Kane ya yi kan-kan-kan da Cole a cin kwallaye a Premier

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

Tottenham ta je ta doke Nottingham Forest 2-0 a wasan mako na hudu a gasar Premier League da suka fafata ranar Lahadi.

Harry Kane ne ya ci kwallayen biyu ya kuma barar da bugun daga kai ssai mai tsaron raga, inda Tottenham ta yi wasa hudu a jere ba tare da rashin nasara ba.

Kawo yanzu Kane ya ci kwallo 201 tun fara sana'ar tamaula, kuma 187 a gasar Premier League, ya yi kan-kan-kan da Andrew Cole a mataki na uku a jerin mafiya cin kwallaye a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Alan Shearer ne kan gaba mai 260 da kuma Wayne Rooney mai 208 a raga a wasa 491, ya kuma bayar da 103 aka zura a raga.

Kane dan wasan tawagar Ingila ya buga wasa 286 a Premier League mai kwallo 187 a raga, yana tarihin shi ne ya ci kwallaye da yawa a kungiya daya a Premier League.

Bayan kwallo 187 da ya zura a raga a Premier League, ya kuma ci tara a Championship da kuma biyar a League One.

Tottenham ta yi wasa hudu a jere ba tare da rashin nasara ba a kakar nan, bayan da ta fara cin Southampton 4-1 da yin 2-2 da Chelsea da kuma nasara a kan Wolves 1-0.

Ranar 31 ga watan Agusta, Tottenham za ta karbi bakuncin West Ham United a wasan mako na biyar, sannan ta je gidan Fulham ranar 3 ga watan Satumba.