Yadda kasashe uku suka yi gogayya kan Yamal ya buga wa daya tamaula

Lamine Yamal

Asalin hoton, Getty Images

Rawar da Lamine Yamal ke takawa a gasar cin kofin nahiyar Turai da ake ci gaba da yi na shirin bunkasa kwallon kafa a Equatorial Guinea, in ji hukumar kwallon kafar kasar.

Dan wasan mai shekaru 16, wanda ya bai wa duniya mamaki kan bajintar da yake yi a Jamus, yana buga wa Sifaniya wasa duk da cewa mahaifiya 'yar Equatorial Guinea ce da kuma mahaifinsa dan Morocco.

An haife shi a Barcelona, ​​inda ya girma, kuma yana zuwa koyon tamaula a makarantar La Masia, wanda kwanan nan ya kammala kakar wasa ta farko.

Shugaban hukumar kwallon kafar kasar, Venancio Tomas Ndong Micha ya shaida wa BBC cewa "Duk da cewa Lamine ba ya buga wa Equatorial Guinea wasa, muna tare da shi sosai a cikin zukatanmu, kuma muna tunanin zai yi abubuwa da yawa a wasan kwallon kafar Equatorial Guinea."

Ndong Micha ya kara da cewa "Muna jin dadin irin rawar da yake yi a gasar Euro, da rawar da ya taka a kakar da ta wuce a FC Barcelona.". "Yana da tushe daga wajenmu, kuma hakan ya nuna cewa mu kasa ce ta 'yan wasan kwallon kafa."

Yamal, wanda Sifaniya ta yi amanna da shi a babbar gasar tamaula ta Turai, duk da karancin shekarunsa, ya nuna kwarewarsa ta ko'ina tare da kwallon da ya ci Faransa mai ban sha'awa, kuma ya taimaka kasar a wasannin da suka yi da Croatia da Georgia da kuma Jamus.

Yamal zai buga wasan karshe ranar Lahadi da Ingila, kwana guda bayan ya cika shekaru 17, wanda hakan ya sa ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da zai fafata a wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai ko kuma ta cin kofin duniya.

Pele shi ne mafi karancin shekaru da ya taka leda a gasar cin kofin duniya. Yana da shekaru 17 da kwanaki 249 lokacin da ya buga wasan da Brazil ta doke Sweden da ci 5-2 a wasan karshe a 1958, inda ya zura kwallaye biyu a raga.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tarihin da Yamal ya kafa a matsayin matashi wanda ya zura kwallo a gasar Euro 2024 (yana da shekara 16 da kwanaki 361) zai yi wuya a doke shi. Kamar yadda ya yi a Barcelona – wanda shi ne matashin dan wasa da ya fara buga mata tamaula (shekaru 16 da kwanaki 38) – da kuma a La Liga, inda shi ne dan wasa mafi karancin shekaru a tarihi (shekaru 16 da kwanaki 87).

'Bai manta da tushen sa ba'

Equatorial Guinea kasa ce da ta rabu gida biyu, babban birnin Malabo yana daya daga cikin yankunan tsibiranta yayin da daya yankin da ke Bata, a nan aka haifi mahaifiyar Yamal.

Daga karshe ta samu hanyar zuwa kasar Sifaniya, inda take aiki a matsayin aikatau a lokacin ta hadu da mahaifinsa, wanda daga baya ta rabu da shi.

Yayin da mahaifiyarsa da kakarsa ke zaune a Barcelona, ​​sauran dangin mahaifiyar Yamal har yanzu suna cikin Equatorial Guinea, kasar da ta kai matakin kwata fainal karo biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka da suka gabata duk da kankantarta.

Shekaru uku da suka gabata, hukumar kwallon kafa ta Equatorial Guinea (Feguifoot) ta yi kokarin amfani da Yamal a wasa, kasar da take a halin yanzu a matsayi na 89 a Fifa, sai daga baya ta gano cewa Sifaniya sun yi nisa wajen tuntubar matashin, wacce za ta kara da Ingila a wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai ranar Lahadi.

Ndong Micha ya bayyana cewa "Mun tuntubi danginsa a shekarar 2021 amma tuni hukumar kwallon kafar Sifaniya ta yi nisa sosai a wajen tuntubarsu."

""Amma mun yi ƙoƙari, domin ni abokin iyalinsu ne - musamman kakan shi - kuma dukkan iyalan sun kasance suna magana game da yaron.

"Sa'an nan, akwai kuma Morocco da ta tuntube shi ... amma tuni Sifaniya ta yi musu shigar sauri.."

“Faouzi Lekjaa, shugaban hukumar kwallon kafar Morocco, ya bayyana yadda yunkurinsu na daukar Yamal a shekarar da ta gabata ya ci karo da cikas, duba da yadda matashin ke son bugawa Spain tamaula.

Duk da haka, kasashen biyu na Afirka suna cikin zuciyar Yamal - kamar yadda ake iya gani ta fuskar tutocin kasarsu a kan takalman kwallon kafarsa.

Ndong Micha ya kara da cewa "Wannan ya nuna cewa ko da yake yana bugawa Sifaniya wasanni, amma bai manta tushen sa na Equatorial Guinea ba".

"Ndong Micha ya yi imanin cewa Yamal yana sanya al'ummar mahaifiyarsa a idon duniya, yana mai cewa hakan ya yi daidai da nasarar Ansu Fati tun yana karami, shi ma a Barcelona, ​​lokacin da mutane suka sami labarin kasarsa ita ce Guinea-Bissau.

Ndong Micha ya ce: "Kwazon da yake yi - tare da rawar da yake yi a Barcelona - sun nuna cewa Equatorial Guinea tana da wata hanya ta daban ta taka leda a fiye da yawancin kasashen Afirka."

"Idan ka hangi basirarsa, da tushensa, wata rana za mu iya samun karin 'yan wasa kamar Lamine a nan gaba."

Yamal ba shi ne dan wasa na farko da ke zaune a Sifaniya ba mai asalin Equatoguine da kowa ke labarinsa a bana ba, akwai Emilio Nsue wanda ya bayar da mamaki lokacin da ya zama dan wasan da ya fi zira kwallaye a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta bana yana da shekaru 34.

Ba a yi ta surutai ba a duniya a watan da ya gabata, lokacin da Fifa ta yanke hukuncin cewa ba a taba bayyana dan wasan ya cancanci bugawa Equatorial Guinea wasa ba, wanda shi ne kan gaba wajen zura kwallaye 22.

Duk da haka, kwallayen da ya ci sun taimaka wa kasar zuwa zagaye na biyu. Kasar da take da yawan mutum kasa da miliyan biyu ta kai zagayen gaba a gasa hudu baya da ta kara a Afcon.

"Dole ne mu ci gaba da shiri sosai," in ji Ndong Micha.

"Gwamnati za ta zuba jari a makarantun koyar da kwallon kafa domin mu kara samun wasu Lamine da kuma Emilios nan gaba. A shirye ta ke ta ci gaba da saka hannun jari kamar yadda ta yi a shekarun baya, don ci gaba da neman hazikai daga Equatorial Guinea, musamman a kasar kanta.

"Kafin na kama aiki, ba mu taba samun cancantar shiga gasar cin kofin kasashen da kanmu ba - sai dai a matsayinmu na mai masaukin baki (sau biyu) - amma yanzu mun tsallake zuwa gasar ta Afcon har sau biyu (a 2021 da 2023).

A matakin wasanni, tare da Fifa da hukumar Kwallon Kafa ta Afirka, da gwamnatinmu za mu ci gaba da bunkasa kwallon kafa ta yadda a cikin 'yan shekaru masu zuwa, Equatorial Guinea za ta zama abin koyi cewar karamar kasa amma mai dakawa manya kashi.”

Idan Ndong Micha ya sami dama kuma ƙaramar ƙasar tsakiyar Afirka ta sami nasarar shiga gasar cin kofin duniya karon farko a tarihi, to wata rana akwai damar da Yamal zai iya fuskantar al'ummar mahaifiyarsa a wani mataki mafi girma.