Winks, na dab da tafiya Sampdoria bayan da ya jira ko zai samu wata kungiya ta Premier da za ta dauke shi. (Evening Standard)
Chelsea ta yanke shawarar cewa dan bayanta Trevoh Chalobah, dan Ingila ba zai bar kungiyar ba a wannan bazara duk da cewa ya tattauna da Inter Milan da AC Milan da RB Leipzig, domin tafiya aro. (Fabrizio Romano)
Chelsea na fatan doke Tottenham da Crystal Palace wajen sayen matashin dan bayan Peterborough na Ingila, Ronnie Edwards, mai shekara 19. (Football Insider)
Spezia za ta dauki aron dan wasan tsakiya na Wales, Ethan Ampadu mai shekara 21, daga Chelsea tare da damar sayensa a kan kudin da ya kai Fam miliyan 12.7 (Fabrizio Romano)










