'Ina Larabawa da sauran Musulmi? Falasdinawa na cikin bakar wahala'

.
Bayanan hoto, Wanna matar da ke jiran a bata gas din girki, ta zargi duniya da yin watsi da Falasdinawa

"Ina larabawa da Musulmai suke? Ina masu kare hakkin dan'adam? Kun wofintar da al'ummar Falasdinawa su na shan wuya, ga yunwa, sannan an daidaita su."

Wannan ce maganar da wata mata da ta haura shekaru 40 ke yi a lokacin da ta ke kan dogon layin karbar gas din girki a Gaza.

Cikin fusata da bacin rai ta ke yin maganar da karfi, da ka kalli fuskarta za ka ga tsananin damuwa da tashin hankali da wahala sun lullube ta.

''Tun da tsakar dare, muke kan layin nan dan karbar gas din girki, a tsaye na yi sallar asuba a wurin nan."

Ta shaida min 'yar gudun hijira ce daga Beit Hanoun da ke arewacin Gaza, tafiyar kilomita 2 zuwa iyakarsu da Isra'ila.

"Ba zan iya kwatanta miki yadda aka lalata wurin ba. An shafe daukacin iyalai daga doron kasa, an kashe su baki daya a cikin gidansu.

"An lalata Gaza baki daya. Allah ka kawo mana dauki."

A yanzu ta na zaune tare da iyalanta a wata makaranta da Majalisar Dinkin Duniya ta maida sansanin 'yan gudun hijira da ke birnin Deir al-Balah a tsakiyar Gaza.

.
Bayanan hoto, Daruruwan mutane sun yi layin karbar gas din girki, a birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza ranar Talata 28 Nuwamba
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan harin da Hamas ta kai wa Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, tare da kashe Isra'ilawa 1,200 tare da yin garkuwa da wasu sama da 200, Isra'ila ta maida martani da hare-hare ta sama da kaddamar da yaki ta kasa a daukacin Gaza.

Akalla Falasdinawa 14,800 ne suka mutu daga fara yakin, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Hamas ta bayyana.

Zirin Gaza wuri ne da al'umma miliyan Daya da dubu dari hudu ke rayuwa, amma Majalisar Dinkin Duniya ta ce Faladinawa kusan miliyan Biyu ne suka rasa muhallansu bayan Isra'ila ta umarci su gaggauta komawa kudancin Gaza.

Daruruwa ne ke kan layin karbar iskar gas din girki. Maza matasa na zaune kan tukunyar gas din cikin tashin hankali, gajiya da zakuwa. Mutanen wurin sun gama galabaita, gajiya ce bayye a fuskokinsu.

Tun bayan fara aikin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Hamas da Isra'ila, a ranar 24 ga watan Nuwamba, kusan a kowacce rana, manyan motoci 200 dauke da kayan agaji ne ke shiga zirin Gaza, kusan rabin abin da aka saba kai wa gabannin fara yakin.

Kungiyoyin agaji na Majalisar Dinkin Duniya, sun samu zarafin kai agaji arewacin Gaza inda sojojin Isra'ila suka kafa sansani, amma duk da haka agajin bai wadata ba.

Wani mutum da ke tsaye kan layin karbar iskar gas din girkin, ya amince na yi hira da shi.

"Ba za ki iya ganin kofin shayi ko biskita ba. A daren jiya mutanen da ke kwana kan titi sun rabawa juna dan biredin da suke da shi.

"Ruwan sama ya mana duka, ga kuma tsananin sanyi. Haka mutane suka kwana kan titi. Allah ka kawo mana agaji."

.

Asalin hoton, Hani Kali/BBC

Bayanan hoto, Wani mutum zaune kan tukunyar gas a Deir al-Balah

Isra'ila ta dakatar da shigar man fetur Gaza tun fara yakin, daga baya ta amince da shigar da dan kadan. A yanzu ta amince a shigar da lita 140,000 cikin kowanne kwanaki biyu, kamar yadda wani jami'i a ma'aikatar tsaron Amirka ya bayyana.

Gwamnatin Isra'ila ta ce idan ana shigar da isasshen man fetur, Hamas za ta samu damar amfani da shi, wadda kasashen Amirka da Birtaniya da Tarayyar Turai suka bayyana a matsayin 'yan ta'adda.

Mohammed al-Qidrah na tsaye kan layi ya na jiran a zo kan shi domin samun gas din girki.

"Kwananmu uku anan wurin. Mun zo nan kwanaki biyu da suka gabata, amma tun 3 na rana muke tsaye kan layi amma bai zo kan mu ba.

"Babu inda za mu samu man fetur, ko Fulawa ko abin da ka ke bukata. Sai ka sha bakar wuya da fadi tashi da tsayuwa kan layi kafin za ka samu dan abin kai wa baki."

Amirka za ta aike jirage uku na kayan agaji zuwa Masar, dauke da magunguna, da kayan abinci, da kayan bukata a lokacin hunturu, wanda Majalisar Dinkin Duniya za ta yi aikin rarrabawa a Gaza.

.

Asalin hoton, Hani Kali/BBC

Bayanan hoto, Mutane kan layin karbar gas din girki, cikin fusata a Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza

Hukumar Lafiya ta Duniya kuwa ta yi gargadin, za a samu karuwar mace-mace sakamakon barkewar cututtuka fiye da bama-baman da ake yin ruwansu, sakamakon yadda aka daidaita fannin lafiyar Gaza.

A bangare guda kuma, Majalisar Dinkin Duniya ke cewa bama-bamai sun daidaita kashi 61 na gine-ginen Gaza.

Ya yin da yarjejeniyar tsagaita wutar ke aiki, akwai alamun rayuwa ta dan fara komawa Gaza, inda ake fatan girbe dan abin da ya yi saura na gonakin zaitun.

"Mun yi gaggawar amfani da wannan damar domin saurin girbe abin da muka shuka, ba mu da lokaci," in ji wani manomi Bafalasdine mai suna Fathy Abu Salah a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Reuters . wanda mazaunin kudancin Khan Younis.

Ya kara da cewa; "Wannan yakin ya daidaita mu, ba mu da komai, babu amfanin gona. Yawancin abin da aka girbe sun lalace."

.

Asalin hoton, reuters

Bayanan hoto, Falasdinawa sun yi amfani da tsagaita wutar a kudancin Gaza, domin tsince ragowar Zaitun din da ya rage cikin amfanin gonar da suka girbe

Rashin wutar lantarki, ya kara munana lamarin, an kuma dogara ga man fetur domin amfanin injinan da ke sarrafawa da fitar da abubuwan da ake samu daga Zaitun.

"Samun man fetur a lokacin tashin hankali irin wannan abu ne mai wuya ," in ji Muhammad Wafy, ma'aikaci a wurin matse man Zaitun, kima mai noman shi.

Ya kara da cewa; "Da zarar mun samu man fetur, za mu samu zarafin fara aikin matsar man, ko da dan kadan ne."

Gaza

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Rashin wutar lantarki ya sanya Falasdinawa yin dabaru domin matse mai daga Zaitun din da suke nomawa