Dattijuwar da ta zaɓi Nelson Mandela yanzu ba ta goyon bayan magadansa

Cynthia
    • Marubuci, fagal Keane
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

A wannan bangare na wannan kasa, lokacin sanyi lokaci ne na bazara, kasa ta bushe ga kuma kadawar iska da ake samu akai-akai.

Ina jin karar yadda ake haƙa akusa da ni kuma a nan ne na ga wata mata tana wannan haƙa, a can gefe kuma ga wasu maza da mata ma na irin wannan haƙa, suna da wani tsohon lambu ga fatanya da adduna da duwatsu da dai duk wasu abubuwa da ake bukata wajen haƙa rami, inda a nan ne suke zuba tarkacen roba da kuma katakai.

Na tambayi matar ko me take yi?" Muna boye bukkokinmu", ta shaida mini.

Wannan wani sansani ne da ke wajen Jonnesburg tun 1994 yayin da Afirka ta Kudu ke shirye-shiryen zabe a karon farko wanda ba na wariya ba.

Ganin irin wannan lokaci abin alfahari ne ga kasar da aka yi mulkin wariyar launin fata tsawon shekaru, kuma yawancin wadanda suka shaida wannan mulki duk sun kwana biyu.

Shekaru 30 da suka wuce Afirka ta Kudu ta bambanta da yadda take a yanzu. An sha gwagwarmayar siyasa. Fargabar da ake da ita a kan batun wariyar launin fata duk ta kau.

Sai dai mutane da dama a kasar na nuna rashin jin dadinsu da jam’iyyar ANC mai mulki tun bayan da Nelson Mandela ya zamo shugaban kasa bakar fata na farko a kasar.

Idan muka koma kan maganar matar nan da take boye bukkokinsu, ta shaida mini cewa sunanta Cynthia Mthebe.

Labarinta ya tsaya mini a rai tsawon shekara 30.

Cynthia

Yara sun shirya a cikin kayan makaranta inda suka nufi hanyar makaranta, akwai nisa sosai daga inda suke.Komai wuya komai rintsi iyaye na kokarin ganin sun ba wa 'ya''yansu ilimi.

Cynthia na da yara bakwai a lokacin, kuma ita ke kula da su. Mjinta ya gudu ya bar su shekara da shekaru kuma ba su kara jin duriyarsa ba.

A kowacce rana suna binne bukkokinsu saboda gudun gwamnati kada ta rushe musu su. Kuma da yammaci sai su tone ta don su samu su kanta tare da 'ya'yansu. An sha watsa musu barkwanon tsohuwa da harbi da harsashin roba to amma duk da haka sai sun koma inda suke kwana saboda babu inda za suje su kwanta.

"Ina so na yi rayuwa a gida mai kyau tare da 'ya'yana saboda ina shan wuya.Ina so n aji dadi kamar yadda fararen fata ke ji, ina sha wuya ne saboda ni bakar fata ce", ta fada a wancan lokacin.Cynthia na ciyar da 'ya'yanta ne ta hanyar tsintar robobi a bola ta kai ta siyar.

Nelson Mandela

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cikin labarin rayuwarta da take bayarwa labari ne na miliyoyin marassa karfi a Afirka ta Kudu.An haifeta a wata gonar da wani farin fata ya mallaka a 1946 shekaru biyu kafin masu kishin Afirka su karbi mulki da kuma fara amfani da manufar yaki da wariyar launin fata.

A karkashin mulkin wariya, hukumomi da daukan miliyoyin bakaken fata tana jibgewa a kauyuka da sunan mayar da su ‘gida’ da sunan an ba su ‘yanci.

Amma a zahirin gaskiya ana jefa su ne cikin kangin talauci a karkashin azzaluman shugabannin yanki.

Daya daga cikin abubuwan da Cynthia ba zata ta manta da shi ba a rayuwarta shi ne lokacin mulkin rayuwa da ta yi aiki a karkashi a matsayin mai aiki a gidan wani farar fata a Johannesburg.An bata ragowar abinci ta fara ci ke nan a cikin farantin masu gidanta.Sai matar gidan ta shaida mata cewa kada ta sake cin abinci a kwano ko farantin da suke amfani da shi.Sun nuna kamar ni karya ce, inji ta.

Cynthia ta na daga cikin miliyoyin 'yan kasar da Nelson Mandela ya yi wa alkawarin samar da kasa kwaya daya da daidaito bayan an sake shi daga gidan yari a 1990.

A yayin da Afirka ta Kudu ta shiga kwanakin karshe na yain neman zaben 2024, na kai ziyara kauyukan kasar da ke area maso yamma domin na ga halin da Cynthia ke ciki a yanzu.

Yaro rike da fasta

Asalin hoton, Getty Images

Mandela ya kai gwamman shekaru da rasuwa, sannan jam'iyyarsa a Africa’s oldest liberation movement, na kara karbuwa.Afirka ta Kudu ita ce kasar da tafi kowacce kasa a duniya bambance bambance a tsakanin al'umma, ma'ana babu daidaito.

Hasashe na nuna cewa jam'iyyar ANC na cikin hadari rasa kuerunta da ta samu a lokacin zaben 1994.

Na je kauyen su Cynthia na ci karo da abubuwa da dama da suka sauya a tsawon shekarun da na je a baya.

Na gane wani gida mai ruwan shudi da bishiyar lemon tsami a gabansa, na taba zuwa wajen shekaru 30 da suka wuce anan ne na hadu da Cynthia.

Na ga wata tsihuwar mata ta dauki jikarta a kafada, a yanzu Cynthia na da 'ya'ya tara da jikoki 13 da kuma tattaba kunne bakwai.

Cynthia ta gane ni ta kama hannuna tare da ja mini kunne sannan ta rungume ni ta ce," Fergal kai ne? yanzu Cynthia bata gani.Sannan tana da ciwon suga.

Yanzu gidanta ba laifi akwai duk abin da ake bukata, kuma tana samun wani kudi a duk wata d aya kai dala 108.

'Ya'yanta sun gina mata gida, saboda yanzu duk suna aiki.Haka suma jikokinta.

Cynthia da iyalanta

Cynthia na jin haushin gwamnati." Babu aiki, mutane na shan wahala.Amma jam'iyyar ANC na cewa a zabeta, ni na yi zabe, ba wanda zan zaba, akan me me aka yi mana? in ji Cynthia.

Ta ce ba su da ruwan sha a gidansu, sannan ga yawan dauke wutar lantarki saboda cin hanci da rashawa duk ya yi wa bangaren samar wutar katutu in ji ta.

Jam'iyyar ANC dai ta amince cewa ta tafka kura kurai to amma zata gyara.Kodayake jam'iyyar ta ce duk da kura kuranta amma ta yi wasu ayyuka na ayaba mata kamar gina miliyoyin gidaje da asibitoci da dai sauransu.

To amma duk da haka kididdiga ta nuna cewa har yanzu akwai mutum miliyan daya da dubu dari hudu da basu da gidaje.

Cynthia ta ce sam ba ta goyon bayan jam'iyyar ANC, ta ce tana mai alfaharin kasancewarta mai goyon bayan Mandela a 1994.

A Afirka ta Kudu ana tafka ayyuka na rashin imani ga kashe kashe na babu gaira ba dalili da ake yi wa mutanen kasar.