Kungiyoyin Firimiyar Ingila sun kashe £1.5bn a kasuwar 'yan kwallo ya zuwa yanzu

Erling Haaland da Darwin Nunez sune mafiya tsada da aka saya a wannan kakar

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyoyin Premier sun kafa tarihin kashe kudade mafiya yawa a lokacin musayar 'yan wasa, kamar yadda mujallar Deloitte ta bayyana.

Mujallar mai kididdiga kan kudaden da ake kashewa a fannin kasuwancin kwallon kafa ta ce, ya zuwa yanzu kungiyoyin sun kashe fan biliyan 1.5 a wannan kakar bana, wanda ya haura na 2017 da aka kashe da suka kai fan biliyan 1.4.

Akwai mako guda da ya yi ragowa a rufe kasuwar musayar 'yan wasan, a ranar 1 ga watan Satumba da misalin karfe 12 na dare.

A daidai irin wannan lokacin a 2021 sun kashe fan miliyan 895 a karshe kuma adadin yakai fan biliyan 1.1.

"Yanayin habbakar kasuwancin da muke gani a wannan kakar na nuna yadda kungiyoyi ke farfadowa daga koma bayan da korona ta haifar musu," in ji Chris Wood mataimakin daranktan mujallar.

"Wannan shi ake nufi kasuwanci a harkar kwallon kafa, kuma kungiyoyin Premeir na nuna cewa a shirye suke su habbaka wannan kasuwanci."

Cikin manyan kasuwancin da aka yi akwai wanda Liverpool ta dauko dan wasan Urguay Darwin Nunez daga Benfica, wanda aka cimma a kan fan miliyan 64 wanda aka cimma a kan fan miliyan 85.

Sai kuma cinikin da aka yi a makon jiya na dan wasan Brazil da Manchester United ta yi, Casemiro wanda aka yi shi kan fan miliyan 60 amma da sauran kudaden da za a biya cinikin yakai fan miliyan 70.

Tottenham ta sayi dan wasan Brazil Richalison daga Everton kan cinikin da yakai fan miliyan 60, sai kuma Manchester City da ta dauki dan wasan Norway daga Dortmund kan kudi fan miliyan 51.2.

Cinikin Raheem Sterling daga City wanda ya koma Chelsea shima ya kai fan miliyan 50, kazalika Chelsea sun sayi dan wasan bayan Sifaniya daga Brighton kan kudi fan miliyan 60.

Ya zuwa yanzu kungiyoyin Premier sun sayi 'yan wasa 14 a kan kudi sama da fan miliyan 30, idan aka kwatanta da takwas din nan.